← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 106

Sashe 25

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kasim ina zuwa za mu yi magana an jima akwai gwarama" Kafin ya bata amsa ƙit ya ji ta kashe wayar.Zaman dirshan ya yi a saman katifarsa yana jin wani faɗuwar gaba yana fatan dai kar idan ta ga nata kayan ta ce ta fasa aurensa, tun da dai ya ga gashi nan tana yi wa Jidda dariyar an kawo mata kaya a baro.

A ƙofa mai baron ya tsayar da baron inda su kuma masu kawo kayan su Abba suke musu marhabin, a daidai lokacin wannan da Amatullahi da Aliya suka diro daga saman bencin da suka taka suka fito tsakar gida a sukwane suna haɗa baki wajen faɗi

"Umma wallahi kayan Jidda a baro aka kawo, kuma akwati biyu da kit" Daga Umma har ƙawayenta guda biyu wata guɗa suka saki a tare sai bayan sun yi suka tuntsure da dariya har da tafawa, kafi suka yi ayari suka shige ɗakin tare da su Aliya, domin su ƙyaƙyata dariya son ransu gudun kar su Abba suke jiyo tsegumin da za su yi.

Suna ta dariyar ƙeta inda Umma ta ce wallahi sai ta ga ƙwal uwar daka don sai ta ga baron ma, haka aka riƙe mata ta ɗane katakon har ɗaya ƙawarta tana faɗin da kin yi haƙuri har gida za a shigo da su. Tana hawa ta yi ido huɗu da baro lokacin mai baron yana sakko da akwatunan, dariya har da hawaye garin dariya kaɗan ta faɗo daga saman bencin haka ta diro har tana cewa su Aliya suke sassauta murya kar Abbansu ya san suna gidan tun da kamar rashin kunya ne a kawo maka kaya kana gida.

Su Umma a ɗakin suka bar su Aliya suka fito waje suka zauna suna ƙusƙus ransu fari ƙal suna fatan ba abin arziƙi ba ne a akwati biyun don a ganinsu lefen ma kamar na bazawara. Su Umma suna fita su Aliya suka koma saman bencin suka kasa suka tsare a windwon kamar a mafarki kyawawan motocin suka yi wa layin tsincke kowacce tana fitar da ƙyalli na sabunta, a jere suke iya ganinka dole su birgeka daga Amatullahi har Aliya mutuwar tsaye suka yi baki sake domin motocin su tafi da su, sai dai abin da ya sa suka shiga ruɗu shi ne motocin basu tsaya a ko ina ba sai a ƙofar gidan su Aliya, kallon kallo aka shiga yi tsakanin Aliya da ƙawarta, bakin Aliya kamar ƙofar gari ya ƙi rufuwa sam saboda mamaki tana tunani a ranta cewa dama Kasim har yana da abokan da suke da motoci na alfarma haka, amma bata taɓa ganin sun zo da su wajenta ba ko dai abokan nasa ne suka masa hanya ya samo wannan motocin irin wanda take mafarkin samu, ko da sau ɗaya ne tak ta shiga ciki ta yawata, amma kash! Bata da wannan damar, basu tsinke da lamarin ba sai da suka fara ganin mutanen ciki suna fitowa suka ga gabaɗaya babu kalar talauci a cikinsu sai kuma direbobin da suka fito suna buɗe ƙofofin motocin inda guda ɗaya direba ya saka hannu ya fito da wata ɗirkekiyar akwati wacce kai kana gani ka san an kashe maƙudan kuɗi wajen sayan akwatin kaɗai, jikin Aliya karkarwa ya fara saboda farinciki jin ta take tana yawo a cikin gajimare.

Yadda ake ta fito da akwatin nan kala-kala ne ya sa ta tabbatar cewa ba iya goshi ta yi ba har da ƙeya!. Da sauri ta diro daga saman bencin ta tsaya a tsakar ɗakin hannunta yana karkarwa ta dokawa Kasim waya, Kasim wansa yake kwance lifet a katifa yana jiran kiran ko ta kwana daga Aliya jin ƙaran wayarsa gabansa ya ninku da faɗuwa amma haka ya daure ganin sunanta ya ɗauki wayar ya danna ya kara a kunne kamar daga sama ya ji muryarta rana faɗin

"Na gode Kasim, na gode!. Na gode, wallahi na matuƙae gode ina sonka Kasim zan rayu da kai har ƙarshen rayuwata!" Bata jira ya ce komai ba ta kashe wayar don bata cikin nutsuwar da za ta tsaya ta ji mai zai ce. Lokacin da take wayar nan Amatullahi ta diro daga saman bencin ta yi tsakar gida tana faɗin

"Umma wallahi a motoci haɗaɗɗu aka kawo kayan Aliya, kuma akwatunan ni kaina ban iya irga yawansu ba, kamar ma va set ɗaya ba kuma ba biyu ba ni ban ma san nawa ba ne kuma ma su tsada!" Wata wawiyar guɗa Umma ta saki sai da ta yi uku a jere ƙawayenta suna taya ta, inda Aliya da Amatallahi suka haɗu da su Umma aka rungume juna!. Bayan an gama murna su Aliya suka koma ɗaki.

Jim kaɗan wasu samari guda biyu suka shigo ɗaya yana riƙe da akwati ɗaya, ɗayan kuma akwati da kit ɗin nan su ne kayan da aka kawo a baro. Bakin Umma a washe ta nuna musu kan ƙaramar tabarma da take shimfiɗe a gefe ta ce su ajiye, suna ajiyewa har rige-rigen tsegumin mene ne a ciki suke.

