← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 106

Sashe 26

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ku ne iyayen zuwa islamiya gashi nan har qur'ani da sallaya ya saka a kit ɗin maimakon sarƙoƙi da ake sakawa" Cike da Mamaki Abba yake kallon akwatunan da Umma ta nuna sai lokacin ya tuna ashe fa bai cewa samarin nan su ce ga na Aliya ga na Jidda ba. Zaune ya tashi daga ringishen da yake ya yi gyaran murya ya ce

"Wancan akwatunan mai guda biyu su ne lefen Aliya fa" Aliya da take ɗaki a tsaye tana danna waya suna chart da Kasim bata san lokacin da ta saki wayarta ba, Jidda kuma jin furucin Abba gabanta ya buga da mugun ƙarfi tana tunanin to ta yaya hakan zai kasance bayan ta san Ibrahim talaka ne, sannan abin mamakin dai guda ɗaya maganar daga bakin Abba ta fito bare ta ce akwai gyara a ciki.

Umma wacce ta saki baki tana kallon Abba ta ce

"A'a fa Abban yara, wannan akwati guda biyu da kit su ne na Jidda waÉ—an nan guda 24 su ne na Aliya" Abba ya murmusa ya ce

"Tsakanin ni da ke waye ya fara karɓar kayan?" ,Hankalin ta ne ya fara tashi ta ce

"Kai kuwa mene ne na wasa?"

Hannu ya sa a aljihu ya ciro wani mukulli ya ajiye a gabansa ya ce

"Magabatan Kasim su suka fara zuwa da wancan akwatunan biyi da kit a baro, wannan akwatunan 24 su ne magabatan Ibrahim suka kawo a mota, dama miliyan goma suka kawo kuɗin gaisuwa da saka rana ni ne na ƙi karɓa dakyar na karɓi miliyan uku, to yau kuma kin ga lefen da suka kawo wannan mukullin motar ta ne haɗe suke a lefen motar ita ce a waje tana nan!" Jidda ƙarfen windown ta dafe idanunta suka fara hawaye a inda Aliya ta yanke jiki ta faɗi ji kake yaraf, Umma tsaye ta tashi a kiɗime tana zare idanu...

MAMAN AFRAH
09025576222

[10/20, 3:08 AM] Maman boy: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E3Pn5QPLfOVGFdNgMR6ltU?mode=wwc

*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 🔟

*JIDDA*

Cikin sauri ta saki ƙarfen windown da ta riƙe ta yi kan Aliya da gudu tana kiran sunanta, Umma wacce ta tashi tsaye a kiɗimen jin lefen Jidda da miliyoyin da ta ji ya lissafa amma sai ta wayence tana sakin murmushin yaƙe, sai kuma ta yi ɗaki da sauri tana tambayar abin da ya faru duk da ta san musabbabin abun domin zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi ma'ana ta san cewa furucin Abba ne ya saka Aliya faɗuwa.

Salama ma wacce take son fahimtar inda abin ya dosa musamman ma da yake ta san abubuwan da suke faruwa a cikin gidan ita ma bin bayan Umma ta yi, a kusan tare suka ƙarasa da Abba da ya biyo bayanta yana tambaya. Jidda ce cikin kuka ta ce

"Ni ban san mene ne ba na ga ta saki wayarta da take dannawa, kuma sai ta yanke jiki ta faÉ—i" Abba ya ce

"Subhanallahi dama bata da lafiya ne?" Jidda ta ce

"Lafiya take Abba" Abun ya ɗaure masa kai, Umma kuma kuka ta fashe da shi tana mai ɗaga Aliyar, wanda kukan ya zame mata biyu ga na canjin lefwn bazatan da ya ziyarce ta ga kuma faɗuwar Aliya tana fatan dai abin ya tsaya iya faɗuwa kar wani ciwon ya samu Aliya, ta san a yadda zuciyar Aliya take da riƙe abu da kuma ƙyashin Jidda ta samu wani abu ta san da wuya idan wannan abin bai mata mummunar illah ba.

Jidda bil haƙƙi kuka take saboda ganin ƴar uwarta kuma ƙawarta a cikin wani hali domin ko numfashi bata yi ta sandare kamar wata gawa. Gabaɗaya Jidda ta ma manta da cewa an faɗi abin da ya gigita mata tunani na kaya da kuɗin da aka ce Ibrahim ya kawo mata, yanzu damuwar Aliya ce a zuciyarta tana son Aliya da soyayyar Aliya ta tashi sai dai daga baya da Aliyar ta sauya mata shi ne babu yadda za ta yi yanzu ma ji take tamkar ta cire duk wata damuwar Aliyar ta mayar kanta.

Abba ganin Umma tana kuka wiwi ya ce

"Haba Ummar yara yanzu mene ne abin kukan" Tana riƙe da kan Aliya a cinyarta ta ce

"Bata numfashi fa, ya hankalina ba zai tashi ba, ƴar ɗaya tallin tal kamar rai" Ta faɗa tana rushewa da wani kukan. Salama kuwa sai taɓe baki take don ta san zuciyar Umma da ta Aliya ko kaɗan bata da kyau.

