← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 106

Sashe 92

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Momi yanzu duk wannan halin da muke ciki amma sai kike mini zancen kurame?"
Momi tana ɗan ƙoƙartawa wajen ganin ta tashi zaune saboda yadda jikinta yale tsananin ciwo tsabar dukan da ta ci, ganin tashin ba zai iyu ba ta buɗe bakinta da ya kumbura suntum saboda naushin da ya sha kamar ana saka ƙaton ƙuli-ƙuli daga cikin kumatun ta ce
"Haba Meenal baki ga yadda na daku ba kamar sakawara a turmi, wannan yara mararsa imani a ce ko tausayin shekaruna ba su ji ba suka nakaÉ—a mini na jaki... Shiru ta yi sai da ta É—an huta saboda yadda take jin ciwo in tana mganar tamkar an saka gishiri a ciwo ta ce

"Ai tsakanina da su Allah ya isa!"

Meenal ta ce
"Haba Momi yanzu ta dukan da kika sha ma ke kike yi, bakya ta maƙudan kuɗin da suka ƙwace wanda ko bokan ba a kaiwa ba ya yi maganin, kuma sia magana kike kamar kin cika baki da abinci"

Tsaki Momi ta ja dakyar ta ce

"Wane shege ne ya ce miki ban damu da kuɗin ba amma ai lafiya ta fi komai, kuma da kike maganar na saka abinci a baki ba gwara in saka abinci sai dubu a bakin ba da wannan masifaffan dukan da na sha, baki ya kumbura suntum ai wannan sai na nemi mansileta" Ta faɗa tana ƙara bajewa a tsakiyar hanyar domin tana jin idan ba kama-kama aka mata ba to ita dai ba za ta iya tashi ba.

Meenal ta ce

"To da ba ke kaɗai suka duka ba, kalli hancina ji nake kamar jini ne yake zuba duk sun dauje mini, ga fuskata ma sai raɗaɗi take" Momi ta ɗan ɗago kai ta kalli fuskar Meenal wata dariya ta so wwace mata amma bata son ta yi saboda yadda bakinta yake zugi. Ganin Meenal ta yi kamar an yi murjin taliyar hausa a fuskar tata, ga wata ƙasa da ta yi buɗuɗu kamar wanda ta ziyarci yaƙin badar.

Sun jima a kwance a tsakiyar hanyar amma banu wani mahluƙi da ya biyo hanyar ma bare ya taimaka musu, haka suka ba kansu shawarar tashi su lallaɓa.

Momi ɗankwalinta sa yake can gefe ta ɗaukko ta ɗora a kanta ya kalli gabas maso kudu, amma bata damu ba burinta su samu su bar tsakiyar jejin. Haka ta ɗauki mayafinta ta yaɓa a kafaɗa tana riƙe da zaninta da ta tattare tamkar za ta yi tseran gudu. Meenal ma ta lallaɓa ta miƙe tana jin ƙugunta kamar ba a jikinta yake ba,ga shi duk haushi ya cika ta a haka ta ɗauki jakar da banu ko sisi a ciki takaicin ma da har da wayoyinsu aka ƙwace.
Haka suka tashi suna tafiya kamat masu tatata, Momi a gaba zanin nan a tattare a hannunta Meenal tana biye da ita, Meenal ta ce

"Wallahj Momi ina ga mutanen nan ƴan iska ne, ni fa ɗayan nan sai da ya jimƙe hannunsa ya dage ƙarfinsa ya kirɓa mini naushi a mazaunai" Wani gajeran tsaki Momi ta yi ta ce

"Kukan daɗu kike Meenal wallahi allon kafaɗar nan tawa kamar an buga mini filankin katako, wai hannu ne ya yi wannan aiki, ba gwara ma mazaunai wajen tsoka ba ne ni fa wajen ƙashi ne kin ga ai ni na ji abin da na ji, daga rakiya haka kawai an illa ta ni gani nan duk na fita hayyacina" Banza Meenal ta mata don ta ga kamar ma bata damu da abin da ta faɗa ba, haka suke ta tafiya amma sun kasa ganin ko mashin ne.

Suna cikin tafiya sai suka wani ƙaton mutum a amalanken shanu haka suka tare shi dama daga wata hanya ya ɓullo, suna ɗaga masa hannu da maaa magiya sannan ya tsaya, ganinsu a firgice sai ya ƙara ɓata rai, nan Momi ta dage tana sheƙa masa ƙarya cewa zumunci za su je waji kauye m nisa ziyara shi ne suka haɗu da haɗarin ƴan fashi suka musu duka duka musu ƙwace, shi dai bai ce komai ba sai cewa da ya yi su shiga tun da sun nema ya rage musu hanya. Dakyar yake tafiya su dai suna baya sun zazzaunai suna tafiyar dakyar ƙiƙar ƙiƙar.
Suna cikin tafiya tsabar wahala Momi tana jingina bayanta sai kawai gyangyaɗi ya kwashe ta, a cikin bacci ta yi mafarkin sun cim ma mummunar manufarsu, Meenal ta mallaki manyan gidaje da motoci suna mulkar Ibrahim yadda suka so. Meenal da ta kalli Momi tana gyangyaɗi har neman tuntsurawa take sai abin ya ɓata mata rai a nata ganin su da suke cikin wannan yanayin ina suka ga damar wani bacci in banda dai shi bacci ba ka sanin lokacin zuwansa.