Suna fita aka fara shigo da akwatuna masu kyau wannan karon samarin guda huɗu ne suke shigowa da akwatunan, Umma garin saurin ɗakko manyan tabarmi har zaninta neman faɗuwa yakr duk sun ruɗe don Aliya da take windown da yake tsakar gidan suna leƙowa daga falon Umma har ta fara tunanin ko dai dama Kasim mai kuɗi ne ya rufe ta amma daga ganin kayan abin ya fi gaban wasa an kashe naira.

Dozin biyu haka aka jere a gefe Aliya ko zama ta kasa yi da mazaunanta hango irin iyayin da za ta ɗiga take a wajen ƙawayenta. Wayar Jidda ta kira da Jiida ta ɗauka ta ce

"Jidda an kawo akwatunan ki guda biyu da ƙaramin kit" Buɗar bakin Jidda sai ta ce

"Ubangiji ya sa albarka a auren" Wani uban tsaki Aliya ta ja kafin ta kashe wayar tana kiran Jidda da Æ´ar wahala!.

Atamafa kala takwas leshi kala biyar shadda uku material uku, takalmi da jaka kala biyu sai takalmi marar jaka kala biyar mayafai buyar hijabi huɗu, sai sauran tarkacen kayan shafawa da sarƙoƙi ƙaramar kit kuwa qur'ani ne da sallaya. Su ne kayan da suke cikin akwatunan biyu kayan bacci ma huɗu ne da kuma under wears.

Akwatunan kuwa na leshi da ban akwatin atamfofi da ban kaya ne iya ganinka kamar hauka, hatta sarƙar gwal ma kala uku ce a ciki tun su Umma suna ganin kayan da marmari har suka gaji da ɗagawa kawai faɗi suke shikenan Aliya da Umma sunw arke. Aliya kamar wanda taɓi ya same ta gami take za a taɓa ta a ce ta tashi daga nannauyan baccin da take, a nata ganin kawai mafarki ne take yi.

Baba kuwa daga zauren gaba suka yi saboda bayan masu kawo kayannsun tafi sai mata suka fara tururuwar zuwa daga maƙota, Umma ta maƙale gwal a cinyarta sai dai a gani a bata don mutane da suka cika gidan wasu ko akwatunan nan masu biyu da kit wato na Aliya wanda suke a mazaunin na Jidda babu wanda yakr ɗagawa kowa kayan akwatunan nan yake gani wanda suka san iyayen Kasim suna mamakin inda Kasim ya tara wannan dukiyar da ya yi wanna kayan kamar an buɗe shago!.

Ibrahim ya kasa tsaye ya kasa zaune jira yake ya ji ta bakin Jidda kar ta janye ƙudurin aurensa idan ta san waye shi, hakan ya sa bini-bini sai ya buga mata waya amma sai ya ji bata ce masa komai ba, sai dai ta ce masa har yanzu tana gidan su Salama.

Sai da aka yi isha'i Abba ya shigo gidan, lokacin Aliya har ta gaji da gwada tsadaddun abayoyin Jidda na lefe wanda take tunanin nata ne, takalmi da jaka ma har rasa wanne za ta gwada ta yi ga sarƙoƙi fassion abin kawai ba a magana komai ya yi. Jin motsin zuwan Abba hakan ya sa ta gudu ɗaki don dama Amatallahi tuni ta tafi gida tana faɗin sai ta dawo ganin kaya na biyu don ta fi so sai ta zo ta musu ɗai-ɗai za ta gani.

Lokacin da Baba ya zo gabaɗaya an ajiye akwatunan a waje ɗaya sai sheƙi suke, ga guda biyu da kit su ma a gefe don ba a ma haɗa su waje guda ba. Bayan ya zauna ya ci abinci Umma tana ta masa surutu kamar za ta ari baki, sai faman faɗin Aliya ta sha kaya take ta yi sai kuma ta ce Jidda ma ba laifi tana yin hakan ne don kar Abba ya ce ta nuna bambanci tsakaninsu.

Tana ta faɗa masa abubuwan da suke ciki a daidai nan ne Jidda da Salama suka yi sallama suka shigo bayan an amsa. Abba suka gaisa da shi sai suka shige ɗaki, yau ko fuska Aliya bata tanke musu ba sai ma labarin uban kayan da aka zuba mata a lefe take basu akwatuna 24 Jidda sosai ta ji farincikin jin Aliya ta samu kaya masu yawa, suna cikin haka Umma ta dage ta ƙwalawa Salama kira Salamar da Umma ta tsani ma ta ga ta zo gidan amma yau saboda tana so ta mata kaju kuma ta tura mata haushi. Amsawa Salamar ta yi ta fito ta zo cike da ladabi ta ce

"Umma gani"

Umma ta ce

"Cewa na yi to kya shiga ɗaki ai sai ki zo ki ga kayan ƙawar taki da na ƴar uwarta idan kina ɗagawa ma har Abban naku ya gani shi ma yanzu ya shigo" Abba ya murmusa yana jin daɗin yadda Ummar bata nuna bambanci ba ya ga tana farinciki da abubuwan da kowa ya samu ashe dai ta yarda kowa rabonsa yakw samu, tunaninsa ko za ta ji ƙyashi ashe ma gurguwar fahimta ya mata da ya ƙi bayyana kuɗin da aka kawo.

Salama ta durƙusa a gaban akwatunan da Ibrahim ya yi Umma ta yi karaf ta ce

"Ke kuwa ai da kin fara da na ƙawar taki" Ta faɗa tana nunawa Salama akwatunan nan guda biyu wanda Kasim ya kawo har da cewa
Chapter 25 · 0% Book details