Sashe 28
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ibrahim wanda ya hango Jidda tana shirin shiga gidan ya fito daga motar a sukwane, Jidda tana shirin shiga gidan sai ta ji muryarsa mai sanyi yana kiranta, gabanta ne ya harba da ƙarfi ta juyo cikin sauri da jajayen idanunta tana son ganin gaskiyar abin da kunnuwanta suka jiye mata, tana juyowa ta yi arba da shi gabaɗaya bashi da nutsuwa ta ga ko marfin motar bai rufe ba, daga gefen inda motar lefenta take ajiye, yana zuwa gabanta sai kawai ta ga ya zube a kan gwiwoyinsa, hawayen da ta gani kwance a saman fuskarsa sannan hannuwansa biyu a haɗe alamar roƙo, ba ya ma kunyar mutanen da suke wucewa jefi-jefi su ganshi durƙushe a gaban mace. Wani iri ta ji zuciyarta, gabaɗaya sai ta ji hankalinta ya tashi kafin ta samu damar furta wasu kalmomi ya buɗe baki cikin dashshshiyar muryarsa ya ce
"Jidda, don Allah da manzonsa karki gujeni Jidda, ke kaɗai ce farincikin ruhina wallahi ina ƙaunarki fisabililillahi, ki sani ban yi komai ba sai don gudun ki suɓuce mini" Tun da ya fara maganar tamkar an ƙara gudun hawayensa kuka yake haiƙan abin da ya ƙara saka jikinta ya yi sanyi.
Jin bata ce komai ba ya É—ora da faÉ—in
"Tun ranar da na fara ganinki kyakkyawar alaƙar ki da direbana da ya watsa miki ruwa shi ne abin da ya kwaɗaitar da zuciyata ta wuni da ke a ranar, tun daga wannan lokaci ta hanani sukuni Jidda koyaushe ki take ambato!. Na bibiyeki ban samu ganinki ba har dai Allah ya sa a watarana na ganki ke da ƙawarki Salama a inda kuka tsaya kuna tattaunawa a jikin motar da nake ciki, a cikin kalamanki Jidda na samu abin da kike so da wanda bakya so wato kyakkyawan namiji kuma mai kuɗin, wannan furucin ya sa na fara sauya taku ba don na yaudareki ba don yaudara bata cikin tsarina, sai dai kyaun da nake da shi bai ɓuya ba kuma sai Allah ya sa baki gujeni ba, Jidda ki min hukuncin komai amma karki rabo da ni, rabuwarki da ni zai jefani cikin damuwa kuma kin san da hakan, don Allah ba don no ba ki tausayawa wanda ya ƙaunace ki domin Allah" Kallonsa kawai take yadda yake rarraba hannuwa yana roƙonta gashi kalamansa masu kashe jiki domin kalamai ne da wanda ake yi wa su zuciyarsa za ta raunatu!.
Jin bata ce komai ba ya ce
"Idan har za ki yarda ki rayu da ni na yarda zan rabu da duk wani abu da na mallaka wani yake alaƙa da dukiya, in har hakan zai saka ki farinciki Jidda!."
Yanayin yadda yake mata magiya sai ta ji duk tausayinsa ya kamata, a kanta ita Jidda har zai iya sadaukar da komai nasa lallai ƙaunar da yake mata ba ƙarama ba ce. Zuciyarta ce ta mata jagora wajen tsugunnawa a gabansa sai dai ita bata saka gwiyoyinta a ƙasa ba. Tamkar an masa albishir da kujerar makka haka ya ji tun da ganinta tsugunne ya tunatar da shi cewa ba za ta rabu da shi ba amma ganin da yana ta kiranta a waya bata ɗauka ba sai zuciyarsa take ta masa zulumin cewa za ta rabu da shi.
Idanunsa jajaye ya kafe ta da su yana duba nata idanun inda ya ga alamun ta sha kuka duk da ya san kukan ba ya rasa nasaba da gano waye shi amma sai ya ji tausayinta ya kama shi shi ji yake da yana da iko Jidda ba za ta taɓa shiga ƙunci ba a rayuwa ya gwammace duk wata damuwarta ya haɗa da tasa damuwar ya saka a zuciyarsa ita ta rayu cikin salama.
Cikin sanyin murya ta ce
"Na gamsu da jawabinka kuma ko a mafarki ban taɓa tunanin za ka taɓa cutar da ni ba, ina so ka sani ni Jidda ina sonka, kuma zan rayu da kai daɗi ko wuya ina tare da kai, sai dai inaso na ci gaba da kasancewa cikin addu'o,inka kamar yadda kake min a kullum!" Tana gama faɗar hakan bata jira cewarsa ba ta miƙe tsaye kafin ta dawo daga mamakin da ta shayar da shi wuff ya ga ta shige cikin gida.
Tamkar an saka masa daskararriyar ƙanƙara a saitin zuciyarsa haka ya ji, wani sanyi ya baibaye ta haɗe da wani farinciki marar misali a take ya tafi ƙasa ya kai goshinsa ya yi sujada yana miƙa godiyarsa ga mahaliccin da bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, don ya san shi ne ya bashi komai kuma shi yake masa komai. Yana ɗagowa daga sujadar ya tashi ransa fari ƙal ya koma ya shiga mota ya tada ya bar unguwar cikin tuƙi na hankali ba kamar yadda ya zo a kiɗime ba.
Ko da ta shiga gida Abba har ya shige É—aki sallamar da ta yi ma Umma bata amsa ba sannan akwatunan babu ko É—aya a tsakar gidan da alama suna É—akin Abba.
