Sashe 27
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Baƙar munafuka, wato mu za ku haɗu ku rufa ke da wannan soloɓiyon, ashe dai shi kura ne lulluɓe da fatar akuya, har mu za ku yi wa bazata ni za ki kunyatw a idon duniya Jidda? Ni za ki sincewa zani a kasuwa, in rufa miki asiri in riƙe ki tun kina ƙanƙanuwarki amma yau za ki kunyata ni a idanun jama'a kenan yanzu dole in ke cewa akwatuna ashirin da huɗu naki ne?" Gabaɗaya idanun Jidda ya cike da hawaye da sauri ta sunkuyar da kanta don bata son irin kallon ƙiyayyar da Umma take jifanta da shi. Bata samu bakin magana ba ita yanzu tunanin da take ma ta matsu ta yi waya da Ibrahim ta ji ya aka yi aka haihu a rageya.
Kiran da Salama ta ƙwala mata shi ya sa ta tashi ta fita daga ɗakin, da take jin ta tamkar a kan ƙaya. Fitowar Abba daga ɗakinsa bayan ya yi saka jallabiya shi ya dakatar da Umma da Aliya da suke kukan takaici marar sauti, ta hanyar kiran da ya ƙwalawa Umma. Sumi-sumi Umma ta fito daga ɗakin tana ta fatan Allah ya taimake ta kar kuka ya ƙwace mata ta fi so ta ci gaba da yaudarae Abba yadda ba zai taɓa gane ko ya fahimci mugun hali da mugun nufin da take da shi a kan Jidda ba.
Tana zuwa ta zauna a kan tabarmar kamar wata zautacciya sai baki take washewa don kar a gano jirginta, Jidda da Salama da suke tsaye daga can gefe suna magana Abba ya ce
"Salama zo ki buɗe min kayan na gani mana" Da to ta amsa ta taho tana raya yadda za ta turawa Umma haushi, Jidda kuma ɗaki ta nufa tana shiga Aliya ta ja wani uban tsakin da ya sa Jiddar kallonta babu shiri, dama ta san a rina wai an saci zanen mahaukaciya. Aliya wacce ganin screen ɗin wayarta ya yi raga-raga sanadin faɗuwar da ya yi ranta ya ɓaci tana tunanin wannan matsiyacin da ya kawo akwati biyu ina ma zai iya sauya mata sabuwar waya, duk da shi ya kawo mata wannan ɗin. Jidda kuma sai ta koma gefen katifarta ta zauna tana ɗaukan keypad ɗinta ta fara latsawa ganin miss call ɗin Ibrahim babu adadai ta ji duk ranta ya ɓaci domin ita yanzu tuhumarsa ma take a zuciyarta shin waye shi, kenan ba shi ne asalin Ibrahim ɗinta ba ne da take so da ƙauna mene ne manufarsa na ɓoye kansa mai ya sa bai bayyana mata waye shi ba tun asalin shin anya yana da gaskiya ma.
Aliya harara take ta aikwa Jidda da take danna waya, tana tunanin da a ce bata wulaƙanta Ibrahim ba da yanzu ita ce a wannan yanayin. Amma yanzu ta yi wa arziƙi dundu da gwiwar hannu ma ba wai da hannun ba.
A tsakar gida kuwa Salama sai ɗaga lesuna take suna ta walwalin tsada Umma ji take tamkar ta haɗiye zuciya ta mutu zai fi mata sauƙi a kan cewa lefen Jidda ne take gani wanda babu haɗinsa da na tilon ƴarta Aliya.
Cike da ƙarfin hali ta ce
"Kai ga wani leshi mai shefen kyau ai kayan nan babu na banza" Abba yana dariya ya ce
"Wallahi sun yi kaya kam shi ma mijin Aliya ai ya yi ƙoƙari a iya ƙarfinsa" A zuciyar Umma ta ce
'Indai akwati biyu da kit ne ƙoƙari Allah tsine ƙoƙari' A fili kuma sai ta ce
"Ai sun yi ƙoƙari matuƙa Allah sa abokan arziƙi ne"
Abba da Salama suka amsa da amin duk da Salama ta san addu'ar Umma iya fatar baki ne, haka Salama ta yi ta ɗaga kayan har suka ƙare kaf babu wanda bata ɗaga ba, kafin ta janye su gefe ta janyo akwatunan Aliya ta buɗe tana ɗagawa Umma ji take tamkar ta ce ta daina ɗagawa saboda haushin da take ji na Jidda kuwa ji take da za ta samu dama da ta babbaka musu ashana sun ƙone ƙurmus har akwatunan. Musamman a na Aliya da aka zo wajen kit ɗin nan aka fito da qur,ani da sallaya ta ji haushin Kasim kamar mai.
Umma gani take Salama da gayya take wani jujjuya atamfofin da basu da maraba da ƙanana. Bayan sun gama ta yi musu sallama ta ce za ta tafi haja suka fita da Jidda za ta taka mata zuwa waje.
