← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 106

Sashe 82

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai na É—auka ma ko bakya iya shan ruwan gidan namu ba" Ta faÉ—a a zuciyarta kuma tana cewa

'Kin kusa zama tarihi a wajen Ibrahim ɗin da kike taƙama da shi'

Jidda tana Æ´ar dariya ta ce

"Haba Umma ta yaya haka zai faru ni da gidanmu ni da na taso na girma ina shan ruwan"

Umma ta.ce

"Ai da na ga yanzu kin saba da ruwan faro wato ruwan roba" Sosai Jidda take dariya Umma kuma a fili fuskarta ɗauke da murmushi amma a zuciyarta tana fatan Allah ya kawo ranar da wannan murmushi da farincikin zai bar kan fuskar Jidda ta dawwama cikin ƙunci.

Suna ta taɓa hira tana cewa ta zuba mata tuwo ta ce a ƙoshe take, a nan har tana bata labarin yadda take jin daɗi idan Aliya ta kai mata ziyara a fili Umma ta ce

"Ke da Æ´ar uwarki haba Jidda in Aliya bata je wajenki ba waye zai je"

A zuciyarta kuma ta ce

"Ita ma tata ce take kaita, za ki gane baki da wayo ne lokaci yana zuwa sannan za ki yi hankali ki gane ba kowa ake ba yarda ba a rayuwa, domin kamar yadda bahaushe ya ce

'Makashinka yana tare da kai!'

Sunanta taɓa hira har Abba ya dawo, ya yi farincikin ganin Jidda musamman da ya ganta cikin farinciki da kwanciyar hankali, tabbas yana son Jidda yana jinta a zuciyarsa tamkar ƴar da ya haifa wani lokacin har tana jin son Jidda yana barazana ga son da yake wa Aliya wato son Jidda yana neman linka shi.

Ta gaishe da Abba cike da girmamwa tana jin ya maye mata gurbin mahaifinta har abada, bata da wani uban da ya wuce shi tana bashi matsayi irin matsayin da baki ba zai iya fasaltawa ba. Umma tana jin haushin yadda yake nunawa Jidda kulawa amma haka ta danne. Tana tsokanarsu wai ƴa da uba an daɗe ba a haɗu ba. Bayan an ɗan jima ta buɗe jakarta ta ɗakki mukullin motar ta miƙa masa tana faɗa masa Ibrahim ne ya saya masa mota buɗar bakin Abba ya ce

"Mota kuma Jidda?" Umma ranta a matuƙar ɓace amma haka ta daure ta nuna murna. Jidda tana dariya ta ce

"Mota Abba ita ce dai za ka ganta a waje sabuwa dadal" Ta faÉ—a tana dariya.

Idanun Abba suka kawo ruwa yana jin cewa shi ya sa aka ce ba a yi wa É—a da dukiya mugunta domin baka san mai amfanarka ba.

Ya yi farinciki har ya rasa da wane baki zai ambata murnarsa sai albarka yake sakawa Jidda da Ibrahim yana ta musu fatan alkairi a rayuwar aurensu, tare da nemar musu tsari daga dukkanin sharri. Jidda sai amin take cewa inda Umma duk ta ji kamar ta fasa ihu saboda takaici da baƙinciki musamman yadda yake ta zabgo addu,ar nema musu tsari da kuma ta dawwamar da farinciki sai take ganin kamar addu,ar da yake yana adawa ne da cikar nasu burin.

Farincikinsa ya kasa ɓoyuwa har sai da Ibrahim yan dawo ɗaukan Jidda ya kira ta a waya inda ta sanar da su zai shigo haka ya shigo Abba ya yi ta masa godiya da kuma addu,a Umma ma haka ta daure tana masa godiyar amma ko da wasa bata yi addu,a ba.

Sun musu sallama inda suka tafi.

Washe gari da yamma Jidda ta fito wanka tana zaune gana mudubi tana shiryawa shi kuma dama ta bar shi a sama yana ƙarasa wani aiki, ƙaran wayarta ne ya dakatar da ita daga shafa powder da take ta ajiye sosan shafa powder ta ɗakko wayarta ganin sunan Umma ta ɗauki wayar da murmushi bayan sun gaisa Umma ta shiga tambayar lafiyarta da ta mai gidan har tana faɗa mata da safe sun je gidan su Ibrahim ɗin ita da Abba sun duba Daddyn nashi.

Bayan Jidda ta musu godiya sai kuma Umma ta yi shiru har sai da Jiddan take tambayat shirun da ta yi, Umma ta ce

"Wallahi dama wata damuwa ce nake da ita Jidda ina fata za ki share mini hawaye"

Jidda ta ce

"Subhanallahi damuwa kuma Umma?" Umma jin duk Jidda ta rikice tana nuna damuwa sai Umma ta cr

"Wallhi kuwa wani ɗan uwana ne a ƙauye jeji suka shige shi ƙafa tana nan suntum sai wari take to an kai shi wajen me magani sai aka yanka kuɗaɗe masu yawa, har dubu ɗari biyu da hamsin to yanxu sun haɗa dubu hamsin dubu ɗari biyu suke nema na ce bari na gwada sa,a ta a wajen ɗiyata mai tausayi ko za a dace!" Ta faɗa tana aikawa Jidda harara ta cikin wayar. Ajiyar zuciya Jidda ta sauke ta shiga faɗa mata cewa bata da kuɗi don jiya ta yi sayayyar wasu kaya a online za kawo mata sai dai za a iya samun dubu saba,in.