Aliya tun bayan fitar Jidda wayarta ta shiga neman ɗauki wanda ba kowa ba ne sai Kasim wanda ta wa laƙabi da sabon suna wato faƙiri ɗan anace. Ya daɗe yana kiranta kafin ta ɗauka a kufule ta farfaɗa masa maganganu mararsa daɗi wanda suka sosa masa zuciya a ƙarshe ta ce ya aiko a kwashe wannan akwatunan bata so kuma kar ya ƙara tunkarar ƙofar gidansu. Hankalinsa ya tashi amma ya san ɓacin rai ne yana fatan zuciyarta ta sasauto. Haka suka kwana suƙuƙu, don Jidda ta lura Aliya bata runtsa ba a ranar sai tunane tunane sai dai bacci ɓarawo, don ko da ta tashi sallar dare ma Aliya idonta biyu ko alamar bacci amma kuma ba za ta yi nafila na yi addu'a ba tana dai kwance kamar an soya idanunta amma zuciyarta tsanar Jidda ce fal kuma ta ci alwashin warware duk wani abu wanda zai kawo mata damuwa a zamantakewarta wanda Jidda za ta samu ita bata samu ba, don ta ci alwashin ko mene ne Jidda ta mallaka a rayuwa sai ta dawo da shi gareta ko mene kuwa ta ƙudurta hakan a rai da zuciyarta.
Yadda Umma ta ga rana haka ta ga dare bata runtsa ba, zuciyarta kamar ta buga.
Washe gari da wuri Abba ya tafi kasuwa, don haka Umma da Aliya suna É—akin Aliya suna ta shirya yadda abubuwa za au kasance ba tare sa sun kunyata ba.
Aliya ta ce
"Umma tun jiya da wani zazzaɓi ya rufe ni har yanzu bai sauka ba, ni fa akwatunan nan na gama yin status ɗinsu haka ma ƙawayena hatta grp ɗinmu na makaranta da muke ciki da wanda muka yi karatu na tura musu hoton da kuma hoton akwati biyu da kit ina cewa na Jidda ne yanzu kuma ido ya juye da mujiya?" Umma ta sauke wata nannuyar ajiyar zuciya tana tuno yadda ta yi ta alfahri a idanun mutanen unguwa jiya da kuma ƴan uwa a kan lefen yanzu ya zan ce da mutane wallahi dariya za a yi mana"
Aliya ta ce
"Ni tunanina ma gidan da za a kai Jidda da kuma inda za a kaini ai juma,ar da za ta yi kyau saga laraba ake ganeta wallahi Kasim ya cuceni!"
Umma ta yi shiru tana nazari ta ce..
"Na samo mafita, tun da Abbanku ne kaÉ—ai ya san maganar akwatunan ba naki ba ne, shi kuma ba mazaunin gidan ba ne, ita kuma Jidda ko a gabanta aka ce naki ne ba za ta ce komai ba, kawai yanzu a barshi a mazaunin duk wanda ya zo ganin kaya akwati ashirin da huÉ—u da mota naki ne, akwati biyu da kit na Jidda" Wani daÉ—i ya ziyarci Aliya jin an rufe mata wani asirin, sai kuma ta ce
"Umma idan kuma aka kaimu gidajenmu fa ai ƙawaye da mutane ba mahaukata ba ne da za su yarda cewa wanda ya yi akwatuna da mota zai kai ni gidan matsiyatan da Kasim zai kaini"
Umma ta ce
"Dole zan zage dantse a komai Aliya, ba zai iyu ƴar karo ta fi ƴar gida, wato mummuna ta fi kyakkyawa samun gidan hutu da arziƙi"
MAMAN AFRAH
09025576222
[10/22, 4:33 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/DNhoKsIb9qP8PlVQdpQ4BW?mode=ems_copy_c
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 1ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
*ZALIKA*
Rayuwar gidansu ta ci gaba da kasancewa a ƙunci sanadin takurewar da mahaifinsu yake musu, rashin walwala da kuma damuwa da al'amuransu sakin fuska ko yin hira da su matsayinsa na mahaifinsu. Gashi hatta mahaifiyarsu ba a bakin komai take a wajensa ba hasali ma tana jin tsoronsa ne.
Ya zame musu tamkar kumurcin zaki a cikin gida, kowa tsoronsa yake duk abin da suke idan ya shigo gidan kowa taitayinsa yake shiga.
Duk yadda take ta ƙoƙarin fahimtar da shi a kullum ba ya fahimta yana mata ganin tamkar bata san ma abin da take yi ba ne, shi dai ɗabi'a da al'adarsa ce babu ruwansa da ƴaƴansa suke ciki babu fahimta ko ja a jiki ko kima jin ƙai a tsakaninsa da iyalinsa, abu ɗaya ya sani kuma yake la'akari da shi, shi ne tarbiya ta uwa ce, uwa ita aka sani da tarbiyantar da yara amma uba shi kawai buƙatun yaran su ne abin da zai yi sauran kuma ita ta ji da sauran lamuransu.
A kwana a tashi rayuwa tana tafiya al'amura suna sauyawa abubuwa suna taɓarɓarewa. Tun da suka shiga makarantar gaba da secondry ta fara ganin sauye-sauye amma ba na komai ba sai na sun daina faɗar damuwarsu game da mahaifinsu wato sun daina mata ƙorafi a kan ƙin basu lokacinsa sai dai ta fara nazari da tunani sai dai bata samu komai a kan lamarin ba.
Ta fara ayyana ko dai sabo da lamarin mahaifin nasu, tana tunanin ko abin ya zame musu jiki ne ta yadda suka daina damuwa ko kuma yaya ne ita dai bata sani ba, don haka ko da ta zaunar da su a kan ta ji daga bakinsu sai kowanne ya nuna mata babu komai, duk da bata gamsu da hakan ba.