Wasu ƴan mata ne suka ɓullo su biyu daga wata siririyar hanya, ya kasance suna gaban su Momi kamar an ce yanmatan su ɗago suka hangi amalanken shanun nan suna ganin mau tuƙawar sai suka kwasa a guje suka koma hanyar da suka fito suna faɗin

"Audu kwarto, Audu kwarto" Momi wannan ihun ne ya falkat da ita daga É—an guntun gyangyaÉ—in ita kuma Meenal sai ta fara tunanin inda kwarton yake, kamar daba sama suka ji muryar mai amlanken ya ce

"Ƙarya suke mini"

Momi a zuciyarta ta ce

'In ba rami mai ya kawo rami?" ,Wato da shi suka tun da kaf dajin babu wani sai shi, kallon kallo aka shiga tsakanin Momi da Meenal don mutumin wani jibgege ne dukwanda ya sake ya damƙe shi to bai isa ya ƙwace ba. Shi kuma ya ji haushin bayyanar ƴanmatan don ya san da gaske suke tin da shi ne yake lalata ƴaƴan mutane.

Momi da ido ta yi wa Meenal signa duk da Meenal ta saba da banbaɗar da mutuncin ta ga maza sai ta ji wannan tana shayinsa shi kuma dama a nasa ƙudurin sai ya ƙarasa fa su gidansa da yake wata hanya zai tilasta musu shiga gidan don zai sanar da su zai ɗauki wani saƙo sai su wuce amma ba saƙo zai ɗauka ba, dama zai sheƙe ayarsa ne a tattare da uwa da ƴar gabaɗaya wato Momi da Meenal.

Momi ba ta yi wata-wata ba ta yi tsalle ta dira ita ma Meenal ta mara mata baya, Audu kwarto sai jin dirarsu ya yi da yake shi ya mayar da hankali gabansa, ai kuwa ya ji haushi domin ya gama sakawa a ransa cewa ya samu mata har biyu kasancewarsa hariji.

Momi suna dira suka yanke wata hanya a guje ko waiwaiye ba sa yi don ita Meenal hatta jakarta ta barta a cikin amalanken shanun, Momi da take ɗingishi lokacin tahowarsa amma yanzu ta ware ƙafa sai zabga gudu take, tsayar da shanun ya yi ya diro duk da girman jikinsa ba ya jin nauyinsa lokacin gudu a kan cikar burinsa don haka ya gwammace ya bi bayansu in ya so idan yana da rabo ko ɗaya ce a cikinsu ya kama a dokar dajin ya biya buƙatarsa.

Meenal ce a baya Momi har ta fi ta ware ƙafa su duka ko ciwon jikin da suka ce suna ji na dukan da ɓarayin kuɗi da wayar nan suka musu ba sa ji, ta ware murya ta ce

"Momi ga shi nan ya biyo mu"

Momi da sauri ta waiwayo sai ta ga ya dage tana sheƙa gudu, su duka ƙafa mai na ci ban baki ba, suka ƙara zage dantse wajen zabgar gudun famfalaƙi. gudu suke babu mai ko takalmi domin sun watsar da su. Ganin yana neman cim musu ya saka Momi ta sha wata kwatar cikin ciyayi ta durƙusa Meenal ma ta mara mata baya, suna durƙushe a wajen suna hakin gudun da suka yi, sai ga Audun ya zo sai dai ya ga hanya ta rabu biyu sannan ya rasa ina suka bi ya duba sawun su ya ga babu hakan ya sa ya ɗan tsaya yana dube dube. Yana tsaye a dab da su sai dai ya basu baya ne, jikinsa yana bashi suna wajen domin bai ga samun su na wucewa ba.

Momi bakinta har kumfa yake wajen karanto ƙulaƙuzai wa to falaƙi da nasi, sai dai a hankli take yi ba a fili ba gudun tonuwar asirinsu. Ita Meenal sai zare ido take tana kallon girmansa hatta mazaunansa kaɗai girmansu sai ya tsorata mutum.

Momi ba ta dakata da adsu,a ba don ba ta san iya mugun nufinsa a kansu ba. Ɗan ja da baya ya yi sai kuwa ya yi wa ƙatuwar ƙafarsa masauki a kan hannun Meenal, wani raɗaɗi ta ji don haka ta shiga zare ido tana ƙoƙarin rafka ihu sai dai Momi tana ta mata nuni da hannu a kan ta rufa musu asiri kar ta yi ihun. haka ta daure tana rausaya kai tamkar mai magogon naƙudar haihuwa. Idanun ya kaɗa ya yi ja sai dai a zuciyarta tana jin kamar ta hankaɗa shi ɗan gyara tsayuwa ya yi hakan ya sa Meenal jin tamkar wanda ya murtsuka ƙafar tasa wato tsananin azaba ya ƙara ratsa ta Momi kuma sai jan addu,a take duk wacce ta zo bakinta daga inda take iya hango gaban rigarsa ya ɗaga sosai daga saitin mararsa hakan ya sa ta yi mugun gani duk da cewa daga gafe ne take hange. Ajiyar da take mararsa tana ta harbin iska da alama a buƙace yake hakan ya tabbatarwa da Momi duk macen da ya damƙa sai ta gwammace kiɗa da karatu.

Meenal tana ta hawaye cikin ikon Allah kamar wanda aka ce ya tafi sai suka ji ya ce

"Ina jin gaba suka yi sai suka samu mafaka shi ya sa ban gan su ba, bari na bi bayansu wataƙika sun sauka daga tsakiyar hanya ne suna bin gefe inda da ciyayi shi ya sa na daina ganin sawunsu" Yana gama faɗar hakan sai ya zabga da gudu ya ci gaba da tafiya. Meenal ta ce

"Momi wayyo hannuna kalli yadda ya kumbura" Momi ta ce
Chapter 92 · 0% Book details