← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 106

Sashe 1

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=ems_copy_t

*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 1️⃣

*JAN HANKALI GA MASU BIBIYAR LABARIN NAN*

*Labari ne da yake ɗauke da ɓangare uku, kowane ɓangare akwai muhimmiyar rawar da zai *taka. Labarin manyan taurarin cikin littafin guda uku wacce kowacce ɓangaren ta akwai tarin abubuwan da za mu yi nutso a ciki, muna da labarin ZALIKA, akwai labarin SADIYA, sannan akwai labarin JIDDA sai dai in ce ku biyo ni sannu a hakali domin jin da mai labaran nasu zai zo NGD* .

Da sallama Malam Bala ya shigo gidan nasa, wanda yake sallamar kamar zai tsaga gidan, Mama Habiba da take kwalfar ruwa ta É—ago tana amsa masa a inda ya mata kallo É—aya ya doka uban tsaki tare da É—auke kai.

Ƴan matan gidan ya shiga kwaɗawa kira ɗaya bayan ɗaya, kowacce tana ɗakin nasu da aka warr musu a gidan, jin kiran Aisha ta yatsina fuska ta ce

"To fa! Watan cin ubanmu ya kama mun shiga uku yanzu Baba zai fara faÉ—an nashi bari mu je mu ji da mai ya zo"

Malika ta taɓe baki tare da ci gaba da danna waya, haka suka fito sumi-sumi kowacce ta zo a ɗarare ta zauna a kan tabarmar gabansa ganin ya koma kan kujerar plastic ya zauna.

Wani ƙullin magani ya fito daga cikin babbar rigarsa ƙullin ƙato ne ya ce

"Kai ni dai na shiga uku! Allah ka bani ɗa namiji ko kangararre ne!" Mama Habiba da ta ji sautin maganrsa ya sosa ranta duk da ba yau ne ta fara jin wannan furucin nasa ba, amma dai kullum furucin yana zama tamkar sabo ne a kunnuwan ta. Gabaɗaya ƴan mata sai kowacce ta sunkuyar da kai kasancewar daga su har iyayansu suna matuƙar tsoron Baba, saboda ba ya ragawa kowa. Cikin sanyin murya Mama Habiba ta ce

"Haba Malam ka daina wannan maganar wallahi babu daÉ—in sauraro, haba kowane jinsi ma ai kyauta ce ta ...

Wata tsawa da ya doka mata ya sanya sauran maganar da ta guntso za ta amaryar masa ta haÉ—iye, a fusace ya ce

"Habiba ina miki kashedi koyaushe a kan shiga sabgata da Æ´aÆ´ana bakya ji ko? Mai ya sa kike saka baki a abin da babu ruwanki? Ko namijin da na ce a bani ke na tambaya ki ban?" Kai ta shiga girgizawa ya ci gaba da faÉ—in

"To ahir ɗinki, Allah na ce ya bani ɗa namiji ko kangararre ne ba ke ba, ai ko maganar ce ki bari masu haihuwa su faɗa amma ke da baki da ko ƙuda a gidan ina ruwanki" Kai ta sunkuyar idanunta suna kawo ƙwalla tana jin zafi da ɗacin gorin Malam duk da ta san Allah ne yake bada haihuwa kuma shi yake hanawa ta yi imani da hakan amma gorin mijinta yana ci mata tuwo a ƙwarya, saboda tana ganin da a ce shi ne ba ya haihuwa ko a haka za su dawwama to ba za ta taɓa masa gori ba kuma za ta rungumi ƙaddara ta zauna da shi har ƙarshen bugun numfashin ta, amma shi ban da kishiyoyi uku da ya mata har sai yana mata bita da ƙulli dulan kabarin kishiya.

Mama Talatuwa da ta firo daga É—akinta jin abin da yake faruwa duk da ba wannan ne karon farko ba, amma koyaushe idan yana yi wa Habiba cin kashin nan tana jin babu daÉ—i a ranta, haka ta fito tana nufar wajen da Habibar take don ta bata baki, sai dai tana dab da zuwa ta tsumayi maganar Malam yana cewa

"To uwar ƴan tausayi me raunatacciyar zuciya, ke irin kishin nan ma na mata bakya yi, bakya jin daɗi mijin ki ya duzga kishiyarki, sai ki yi kamar wanda aka taɓa wata ƴar uwarki ta jini" Juyowa ta yi cikin sanyin murya ta ce

"Haba Malam ai duk mace mai hankali ba za ta so ta ji daÉ—in don mijin ta yana tozarta kishiyarta ba, domin rayuwar duniya yau gare ka ne gobe ga waninka, kenan ni ma jifa zai iya zuwa kaina ko in ce... Hannun da ya É—aga mata ya sa ta yi shiru ya ce

"Ki ciko bokiti da ruwa ki kawo min" Da to ta amsa tana kallon Habiba da tausayawa ta nufi wajen ruwan za ta ɗakko, Mama Habiba kuwa sai ta kama hanyar ɗakin ta tana jin tamkar an ajiye mata dutsi a ƙirjinta na gorin haihuwar nan kasancewar ta mace mai son yara sai kuma ƙaddararta ta kasance ta rashin haihuwa, sannan mijin ta ba ya tausaya mata a kan rashin haihuwar sai dai ya yi ta yada mata baƙar magana tamkar ita ta hana kanta haihuwar.

