Sashe 3
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannu Sadiya ta saka ta ƙara goge hawayenta duk da hakan bai hana wasu zubowa ba, ta ja hanci tare da ru tse idanu tana cije bakinta a hankali ta buɗe baki za ta yi magana, kukan da Kalifa ya saki saboda ya tashi, shi ne ya hanata ƙarasawa. Da sauri Mama ta kai hannu ta rufe masa baki, cikin raɗa-raɗa ta ce
"Kin san dai Malam bai san kin zo gidan nan ba, ina dai gani takalmanki ma sai a bayan ƙofar ɗaki na saka su, saboda yana ganin takalmi a ƙofar ɗakin zai fahimci kina nan, kuma daga ni har ke ranmu in ya yi dubu sai ya ɓaci" Da sauri Sadiya ta ɗaga kalifa zaune tana ɗan jijjiga shi ya yi shiru, yana buɗe udanun ya wartsake ya ce
"Momma abinci" Shiru Sadiya ta yi tana tunanin abin da za a bashi, sai Mama ta matsa ta ɗakko wani ƙaramin filas da yake can gefe ta buɗe ta ce
"Wannan kashin É—umamen Sumayya ne na safe ta ajiye sai ta dawo daga makaranta za ta ci, bari a tsakura masa" Sadiya ta ce
"Mama kin san dai yarinyar nan ba kunya gare ta ba, kina gani da muka zo ma sai da ta yaɓa min magana, ni ban san Sumy wace irin yarinya ba ce" Mama ta ce
"To Halima saboda rashin kunyarta ai ba a ƙi ba yaron nan abinci ba, kuma kin san dai kuka zai yi idan Malam ya ji kukansa kuwa zai gano kuna gidan nan kuma dai kin san ƙarshen zancen, ita kuma Sumayya sai dai na ci gaba da mata addu'a kina gani dai yarinyar nan bata raga mini ko kaɗan kamar ita ce uwar ni ce ƴar ta raina ni wallahi" Cewar Mama tana ɗakko ƙaramin plate ta ɗaukawa Kalifa tuwon aka saka ruwa aka goge masa fuskar ya karɓi tuwon yana ci.
Mama ta ce
"Ni dai abin da zan faɗa miki Halima ki yi haƙuri da lamuran rayuwa" Mama ta faɗa don ganin ta dakatar da Sadiya daga maganar da take son furzarwa daga bakinta. Idanu Sadiya ta ɗaga tana kallon mahaifiyarta a ranta tana tunanin ita sai yaushe ne za a ɗauki lamarin gidan aurenta da muhimmanci an san tana cikin damuwa da matsaloli amma sai a hanata furta komai ake bata haƙuri, basu san irin ƙangin da take ciki ba a ƙalla ko ba za a sama mata mafita ba ai a saurari damuwarta hakan zai rage mata nauyin zuciya.
Cikin sanyin murya ta ce
"Mama wai mai ya sa a kullum bakya sauraren damuwata, kin san irin zaman uƙubar da nake a gidan aurena kuwa? Koyushe na zo da matsala sai dai ki dakatar da ni ki ce in cigaba da haƙuri"
Mama ta ce
"To Halima in ban baki haƙuri ba mai kike so na ce miki, kin san dai aurenki kamar auren zobe ne ba mutuwa zai yi ba don mutuwar aurenki daidai yake da mutuwar nawa auren, ko ma in ce daidai yake da mutuwarki, kin san dai duk cikin ƴaƴa gidan nan ke kaɗai ce mahaifinki yake alfahri da mijin da kika samu kika yi aure, ni ma ke ɗaya nake dakar ƙirji in ce kina ɗakin miji, kina dai gani har kishiyoyi haushin aurenki suke ji suna ganin nasu ƴaƴan basu samu miji ba"
Sadiya ta ce
"Mama wallahi wani auren da shi gwara babu, na san ba za a ce ni kaÉ—ai ce a cikin halin da nake ciki ba dole za a samu mata da yawa da suke cikin damuwa a gidajen mazajensu amma dai wallahi da wannan auren gani nake gwara na dawwama babu...
Katse ta Mama ta yi a daidai nan kalifa ya turo plate É—in da aka tsakura masa tuwon, har ya cinye dama ba yawa ne da shi ba ya ce
"Momma abinci" Ajiyar zuciya Sadiya ta sauke, Mama kuma gabanta ne ya faɗi, saboda ta lura so yake a ƙara masa kuma dai ta san idan aka tarki ƙara masa tuwon ba zai yi saura ba, kuma dai ta san tabbas ƙarewar tuwon nan matsala ne. Filas ɗin ta ɗaga ta juye masa sai Sadiya ta ce
"Mama ya kika juye masa?" Mama ta ce
"To ya zan masa Sadiya yanzu dai kin san idan ba a ƙara masa ba kuka zai yi kuma dama cikin ɗan yaye akwai cin abinci"
Sadiya ta ce
"Ai kuma ni Sumy nake tsoro ta zo ta yi wa mutane tijara" Mama ta ce
"To mene ne baƙo a wajenmu sai ta zo ta yi abin da za ta yi"
Sadiya ta ce
"Mama wallahi Mama zaman gidan Nasir kamar zaman kurku yake a wajena, wulaƙancin yau daban na gobe da ban kuma iyayena kamar wanda suke sa,anninsa wallahi idan kin ga abin da yake min kare ma ba zai ci ba" Ta faɗa hawaye yana malalowa daga idanunta.
