← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 106

Sashe 44

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ALIYA
Ranta yana ƙuna ta ji Umma ta ce
"Tsakaninki da Allah Aliya ko dai don kin daina ra,ayinsa kika faɗi haka Aliya ban da sharri" Umma ta faɗa tana yin ƙasa da murya don tuni idanunta sun raina fata sun yi jawur kamar ta sha ƙwayar da ta fi ƙarfin kanta.
Aliya tana kuka ƙasa-ƙasa ta ce
"Umma wallahi ganin idona Kasim ba asalin namiji ba ne" Umma cike da ruÉ—u ta ce
"Ya aka yi kika gane Aliya kar fa ki yi abu da ka" Aliya tana jin tamkar dai ta shiga kwakwalwar Umma ta cusa mata abinnda take so ta fahimta. Ta ce
"Umma idan baki yarda ba in koma ɗakin in ɗakko miki hotonsa ki ga zahir... Tun bata ƙarasa ba Umma ta ce
"Kina da hankali Aliya ina ni ina ganin gaban siriki tsakani da Allah wannan ai mugun ji ne, to ke in ban da ma tonon silili Aliya amarya tana langwaɓewa namiji ya mata bauta a daren farko amma ke kin... Aliya ta katse Umma da faɗin
"Umma ana ga yaƙi kina ga ƙura Umma ba zan taɓa zama da mata maza a matsayin miji ba" Umma tana ƙara da murya ta ce
"Aliya kar fa kisa in ke ɗaga murya kin san dai akwai sauran ƴan biki da basu tafi ba suna ɗakinku ku, dama jiyaa ana ta batun kyawun gidan Jidda ke babu ma wanda yake batun ki in dai aka sako maganar gidanki sai dai in zancen mutuwar inji za a yi haka jiya na sha ƙunsar takaici, dakyae bacci ɓarawo ya sureni wallahi cikin baccina na yi mafarki ke kin koma gidan Jidda matsayin matar Ibrahim ita kuma ta koma gidan Kasim matsayin matarsa " Aliya ta ce
"Ai haka ne ma Umma wannan ba gidan zamana ba ne babu wani kyau da armashi ga miji yana ɗauke da baƙar ƙaddara, ni dai Umma ki faɗawa Abba ana jimawa daga gari ya waye zan taho gi.. Umma ta katse mata hanzari da faɗin
"Aliya ki rufa min asiri wallahi kinnsan dai halin Abbanku, sannan tonuwar asiri ne a ce kin fito a ranar da kika yi kwana ɗaya da tarewa a gidan miji, ƙaramar bazawara kike son zama?" Aliya ta rushe da kuka ta ce
"Ni dai ba zan zauna in haifi mata maza ba" Umma ta ce
"Aliya wa ya faɗa miki ana gadon haihuwar mata maza? Ai baba gadon haihuwar kawai dai halitta ce amma ba a gado" Umma ta faɗa cike da son ganin ra lallaɓa ta duk da ta san tabbas gaskiya ta faɗa ba a gadon haihuwar amma dai ita yanzu duk ta rasa nutsuwa in ta tuno Jidda tana can maƙure da nata mijin a gidan daula cikin kwanciyar hankali sai ta yi ta tsine mata a zuciyarta.
Sun jima suna waya Aliya tana kuka Umma tana lallashin ta duk da ita ma kaɗan ya rage ta rushe da kukan, amma ta bari sai bayan sun gama wayar ta keɓe ta sharɓi kukanta son ranta, suna cikin wayar Abba ya shigo da sallama da sauri Umma ta danne makunnar wayar har sai da wayar ta mutu, tana kirkirar murmushi tare da ɗauke kai kar ya ga fuskarta.
Aliya kuwa ko da ta ji wayar ta ɗauke ta sauke ta daga kunnenta ta duba aai ta ga kiran ne ya katse, ƙara kiran Umma ta yi amma sai ta ji wayar a kashe, hakan ya sa ta fito daga kicin ɗin har wani duhu take gani tsabar ɓacin rai ta nufi ɗakin tana tuna irin uƙubar da za ta shayar da Kasim a zaman ta d shi a gidan, tun da har shi ya ga ya ji ya gani.
Tana shiga ɗakin ta ɗauki riga ta saka har lokacin yana bacci sai jan munshari yake, wani haushinsa ya turnuƙe Aliya ta tsaya tana ƙare masa kallo, Kasim bawan Allah kamar ya san mai take ya ɗan yi juyi kaɗan, sai kuwa ya ɗan yamutsa fuska kafin ya buɗe idanunsa tarrr a kan Aliya wacce take tsaye riƙe da ƙugu tana jifansa da mugun kallo hawaye yana zuba kamar an buɗe famfo. Sai lokacin ma ya gama wartsakewa da sauri ya lura da babu kaya jikinsa faɗuwar gabansa ya tsananta tunowa da ya yi cewa akwai ɓoyayyan al,amarin da yake tare da shi wanda Aliya bata sani ba.
A kiÉ—ime ya tashi zaune tare da rarumo gefen zanin gadon ya rufa a gabansa...

