← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 106

Sashe 56

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni fa wannan abinci ba ci zan yi ba, to da yanzu abincin ne sai an kawo mana daga gidanku kamar wasu almajirai" Ƙaran wayarsa ne ya katse masa martanin da zai mayar ganin sunan Hajiya ya ɗaga yana gaishe ta daga ɗaya ɓangaren ta ce

"Nasir Allah sa dai wannan matar taka bata ga dankali da ƙwan wannan ba ka santa da zalama kar ma ta saka tai don na ƴata Meenal ne, kuma ka ga tun da kai a nan kake karyawa tun da yanzu ka yi amarya wacce ta saba da cin cima mai kyau sai ake ɗauka muku kashinku amma iya abincin safe shi ya sa ma na tsakura muku kayan shayin wannan na san zai muku kwana uku don ƴata na san akwai tattali" ,Tun da ta fara magana yake kallon farantin da ya juye dankali da wainar sannan yana kallon ledojin kayan shayin da ya zazzage su duka, tun da dai ya san a gidan Hajiya mai kauri take haɗa musu.

Yana ƙirƙirar dariya ya ce

"Eh, mana"

Hajiya ta ce

"Ban gane eh mana ba?" Ya sake cewa hakan ya yi.

Meenal ya ji ta taso ta ɗora hannu a kan wayar ta karɓa amma bata gaishe da Hajiyar ba ta ce

",Hajiya" Jin muryar Meenal ta ce

"Na,am ƴata ya kuka tashi ya kwanan baƙunci, ai ke ki sha kuruminki babu ke babi cin tuwon safe dama hausawa sun ce mai uwa a wurin murhu ba ya cin abinci gaya" Ta faɗa tana ƴar dariya Meenal ta ce

"Hajiya ni dai ba zan lamunci a ce kullum sai ana ɗakko wani kwando da kwanuka ana biyo layi a kawo min ba kowa yana ganin ana bani abinci kamar mai neman sadaka, dankali da doyar da kuma ƙwan da komai za a kwaso a maido gidan nan, su Hibba suke zuwa da safe suna soyawa idan ana gama na tsakura muku naku na ɗauki nawa da na Nasir, shi ma kayan shayin sai nake ƙulla muku a leda suna ɗauka suna tafiya!" Ba Hajiya ba hatta Nasir maganar ta bashi mamaki ganin tana zaro magana mai kama da rashin kunya ko taunawa babu tana faɗawa mahaifiyarsa, wanda abu ne da bai taɓa ganin makamancinsa daga wajen Sadiya ba ko da kuwa an ɓatawa Sadiya rai. Hajiya kuma kasaƙe ta yi tana bin su Husna da suke gefenta da kallo su ɗin ma ita suke kallo bakinta ma ya ƙi rufuwa tsabar mamaki, tana tunanin wuta a maƙera amma tana shirin ganinta a masaƙa lokaci guda ta fara tunanin mai hakan yake nufi ko dai a mafarki take dokar da ta shimfiɗa amma yarinyar da take wa kallon babu mai hankali da ladabi da biyayya irinta amma tana faɗa mata magana gatsal har ita za ta ce ƴaƴanta suke zuwa suna yin abinci a gidanta wai ita za take ɗauka mata tana tsakura mata kayan shayi bayan ita ta tsugunna ta haifi Nasir abin mamakin ma a kwana ɗaya tak!.

GIDAN BABA

Rayuwa ta kacame a gidan Baba yanzu duk abu ya ƙi da daɗi don yanzu sai samo maganin farin jinin yake yana basu suna sha amma har yanzu babu ci gaba babu wanda ya fito ya ce zai aure su. Sai dai kowacce yanzu sai sha,anin gabanta take tana samun kuɗin biyan buƙatunta da ɗauke ɗawainiyarta da mahaifin nasu ya kasa ɗauka sai dai yanzu Arfat ta samu wani mukulli da yake iya buɗe store ɗin Baba da zarar idanunsa ya kauda za a kwaso shinkafa a dafa a wadace duk wacce take da girki ita za a ba mukullin ta ɗauko idan aka samu zaƙaƙura hatta da daddare sai a ci tuwon shinkafa. Idan ya bada hatsin tuwon sai a aunarwa maƙota a yi cefanen miya har da nama. Baba ya samu ya ci har da saka albarka don yanzu ya fara ganin amfanin nasu tun da suna ciyar masa da gida sai dai babu tuhumar inda suke samun kuɗin suke siyan shinkafar.

Da yake a store ɗin inda ya ajiye shinkafar da ban inda hatsin ma yake daban ita shinkafa a lulluɓe take ya ɗora wasu manyan duwatsu sannan tun da mukulli a wajensa yake ya san babu mai shiga hakan ya sa ba ya ma wani dubawa. A haka sai da aka cinye buhu biyu aka fasa na uku shi ma ya yi rabi. Ranar da ya ji labari a kasuwa kayan abinci sunnyi tashin gauron zabi kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha don murna yana ta lissafin yadda zai samu kuɗin don a yadda yake ma tunanin yana son ya yi sabon aure don yana saka ran ko matar za ta haifa masa jari wato namiji. Yana ta jiran wacce ruwan shanta zai ƙare a gidan ya sake ta. Bayan ya dawo ya buɗe store yana murmushi ya shiga sauke duwatsun yana yaye buhun ya yi mugun gani da sauri ya ja baya gabansa yana faɗuwa ya shiga ƙirga buhun nan ya gane babu guda biyu sannan ga ɗayan ma saura rabi, wani ihu ya yi sannn ya ji jiri ya kwashe shi bai sake sanin inda yake ba.