Suna fita Salama ta sassauta murya ta yi Æ´ar guÉ—a yadda iya ita da Jidda ne za su ji ta ce
"Kai Allah abin godiya Allah ka ci gaba da ɗaukaka ƙawata aminiyata, yanzu dai na san jikin ta ƙaura ya yi la,asar tun yanzu an fara gane shayi ruwa ne, domin kuwa wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa!". Ta faɗa tana wani rawar kai Jidda wacce gabaɗaya damuwar da take ciki ta bayyana kanta ta dubi Salama cikin sanyjn murya ta ce
"Na lura ke farinciki kike, baki hango damuwar da zan shiga ba Salama, ni ba ma wannan ba Ibrahim ina ya samu kuɗi da ya yi wannan sayayyar sannan har ma da na kayan saka ranar da Abba bai bayyana ba?" Ta faɗa tana jingina da bangon gidan nasu da suke tsaye a kusa da shi tare da harɗe gabaɗaya hannayenta a ƙirji. Salama ta kalleta ta ce
"Tabbas ina yi masa kyakkyawan zato, na san ba sata ya yi ba kuma tabbas yana da tasa hujjar da ya yi hakan kuma dole ki karɓe shi da hannu biyu, sannan kuma ni murna yanzu na fara don da akwai ruwa a kusa da sai na zuba a ƙasa zan sha Jidda, duk iya ƙoƙarin mutanen nan na son ganinki a tsakiyar rana sai gashi Allah ya kai ki inuwa, a i uwar ma ya lulluɓe ki da bargon rahma" Shiru Jidda ta yi tana tuno irin kallon tsanar da Umma take jifanta da shi hatta yanayin kallon Aliya ya tsaye mata a rai, ita basu san ba bata da burin auren kyakkyawan miji bare kuma kuɗi wannan ba ya daga cikin burikanta, Ibrahim ma saboda karamcinsa ya sanya ta amince da shi bayan kasancewarsa kyakkyawa.
A kasalance ta ce
"Salama zan dakatar da Ibrahim domin na fasa aurensa!" Kallon mamaki Salama ta jefa mata, Jidda ta ɗauke idanunta daga kallon Salama tana kallon gefe guda tana tuno irin ƙaunar da take yi wa Ibrahim amma kuma ya zama dole ta haƙura da shi hakan ya sa ta ce
"Baki hangi abin da nake hanga ba Salama, baki san su waye Umma ba duk abin da nake baki labari kaɗan za ki fahimta da abubuwan da idanuna suke gani, zan jure rasa shi a rayuwata a kan na rayu a kan wani giɓi na tsantsar ƙiyayyar waɗanda su ne kaɗai nake kallo a matsayin dangi kuma ƴan uwa!"
Idanun Salama suka tara ruwa ta ciro hannayen Jidda daga ƙirjin Jiddar ta haɗe hannayensu a waje guda duk da akwai wayar Jidda a hannun nata suna kallon juna Salama ta ce
"Jidda!!!"
Amsawa Jiddar ta yi tana kallon Salama kamar yadsa take kallonta ita ma Salama ta ce
"Ina so ki sani abin da Allah ya rubuta ya daɗe da rubutawa, sannan Ibrahim bashi da mugun nufi a kanki don haka kar ki zarge shi ina so ki bashi dama, ya furta miki dalilansa a kan abin da ya yi, na sani ni shaida ce kina son sa kuma ban taɓa ganin kin so wani ɗa namini ba sama da Ibrahim idan kika ce za ki fasa aurensa tabbas zai cutu kuma ke ma za ki cutar da taki zuciyar. Abu na gaba ko ki aure mai kuɗi ko ki auri wanda ya fi mijin da Aliya za ta aura to fa ki sani ba za ta sauya zani ba, babu wani abu da zai sauya a lamarinsu ita kyakkyawar manufa saga zuciya take, duk abin da aka ce miki zuciyar mutum bata da kyau to har abada ba za a iya masa ba, ko da duniya za ka mallaka masa ke ko da za ka ciro zuciyarka ka damƙa masa a hannunsa" Sai da ta numfasa ta ɗora da faɗin
"Idan zuciya ta gyara to dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ta ɓaci dukkan jiki ya ɓaci, su Umma ci gabanki ne basa so don haka shi kuma ubangijin da ya fi kowa sonki yana son ki huta shi ya sa ya baki mijin da za ki aura nagartacce kuma kamili don haka kawai ki fawwalawa ubangiji lamuranki, ki dage da addu,a kamar yadda na sanki tabbas babu wani abu da zaj yi tasiri sai dai alkairi" Tana zuwa nan a maganarta ta damƙe hannun Jiddar da ƙarfi, su duka idanunsu sun cika da hawaye.
Bayanin da Salama ta mata ya sa ta ɗan ji wani ƙwarin gwiwa, shi ya sa take alfahri da ita kasancewarta ƙawar arziƙi a gare ta, duk ƙawar da za ta baka shawarar mai kyau ita ce ƙawa ta har abada, don haka yanzu ta ji tana da ɗamarar jin ta bakin Ibrahim in har bata samu akasin wani abu ba to za ta duba lamarin aurensa kuma ta shirya fuskantar duk wani ƙalubale da za ta tsinci kanta a sanadinsa, aon ta san muddin ta aure shi to bayan dara akwai wata caca!.
Sun daɗe suna magana Salama tana kwantar mata da hankali, kafin daga bisani suka yi sallama Salama ta kama hanya. Jidda kuea ganin Salama ta tafi sai ta ɗan tsaya tana nazarin maganganun tana kuma son kamo bakin zaren, kamar daga sama ta ga wata mota ta shigo layinsu a 360 yanayin yadda aka shigo da motar tuƙin ya yi kama da na ganganci ko dai babu lafiya. Ta gabanta motar da ta zo a guje ta sassauta gudun tana zuwa da ta gifta ta kaɗan sai ta tsaya, Jidda gabaɗaya ta tsorata ma ta fara tunanin ko dai mamallakin motar yana shaye-shaye kar ya je ya fito ya cutar da ita hakan ya sa ta fara ƙoƙarin shiga gida.