Mama Talatuwa bokitin ta ɗakko me cike da ruwa ta kawo gabansa ta ajiye tana kallon ƴan matan yadda kowacce fuskarta cike da damuwa. Ledar ya since ya zazzage maganin kofuna guda biyu ya sa Hafsa ta ɗakko ya gauraya ya cika kofin ya miƙawa Hafsa ya ce

"Karɓi ki kafa kai ki shanye ki miƙo min, ai ni zama bai ganni ba wallahi tun da na ajiye ƴanmata kamarku a gida babu mashinshini, dole na nemi maganin farin jini ko a samu masu kwasa in kawar da ku in huta da raina, amma yara sai shagen baƙin jini, ni dai ba ni kuka biyo ba sai dai iyayenku mata tun da ni dai gashi nan sai dai na rufe ƙofa wato na auri mata huɗu, da ina da baƙin jini wa zai aureni"? Ya faɗa yana musu wani kallo ba yabo ba fallasa kowacce kai ta sunkuyar suna jin babu daɗi a ransu tun da cikin su babu wacce ta haura shekara ashin wasu ma sha takwas suke amma saboda ya ƙwallfa rai a kan su ko kaɗan ya hana kansa sukuni.

Hafsa da kurɓa ɗaya ta yi wa maganin ta ji wani uban ɗaci har tsakar kanta, da hanzari ta cire kofin daga bakinta tana mayar da kallon ta kan mahaifin ta cike da tsoro, a fusace ya ce

"Kin shanye kin miƙo kofin ko kuwa" Cike da tsoro ta ce

"Baba wallahi maganin nan ɗaci ne da shi, na jiya ma da na sha gudawa ya sakani" Ta faɗa tana kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka.

Kafin Baba ya furta wani abu Malika ta yi karaf ta ce

"Wallahi Baba ko ni jiya wanda ka bamu da daddare cikina ya yi ta ciwo, kuma ma fa Baba shan magani ba bisa ƙa,ida ba yana da haɗari ga lafiyar jiki, sannan magungunan nan masu ɗaci idan ba likita ko wani masani ne ya bayar ba yawan shan masu ɗacin nan ba bisa ƙa,ida ba yana iya sakawa mutum ciwon hanta, idan akwai sinadarai masu illa lalata hanta ko ƙoda yake, duk da wasu magungunan masu inganci suna da tasiri in an yi amfani da su bisa ƙa,ida... Hannun da Baba ya ɗaga mata ne ya dakatar da ita daga ƙarasa maganar yana nuna su da yatsa ya ce

"Ba ɗaci ba ko maɗaci ne kan ɗaci sai kun sha maganin farin jinin samarin nan, ina zan iya duka mata kun cika min gida, shiga goma zan yi gidan nan sai gabama ya faɗi in na ganku, kowacce ya ci a ce tana gidan mijin ta amma ƴaƴa shida duka mata kuma ɗaya na aurar haba kamar dai wanda aka mini baki, ai ina roƙon Allah ya bani ɗa namiji duk lalacewar namiji ka amfane shi, duk kangararsa wataran zai maka magani amma mace fa?" Ya faɗa yana bin su da kallo, Mama Talatu da take gefe tsaye kamar mai jiran tsammani don tana tsoron ta bar wajen ya ce ta raina shi, cikin sanyin hali da na muryarta ta ce

"Haba Malam don girman Allah ka daina wannan maganar, kowane ɗa yana da ranarsa, kawai mutum ya yi addu'ar Allah bashi na gari sannan ya nema musu shiriya da kuma saka musu albarka, wani sa'in mace ma ta fi wani namijin jin ƙai da taimakon, amma kana maganar kangararran ɗa to ta ina zai tallafa maka ɗin tun da a kangare yake? Mace ma tana da tata ranar kuma wasu ma suna nan suna neman haihuwa ido rufe amma bai kamta kai da Allah ya azurtaka da su kake wannan furu... Tsaye ya miƙe a zafafe ya nuna Mama Talatu da yatsa ya ce

"Keee! Kin san dai babu abin da za ki nuna mini na sanin abin da ya dace ko wanda ya kamata saboda haka kar na ƙara jin bakin ki" Yana kaiwa nan ya koma ya zauna.

Kallo ɗaya ya yi wa Hafsa da ta kafa kofin sai da ta shanye tasss ta miƙa masa ya kwalfo ya ba Malika sai da ta runtse ido ta shanye ta miƙa masa kofin, kowa ya sha saura Arfat da ya miƙa mata tana yin kurɓa ɗaya amai ya yunƙuro ta da sauri ta cire kofin a bakinta tana saka hannu ya toshe bakin, jin aman yan barazanar zubowa ta ajiye kofin a wajen ta miƙe a hanzarce ta bar wajen sai da ta gama aman ta dawo Baba yana sababi ya ce

"Wato ke kece shafaffiya da mai, kullum in zan bayar da magani ke ce mai yi wa mutane amai, uwarki ta É—aure miki tsantsa a kan cewa wai tu tana goyonki kike amayar da magani ko da na asibiti ne ko É—ura miki aka yi sai ya dawo, É—auke wannan maganin ki shanye kuma wallahi kika sake kika amayar sai na lahira ya fiki jin daÉ—i"

Haka ta shanye maganin tana dantse bakin ta ganin bata yi aman ba.

Baki ya buɗe zai yi magana amma jin kuka daga zauren ƙofar gida ya sa ya dakata, sai kuma suka fara jin wasu muryoyi ana faɗin

"Ta ɓata jikin ta" Shigowar Aisha gidan tana kuka, kowa ya bi ta da kallo, Mama Talatu ce ta kalle ta da alhini ta ce
Chapter 1 · 0% Book details