Baba da ya fito daga bayi ya yi alwala, ya ɗauki babbar rigarsa ya saka ya gyara zaman kuɗaɗensa a aljihunsa, ya fito zai fita masallacin azzahar ɗin ƙarfe biyu ya ji wata yarinya tana tallar awara, kiranta ya yi ya bata ɗari biyar ta zuba masa a leda ya ƙulle ledar ya kai ɗaki ya ajiye ya kulle ɗakin ya saka mukullin a aljihu, ya fito yana gyara zaman rigarsa ya fita zuwa masallaci, a ƙofar gida suka haɗu da Sumy wacce dawowarta daga makaranta kenan, kallon ta ya yi ya ce
"Sai yanzu kika dawo?" Ta ce
"Sai yanzu dai aka tashemu"
Ya ce
"Amma mai ya sa Aisha ta riga ki dawowa bayan ku duka a S.S 3 kuke?"
"Eh Baba ni ai a A nake ita kuma B na tsaya ƙarasa kwafar rubutu ne"
Ya yi É—an jim kaÉ—an har ya fara tafiya ya juyo ya ce
"Kuma babu wani saurayi da kika haɗu da shi a hanya wanda ya ce yana sonki zai zo gidanku ya aure ki" Ɗan zumɓura baki ta yi a ɓoye sai ta ce
"Ni babu wanda na gani"
Ya ce
"Zan dawo ai akwai maganin farin jini naki da na Aisha zan baku gwara ku yi ku tashi" Ya faÉ—a yana yin gaba ita kuma a ranta ta ce
"Wai hanyar makaranta ma sai an tambayi mutum ya haÉ—unda saurayi, wai mu yi ku tashi sai ka ce wasu jiragen sama" Ta faÉ—a tana juyawa ta shige gidan.
Ko sallama bata yi ba a tsakar gidan dama Mama Sa'ada kawai ta gani tana alwala ita ma Mama Sa'ada da ta san cewar Sumy bau ta ido ta ɗauke kanta saboda ta san yanzu sai ta mata rashin kunya yarinyar da hatta uwarta bata ƙyale ba. Labulen ɗaki ta bankaɗa ko sallama babu daga Mama har Sadiya suka ɗago suna kallon ta buɗar bakin Sumy sai cewa ta yi
"Kam bala'i wane ishashshe da man ne ya ɗauka min tuwo ya ba wannan ƙwalamamman yaron?" Ta faɗa tana ƙarasowa tsakiyar ɗakin ta kama tsantsa tana musu wani kallon fitsara.
Mama ta buÉ—e baki cikin sanyin murya ta ce
"Ki yi haƙuri Sumayya ni ce na ɗauka na bashi, ke da ɗanki yunwa yake ji...
Sumy ta yi saurin katse Mama da faÉ—in
"Wallahi in na yarda shegiya nake, kuma wallahi ni kar a ƙara cewa wannan ɗana ne, a toh ɗana dai a gaba zan haifa"
Mama ta ce
"Allah ya baki"
Sumy ta ce
"Wallahi yanzu ba sai anjima ba za a biyani tuwona, tun da dai ubana ne ya nemo don ya fita kunyata ya ciyar da ni haƙƙin da Allah ya ɗora masa, shi mai ya hana shi a zauna a gidan nashi uban a bashi"
Sadiya ta ce
"Wallahi Sumy ki kiyayeni bana son rashin mutunci sa'arki ce ni?" Cewar Sadiya da jajayen idanunta, dama tana cikin damuwa yanzu kuma za a ƙara mata.
Sumy ta ce
"To ƙarya na yi ne? Na ce ƙarya na yi, ai babu wani rashin kunya in kinaso ki ja wa kanki guntun mutunci to ki zauna a ɗakin mijin naki" Tsaye Sadiya ta tashi ta ɗaga hannu za ta sharara mata mari sai Mama ta shiga tsakani ta ce
"Haba Sadiya ya ina yabonki sallah za ki kasa alwala ke yanzu za ki biyewa wannan sakaran"
BuÉ—ar bakin Sumy sai ta ce
"Wallahi dai Mama kike jin tsoron Allah ji daina nuba bambanci a tsanin ƴaƴa dama ai na san kin tsane ni saboda ni ban yi aure ina kawo miki abin duniya ba, kuma ki biyani kuɗin tuwona da jikanki ya cinye" Ta faɗa cike da tsiwa, ran Mama ne ya ɓace ta ce
"Idan na biyewa zuciya sai na miki baki Sumayya amma ki bi duniya a sannu ni mahaifiyarki kike É—agawa murya kina magana da ni kamar wanda kike magana da sa,arki ke kullum ba za ki gane annabi ya faku ba, kuna manta matsayin mahaifiya da É—awainiyar da ta yi da ku?" Mama ta faÉ—a tana É—aukan É—ari huÉ—u ta cillawa Sumy ta ce
"Ga kuÉ—in tuwon naki nan" Babu kunya ta É—auka ta shige bedroom don faÉ—an da Mama ta yi ma ko a jikinta wai an tsikari kakkausa.
Komawa Mama ta yi ta zauna daɓas ranta duk yana mata ƙuna. Sadiya ta ce
"Mama ki yi haƙuri da halayyar Sumy wallahi ko kaɗan bata ma ɗaukan abin da ake faɗa mata"
Mama ta ce
"To ya zan yi da ita Halima ai haƙuri ya zama dole in ba haka ba halayyar Sumayya sai ta saka zuciyata ta buga, dama an ce a ƙarshen duniya kuyanga za ta haifi uwar gijiyarta kuma gashi nan alamomin sun fara bayyana, tun da za ki ga ƴaƴa suna yi wa iyayensu abu kamar dai su ne iyayen"
Sadiya ta ce
"Allah shirye ta ta ganar da ita"
Zayyanawa Mama irin abubuwan da Nasir yake mata ta yi, amma Mama ta dakatar da ita hakan ya sa Sadiya ta shiga kuka tana cewa