Umma ta ringa faÉ—a tana cewa

"Yanzu Jidda har sai an koya miki dabarar zaman aure a gidan mijin, tun da har kika samu kika auri mai aljihu da maiƙo ai kamata ya yi kike farauto mana karki yarda ki zauna kanki da murfi don yanzu kowa ya waye" Jidda cike da rashin fahimta ta ce

"Wallahi Umma ba na iya tambayar Ibrahim kuɗi ina nufin ba na iya roƙonsa, sai dai a ɗan jinkirta idan har da kansa ya bani kuɗi sai na cika miki" Umma ta hau faɗin

"Kidahuma kike so ki zama?" Wannan ya yi daidai da zuwan Ibrahim bakin ƙofar ɗakin Jidda jin tana cewa

"Umma in saci kuɗin Ibrahim kuma? Gaskiya ni ba zan iya yin sata ba ko kuɗin waye in dai ba nawa ba ne bare na Ibrahim" A daidai nan ya tura ƙofar gabaɗaya ta rikice ta saki wayar ma daga hannunta ta faɗi ƙasa sa,ar ta ɗaya wayar bata yi komai ba.

Sai ya nuna mata bai ji abin da take faɗa ba, dama kuma ya san ba za a taɓa haɗa baki da Jidda a cuce shi ba ya yarda da ita 100%
Wayar ta É—auka ta kashe da sauri jin yana cewa har yanzu bata gama shiryawa ba, duk ta rikice yanayin da ya ga ta nuna har ya so bashi dariya amma ya danne.

Umma wani ƙuduri ta ƙudurta a ranta cewa za ta yi maganin Jidda don sai ta mata abin da wani maƙiyinta ma idan ya ganta sai ya tausaya mata.

Wani filinta ta je ta ɗaga ta sayar Abba ma bai sani ba suka haɗa kuɗin suka nufi wajen bokanya. Bayan sun damƙa mata kuɗin ta tashi tsaye tana riƙe da wani ƙaramin kasko take kewaya ɗaki a take hayaƙi ya fara fitoa daga kpwace sukurwa ta ɗakin. Lokaci gida hayaƙi ya baibaye ɗakin su duka a tsorace suke sai da ta gama ta koma mazauninta ta zauna ta dube su ta ce

"Yanzu mai kuke so a yi"

Umma ta yi karaf ta ce

"So muke a saka masa son Aliya yadda ba zai taɓa rabuwa da ita ba yadda zai tsani duk wanda ya kushe ta ko ya nuna sai ya rabu da ita, sannan a saka soyayyarta a zuciyar surukan nata wato iyayan Ibrahim ɗin, shi kuma mahaifinta wato mijina a saka masa son auren nata kuma kar ya taɓa tambayar dalili ita kuma Jidda a sanya ta zama akwai ya babu kakar wajen uba"

Aliya ta ce

"Kawai gwara ya danƙara mata saki lokaci guda idan dai ya yanke igiyar auren dolenta ta tafi ai"

Bokanya ta gyaÉ—a kai tana wani haÉ—e halen magani sai kuma ta shiga kiran sunayen wasu aljannu kafin ta buÉ—e hannu su Umma sai ganin wani magani suka yi kulle a farar leda an É—orowa Bokanyar a tsakiyar hannun.

Nan ta miƙawa Umma magnin ta ce

"Wannan garin maganin za a saka shi a hancin sabuwar gawa ta namiji, bayan an masa wanka an saka likkafani kafin a rufe kan za a cire audugar hancin sai a zuba maganin a duka ƙofofin hancin sai kuma a mayar da audugar a rufe, yadda gawar nan bata da wani sauran amfani haka Jidda ba za ta sake amfani a wajen mijinta ba kuma a take zai sake ta, sanann son Aliya zai shiga zuciyarda daram, sai kuma mahaifinta da ko ma waye ba za su taɓa kawo tsaiko a kan auren ba, babu ma mai tambayar don mai aka yi " Umma tana dafe da ƙirji da hannu biyu sai karkarwa take jin furucin bokanya, tana tuna naira dubu ɗari biyu da suka bayar yanzu kuma ga wani ɗanyen aikin da take ji har gwara na cokalin da Aliya ta yi.

Aliya tana zare ido ta ce

"Bokanya ko za ki sauya aiki?" Umma ta shiga gyaÉ—a kai alamar gamsuwa da maganr Aliya ita kuma Bokanya ta ce

"Ai in mun faɗa sai an yi kuma ba za a canja ba, mene ne abin wahala a wannan aikin ku da kuke neman biyan buƙuta ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, da kuka ci sa,a ma ban ce ku yi ridda ba"

Suna haÉ—a ido suka juya suna kallonta suka haÉ—a baki wajen faÉ—in

"Ridda?" Bokanya ta ce

"Ridda mana mutane nawa ne suka yi ridda saboda su samu biyan buƙata, mutane nawa za su zo mu basu hutun yin sallah na kwana arba,in ko satittika ko watanni kuma su yi"

Umma ce cikin sanyin murya ta ce

"To ai bokanya ta yaya za a yi mutum ya iya zuwa wajen gawa har ya yi abin da kika faÉ—a ba tare da tonuwar asirinsa ba?" Da wata mahaukaciyar dariya ta bushe ta jima tana yi sannan ta haÉ—iye dariyar ta hanyar haÉ—e rai sai kuma ta ce

"Komai a tsare yake, don haka akwai maganin da zan bayar da kowa sai ya suma a take a wajen " Umma suna gyaɗa kai ita da Aliya kamar ƙadangaru Bokanya ta miƙa
Chapter 82 · 0% Book details