Sashe 66
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai karatu ba sai mutum yana waje ba, a haka ma zai ke kore shaiÉ—anu" Yana shirin bata amsa wayarsa É—aya ta shiga ruri yana dubawa ya ga wannan number ta É—azu wani tsaki ya doka ba tare da ya É—auki wayar ba har kiran ya katse, ita kuma Jidda ko a jikinta don ita a tsarinta babu ruwanta da uzurin miji ko saka masa ido a lamuransa.
Aliya kuma tun lokacin da ya kashe sai da ta ji kamar ta yi kuka, a ranta tana raya cewa wataƙila yana tare da wannan baƙar mummunar matar tasa wacce take saka rai nan gaba kaɗan za ta maida rayuwarta a gidan ta zama tarihi ita kuma ta zama mamallakiyar gidan da mai gidan, idan ma bata jera da ita zaman kishin ba don ta gasa mata aya a hannu sannan ta mata gashin ƙuma wanda da ƙafafunta za ta bar gidan, fatan ta dai kar rabo ya shiga tsakanin Jidda da Ibrahim din ta fi so ita kaɗai ce za ta haifa masa ƴaƴa yadda za su ci gadon dukiya a daidai!.
Ko da ta ɗauki lokaci ma jira take a jima ne ta ƙara kiransa sai dai kuma rashin sa'ar da ta yi ya sa ranta ya ɓaci na ƙin ɗaga kiran da ya yi, sai dai ta yi alƙawarin da sannu zai dawo tafin hannunta ta yadda wurin zama ma sai an nuna masa zai zauna.
Washe gari ta sake gwada sa,arta amma sai bai ɗauka ba, hakan ya sa ta yanke hukuncin buɗe whatsapp ɗin da ta buɗe da sabuwar lambar ta rattaba masa sallama, da kuma gaisuwa tana masa fatan alkairi cikin kalamai na jan hankali, sai dai wuni guda curr bai mata replay ba ita kuma daga an ɗauki ƴan mintina sai ta tura mata hoton emoji na yatsa manuniya alamar tana masa nuni da saƙon da ta tura masa, ta tura masa yatsa ya fi sau goma amma Ibrahim bai mata replay ba kuma tana ganinsa online don saƙon ma ya yi tik biyu alamar an isar masa buɗewa ne kawai bai yi ba.
Ganin haka sai ta yi wa Jidda magana da sabuwar lambar ta whatsapp ta farfaɗa mata maganganu baƙaƙe.
Bayan wata guda ta rasa mafita hakan ya sa suka yi shawara da ita da Amatullahi, ai kuwa Amatullahi ta ce
"Rabu da ɗan iska in laila ta ƙiya sai a koma caca, mu zai yi wa tashin balagar tsintsaye wallahi ya yi kaɗan sai kina mallake shi ƙawata" Amatullahi ta faɗa tana nuna mata daga sun samu kan Naair sai ta kashe aurenta, ita kuma Aliya daɗin shawarar ta ji bata san cewa Amatullahi tana baƙin cikin Aliya ta yi aure ta barta tana gararamba a layi ba, so take ta kashe auren ta zama bazawara su dawo suke yawo a layin tare domin a hankalce ta san Ibrahim ba zai aure ta ba.
Sun shirya ƙarya ita da Amatullahi don haka ta sanar da Kasim cewa za su je duba babar ƙawarsu, shi kuma da yake dama yanzu lallaɓata yake sai hakanya masa daɗi ganin an tambaye shi neman izini. Wajen sha ɗaya na safe suka tafi a napep suka tafi suka je tasha suka hau mota a bakin titi ta ajiye su suka ƙarasa shiga surƙuƙin dajin a ƙafa. Ko da suka ƙarasa wani ɗakin kara ne a dokar dajin a gindin wata bishiya hakan ya sa suka nufi wajen don Amatullahi ta ce ƙawarta ce ta rako wajen aiki take kamar yankan wuƙa don bokanya ce ba boka ba ne ma.
Tun kan su ƙarasa ciki ɗakin bukkar da yake kewaye da kara sai jikin Aliya ya fara karkarwa amma Amatullahi ta harare ta tana nuna mata cewa ranar biyan buƙata rai ba a bakin koma yake ba.
An sanar da su su cire takalmi sannan da baya -baya za su shiga sainda suka shiga saura kaɗan Aliya ta taka faifan gaban bokanya mai ɗauke da ƙasa a ka tsawar da aka mata ta matsa gaba da sauri sai da ta musu umarnin juyowa sannan suka juya suka zauna. Kafin su fara bayani ta sanar da su ta san da abin da suke tafe, Aliya sai kallon baƙar matar take wacce babu alamun ɗigon imani a wajenta nan ta ce
"Zan yi miki aiki kuma za a samu biyan buƙata idan har buƙata bata biya ba to ba daga garemu ba ne kin saɓa lamba ne, amma matuƙar kika yi yadda na ce to an wuce wajen" Kai Aliya take kaɗawa kamar ƙadangaruwa sannan sai bokanya ta ce
"Za ki kawo mini cokalin da yake cin abinci da shi a jikin cokalin zan yi aikin, sai kuma ki mayar da cokali a tabbatar ya ci abinci da shi idan haka ta faru to ƙurunƙussss!.
Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Amatullahi da Aliya jin wata gadar zare da aka musu, ita Aliya tunanin da ta farw ta yaya za ta gane cokalin da yakencin abinci sannan har ta mayar ta tabbatar ya ci abinci wannan ai abu ne mai wahala tana cikin wannan maganar muryar bokanya ta katse ta da faÉ—in
"Ba ma magana a musa mana, komai muka faÉ—a sai an aikata in ba haka ba akwai yiwuwar ciwon hauka ga mutumin da ya zo neman taimako wajenmu kuma bai yi abin da aka ce ba"
Didididiiimmmm gaban Aliya ya buga da ƙarfi idanunta suka ciko da ƙwalla.
MAMAN AFRAH
0902557622
https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=hqrt1
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE2ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
MEENAL
Rai a ɓace ta saka hannunta ta riƙe hannun Hajiya wanda takaici ya sa Hajiya ta fashe da kukan takaici bata taɓa zaton akwai irin wannan tanar da har matar ɗanta za ta riƙe mata hannu ba. Nasir da sauri ya fito daga motar ya nufi su yana faɗin
"Meenal ki saka mata hannu" Haka Meenal maimakon ta saki hannun sai ta warɓar da hannun, ita kuma Hajiya sai ta fara tunanin tun da har Meenal ta iya riƙe mata hannu ta warɓar da alama ko marin nata ta yi ba za ta ajiye hannunta ba za ta rama. Faɗa Hajiya take yi kamar za ta ari baki sai Meenal ta kalle ta ta ce
"Hajiya da kin adana kalamanki wataƙila nan gaba za su miki amfani, don yanzu aka fara wasan, sannan ki mayar da wuƙar ni ba zuwa gidan ki zan yi ɗaukan dankali ba, amma ki sani ɗan naki dai da bakya so a ɓanɓare shi, shi zai ƙara cire wasu kuɗin ya siyo kuma muddin kuna so ku ci dankali sai dai ƴaƴanki su zo su soya a tsakura muku don ni ba baiwa kuka ajiye ba" Tana faɗar haka ta juya ta shige gidan. Bak sake Hajiya ta bi bayan Meenal da kakko yadda ta tafi tana karkaɗa mazaunai irin na yaran da suka riƙa a rashin ta ido.
Nasir ne cikin sanyin murya ya ce
"Ki yi haƙuri Hajia... Kafin ya gama faɗa ta katse shi da faɗin
"Haƙurin da ta mutu sadakar nawa ka bani? Kana raye za a yi min cin kashi Nasir har ni matarka za ta ce wai za ake tsakurawa abinci kamar wata almajira" Shi dai baki yake bata amma ta yi banza da shi hatta motar tasa ta ƙi shiga.
Napep ta tare ta nufi gida ta je tana ta kumfar baki su Husna suna taya ta, sai da yamma ya shirya ta nufi gidan ƙawarta mahaifiyar Meenal ko da ta je baƙi basu gama watsewa ba wasu kuma suna ya shigowa yin Allah sanya alheri.
Tana shigowa Momi ta hau mata lale marhabin tana faÉ—in
"Ka ga manyan mata maganin ƙanana ƙanana, ka ga ƙirjin biki uwar amarya uwar ango"Dariyar yaƙe kawai Hajiya ta yi ta nemi wuri ta zauna sai da aka kira magriba ƙafa ta fara ɗaukewa sannan Hajiya suka keɓe da Momi Hajiya ta ce
"Ƙawata akwai matsala wallahi" Cike da nuna damuwa Momi ta ce
"Subhanallahi Allah rabamu da matsala mai ya faru?"
Hajiya ta ce
"Wallahi yarinyar nan Meenal ina ga an samu wasu ƙawaye mararsa imani da tarbiya sun bata sabon darasi da shawarwari a kan zaman gidan miji da kuma uwar miji ganaɗaya ta sauya halayya"
Momi ta hau faÉ—in
"Innalillahi wa inna ilaihi raji,un wane ƙawaye ne wannan waye ya miki wannan bayanin"
Hajiya ta ce
"Ni da idona na gani" Ta faɗa tana kwashe komai ta faɗawa Momo, Momi ta ringa tafa hannuwa tana salallami tana faɗin amma dai bata ɗauki shawarar ƙwarai ba. Hajiya sai ta ga ma yadda take zaton Momin za ta ɗauki maganar sai ta ga bai kai hakan ba, sai ta fara tunanin ko dai son kai ne.
Hajiya ta ce
"Yanzu mene ne mafita?"
Momi ta ce
"To wace itin mafita kuma ai tun da har ƙawaye suka ɗorata a kan wata turba wacce ba tarbiyar gidansu ba sai dai a hankali a fahimtar da ita kin san yaran yanzu, dama fa kana tarbiya sai kana haɗawa da addua amma ƙawaye da abokai su ne matakin farko na warware saƙar da ka ɗauki lokaci kana yi shi ya sa ake so iyaye sukr saka idanu a kan ƴaƴa su ga waye abokinsu kuma su waye ƙawayensu" Baki ta saki tana kallonta ai a ganinta wannan son kai ne ta ɗauka Momin za ta kira Meenal ko a waya ne ta kutuntuma mata ashar ta ƙara fahimtar da ita matsayin Hajiya amma sai ta ga abin ya sha bamban.
Haka ta baro gidan ranta babu daɗi tana tunanin mafita don ba za ta ƙyale wannan abinnya tafi a haka ba amma za ta ɗauki mataki kawai bata so ne zumuncin su ya yi rauni amma duk da hakansai dai zumuncin ya gurɓace.
Ko da Hajiya ta tafi Momi ta kira Meenal ta faɗe mata biri har wutsiya nan ta ƙara zugata da jaddada mata kar ta sake ta saki jiki a rainata, kar ma ta yarda a ga makwancinta ta ƙwaci ƴancin ta duk wanda ya ce kule ta ce casss!.