Abba ganin sun rikita gidan da koke -koke sai yanzu ma tunanin yayfa mata ruwa ya zo masa, da sauri ya ce

"Salama maza ɗakki ruwa a kofi" Juyawa ta yi bayan ta amsa da to ta ɗakko ruwan da sauri ta kawo, Abba yana karɓa ya fara yayyafa mata amma Umma cikin kuka cewa take

"Ni dai a samo abin hawa mu tafi asibiti" Kafin ya samu zarafin bata amsar sai Aliya ta sauke wata zuciya inda Umma ta shiga rarraba ido tana kiran sunanta amma idanun Aliya a rufe, Jidda ma sunanta take kira inda Umma ta faki idanun Abba ta aikawa Jidda wata muguwae harara don ta san ita ce ummul aba,isin faruwar komai ji take kamar ta samu filo ta dannawa Jidda har sai ta daina numfashi!.

Abba ganin tanyi ajiyar zuciya kuma tana motsi ya ce

"Alhamdulillahi ta farfaɗo, ni ban san mene ne ya sanya ta yanke jiki ba" Ya faɗa yana riƙe da kofin Salama a zuciyarta ta ce

'Mene ne kuwa zai sa ta yanke jiki in ba baƙinciki kyashi da kuma hassada ba' A fili kuma ta ce

"Wataƙila ko dama bata da lafiya ne" Jidda kuwa har lokacin kallon Aliya take da tausayawa, Aliya wacce idanunta yake a rufe ta fara magana don har lokacin bata ma san insa take ba ta ce

"Wallahi akwatunan masu ashirin da huÉ—u haÉ—e da mota su ne lefena" Baki Abba ya buÉ—e da mamaki inda Salama a zuciyarta ta ce

"Humm! Ai dama zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi, sai dai ki yi gawa kuwa wallahi don akwati biyu da kit ne naki sai dai in baron da aka kawo kayan za a koma a karɓo ta zama motarki, am a mota ai sai Jidda'

Umma kuma gudun kar Abba ya fara zarginsu sai ta yi saurin kai hannu tana rufewa Aliya baki tana cewa
."Yi shiru Aliya, na san bakya cikin hayyacinki dama an ce idan mutum ya mutu yana tashi ne a ƙiyama da abin da ya mutu yana aikatawa, to ina ga suma ma idan mutum ya yi to yana farfaɗowa ne da ambaton abin da ya suma ana ambato wato lokacin da ta suma ana maganar akwatuna ne shi ya sa ta farfaɗo da maganar akwatin. Abba sai ya ji ya gamsu da maganar da Umma ta yi tana share hawaye, dama shi bai zargi komai ba tun da iya sanin sa bai san da wata maƙarƙashiya a ƙasa ba.

Umma kamo hannayen ta ta yi tana kiran sunanta idanu ta buɗe warai tana kallon kowa, a take ta fara zubar da ruwan hawaye daga idanunta wanda ba hawayen komai ba ne sai hassada da baƙin cikin abin da aka yi wa Jidda, a take ta ji ta tsani Kasim domin ya yi mata abin da ya tozarta ta ya zubar mata da kima, bayan tana ganin mutanen unguwa da ƴan uwa duk sun gama ganin kyawawan akwatuna da manyan lesuna a matsayin kayanta yanzu kuma a ce akwati biyu da kit mai sallaya shi ne nata kayan da gabaɗaya idan za a haɗa ba za su kai yawan kayan da suke cikin akwati ɗaya na kayan Jidda ba!.

Muryar Abba ce ta katse ta da ya ce

"Sannu Aliya mene ne yale damunki?" Aliya cike da kukan baƙinciki wanda take rerashi a zuci wanda ya fi na fili ciwo ta ce

"Abba ni ma ban sani ba, kawai dai na ji cikina ya murɗa mini sai kuma ban ƙara sanin inda nake ba, amma yanzu ba na jin komai" Abba ya ce

"Ah Alhamdulillahi to, bari na shiga na watsa ruwa" Ya faÉ—a yana juyawa ya fice. Yana fita Salama ta ce

"Sannu Aliya Allah baki lafiya" Banza Aliya ta mata don yanzu a halin da ake ciki duk wani abu da ya shafi Jidda ta tsane shi tsana ta har abada kuwa!.

Jidda tana share hawaye ta ce

"Sannu Aliya" Tamkar ta watsa mata ruwan dalma haka ta ji a kunnuwanta, bata taɓa jin tsanar Jidda da ƙyashin alkairin da ya same ta ba sai yau, wani baƙi ta ga ta ƙara yi gashi kanta ya kulle tana son yin nazarin cewa kenan dai Ibrahim ɗin nan matsayinsa na farko wanda ta fara ganinsa a matakin a ranar farkon da suka haɗu shi ne dai matsayinsa, kenan basaja da ɓadda kama ya yi ko mai yanzu take jin da na sanin wulaƙanta shi a ranar da ya zo unguwarsu ta watsa masa ƙasa a ido, da yanzu ita ce da duka waɗannan abubuwan da Jidda ta mallaka tana jin dama bata riƙe wulaƙanta mutane a matsayin wata turba ba, kenan dai wasu mutanen suna cikin rigar tsiya ne yayin da kuma su masu arziƙi ne, a zuciya ta furta

'Na tsane ki Jidda kin hau matsayin da nake so na taka!" A fili kuma sai ta mayar da idanunta ta rufe saboda ganin Jidda baƙanta mata rai yake ƙara yi. Salama kuwa juyawa ta yi ta koma kan tabarmar tsakar gida.

Umma tana hararar Jidda kamar idanunta za su faÉ—o ta ce
Chapter 26 · 0% Book details