Lokacin da matan gidan suka ji haka aka zo ana shiga da ƴaƴan aka ganshi yashe ba ya lumfashi, kowa ya fahimci dalilin suman baba haka aka kinkime shi aka kai shi ɗakinsa, sai da aka ta sheƙa masa ruwa kafin ya fardaɗo yana faɗi

"Wayyo shinkafa ta" Ganjn bai gama wattsakewaba aka shiga bashi baki sai da warware ya tara mutanen gidan duka, yana gargaɗin wanda yake shiga masa store amma kowa ya ce ba shi ba ne. Jin hakan sai a sallami kowa amma dai kowa gabansa yana faɗuwa ana tunanin hukuncin da zai yanke. Aisha ce ta yi laɓe yana waya da abokinsa ta ji yana faɗin yana zargjn ko dai shinkafarsa ce ake ci a gidan idan har ya yi bincike ya gane hakan tabbas rai zai yi mummunan ɓaci, sannan zai fasa fita kasuwa na kwana uku don ganin wanda yakr masa aika-aika idan matarsa ce daga ranar zai yanke igiyar aurenta, idan a ƴaƴa ne zai tsinewa ko wace ce kuma ya kore ta daga gidansa.
Kowa ya tsorata da lamarin basu san abin zai yi tsamari ba hakan ya saka duk mai girki sai ta san yadda za ta yi ta bayar a auno shinkafa ta dafa da miyar dik ta yi cefane. Baba ya auna sauran shinkafar da ta rage a buhu ya san yawanta amma kuma gashi ana dafa abincin a gidan sai dai ahinkafar buhun idan ya sake aunawa sai ya ga tana nan yadsa take, hakan ya sa abin ya ɗaure masa kai ya kasa gane inda matsalar take, a wani ɓangaren na zuciyarsa ya fara tunanin ko dai aljannunne suka masa satar.
Kwana uku yana gadin store amma babu wanda ya gani ya shiga sannan abin da ake ci a gidan ba a a daina ba, hakan ya sa ya gane matsalar ba daga iyalansa ba ne!.
Lokacin da ya tafi masallaci sai Hafsat ta ce yau za ta tashi da dare domin ta kawar wa da Baba zargi ko ya haƙura ya fara zuwa kasuwa sannan ya daina zargin kowa za ta zo a matsayin ɓarawon shinkafa da dare sai dai tana fatan Allah ya sanya saɓanin tsakaninsu kar ya karya mata ƙafa kasancewar da wani ƙaton icce yake kwana!.
Dare ya tsala kowa yana ɗaki ya yi bakam amma ba barci ake yi ba, don kowa yana fargabar zuwan Hafsat a matsayin ɓarawo sai dai ana tsoron ya za ta kasance don kowa yana tsoron hukuncin da za a yanke musaman da abin ya shafi kowa. Riga da wando ta ɗauka a ɗakin Baba wanda ya ware zai bayar wasu tsoffin kayansa ne da suka ga jiya da yau har ma da shekaran jiya domin sun tsufa har sun gaji. Misalin ƙarfe biyu ne na dare ta tashi ta saka kayan bayan ta karɓi mukullin store ɗin da suke amfani da shi a wajen Arfat.

Lallaɓawa ta yi ta buɗe store ɗin a hankali ta tura ƙofar a hankali hakan ya yi daidai da falkawar Baba da bacci ɓarawo ya sure shi, zaune ya tashi a ransa yana raya rana dubu ta ɓarawo ɗaya tak ta mai kaya. Ƙoton icce da yake rinjayarsa ya ɗauka yana ayyana cewa yau sai dai uwar ɓarawon nan ta haifi wani amma idonsa -idonsa sai ya rotsa masa iccen a kansa.

ALIYA
Tun da Baba ya kira ta zaure inda suke zaune da sirikinta gabanta yake faɗuwa a ranta tana fatan Allah sa zaman nan da za a yi ya yi silar warwarwwar aurenta tun da dai har suka rufe ta aka aura mata mata maza a matsayin miji. Tun da ta zo ta gaishe da sirikin nata ya amsa sai kuma suka shiga tattuna maganar sai dai tana jin yadda mahaifin Naair yake ta ƙoƙarin kare ɗansa ranta sai ya fara ƙuna jin nata mahaifin yana gamsuwa da bayanin Abba ya ce
"Kenan dama an daÉ—e da magance matsalar?" Baban Kasim ya ce

"Ai tun da aka haife shi a haka muka garzaya asibiti nan likitoci suka yi bincike suka gano cewa ya fi ƙarfi a ɓangaren namiji hakan ya sa da na ji kuɗin aikin a lokacin bani da kuɗin da za a masa aiki, har ya fara tasowa zuwa shekara bakwai a lokacin ne abokansa yara uke tsokanarsa kullum ya fita waje sai ya dawo da kuka suna tsokanarsa da mata maza har a makaranta ma wannan dalilin ya sa muka ƙauro muka dawo gidan da muke a yanzu to a nan babu wanda ya san larurar da yake ɗauke da ita har Allah ya hore mini na samu aka masa aikin gabaɗaya ma wajen matantakar sai tabon aikin da aka yi a wajen, ni kuma abin da ya sa ban faɗa ba tunanina ya faɗa mata shi Kasim ɗin kuma dai da na ga yanzu a ɓangare ɗaya yake sannan likitoci sun faɗa mana idan aka yi wa mata maza aiki yana rayuwa kamar kowa sannan ba a gadon haihuwar mata maza kuma su ma za su haihu kamar kowa"

Abba ya ce
Chapter 56 · 0% Book details