MAMAN AFRAH
09015576222

https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=wwt

*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 1️⃣5️⃣

SADIYA
Tun da Baba ya fita ta fara zuwa tana gaishe da matan gidan cike da girmamawa, duk cikin ƴaƴan gidan babu mai haƙuri da ladabi da biyayyar Sadiya tamkar dai ba a gidan take ba, don Sadiya daban ce a cikin ƴaƴan gidan ta kowane fanni. Lokacin sa ta je ta gaishe da Mama Habiba har za ta tafi Mama wacce ta ɗauki Kalifa ta ɗora cinya tana cewa
"Tun da dai baka son in É—auke ka to zan maka saki uku"Ta faÉ—a tana dariya shi ma dariyar yake duk da bai san manufar maganar tata ba amma dai ya gane wasa take masa. Mama Habiba ta kalli Sadiya da take zaune kusa da ita ta ce
"Sadiya ki ci gaba da haƙuri a gidan aurenki, ki sani aljanna kike nema duk wani abu da namiji zai ƙunsa miki na baƙin ciki da ɓacin rai to ki sani wannan ɗacin da za ki ji a zuciyarki idan kika danne Allah zai baki ladan haƙuri sannan shi aure dama ɗan haƙuri ne, ita aljanna ba a samunta ta sauƙi, kuma duk ko da a ce mutum ya tauye maka haƙƙi ko yana maka abubuwa da gangan idan ka yi haƙuri wataran za ka ci riba. Na sanki da haƙuri to ki ci gaba wataran in har muna raye za ki ce na faɗa miki domin sai kin ga sakamakon haƙuri da juriyar da kika yi" Sadiya ta ɗago kai ta kalli Mama Habiba idanun Sadiya suka cika da ƙwalla tana jin Mama Habiba tamkar dai mahaifiyarta Mama Habiba tana mata abin da Mamarta bata mata, tana nusar da ita abubuwa masu yawa. Cike da rawar murya ta ce
"In sha Allahu Mama, na gode sosai ina alfahri da ke" Hannu Mama ta kai ta dafa kafaÉ—ar Sadiya ra ce
"Babu komai Sadiya haƙuri ba ya taɓa yin tawa ko kuma a ce ya ƙare ita dama rayuwar cike take da ƙalubale, kowa da jarawabarsa haka kowa da ƙaddararsa wata ƙaddararta rashin samun mijin auren, wata kuma ta samu amma kuma babu kwanciyar hankali, wata kuma kishiya ce matsalarta ta hana ta sakat ta hana ta zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta kange komai ta hana ƴaƴanta su wayata" Sadiya kai kawai take gyaɗawa kamar ƙadangaruwa don ta san duk abin da Mama take faɗa haka yake!.
Suna cikin hakan ta ce ta je ta yi alwala, alwalar ta yi ta dawo ɗakin ita ma Mama ta yi suka tada sallah shi kuma Kalifa yana zaune yana cin biskit ɗin da Mama Habiba ta ɗakko ta ɓarw ta bashi. Bayan sun idar Mamar ta ci gaba da mata nasiha a kan kishiyar da za a mata tana ta nuna mata yadda za ta yi ta zauna lafiya duk da ta san Sadiya bata da hayaniya kuma tana da kawar da kai amma dai dole ta ƙara koyawa kanta juriya kasancewar yanzu abubuwa za au sauya idan da mijinta ne matsalarta yanzu kuma wata za ta shigo gidan kuma ba a san da mai za ta shigo ba, galibi ko yawanci mata ba wai suna tsoron kishiya ba ne sai dai suna tsorob da mai za ta shigo? Shin zaman lafiya ne zai kawo ta ko kuma kawai zuwa za ta yi ta hargitsa gidan, wata sai ta fitar da matar gidan kuma ta zo ta bar gidan, shi ya sa kishiya kala-kala ce wata ta zaman lafiya wata akasin haka.
Sadiya ji take tamkar a cikin ƙwaƙwalwarta Mama take kissima maganganun, don sosai suke shigarta, duk da kasancewarta wacce ta taso a gidan kishiyoyi har huɗu amma dai shi zaman aure makaranta ce mai zaman kanta da babu wacce za ta fane sai wacce ta yi auren, kazalika kishiya ma abu ce mai zaman kanta da babu wacce za ta fahimci zama da ita sai wacce aka yi wa duk da ba a taru zan zama ɗaya ba, tun da ita Sadiyar shaida ce tun da gashi yanzu kishiyar mahaifiyartw ce take nusantar da ita. Ba wai don tata mahaifiyar bata gidan ba, tun da da ta gaishe da Mamar ta je wajen Mama Habibar.
Chapter 44 · 0% Book details