← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 106

Sashe 78

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da suka zo asibitin sun je É—akin da aka kwantar da Daddy yana kwance lifet kamar gawa sai likita da yake sanya masa ruwa a hannu Mummy tana zaune a gaban gadon ta kifa uban tagumi idanunta jajawur. Haka su ma suka tsaya suna ganin ikon Allah. Bayan likitan ya gama abin da zai yi sai ya ce da Ibrahim su je office suka fita aka bar É—akin daga Mummy sai Jidda da take ta faman ba Mummy baki.
Mummy ta ce
"Jidda lafiyarsa ƙalau fa, babu abin da yake damunsa, muna hira kawai miƙewar da zai yi ya yanke jiki ya faɗi sumamme" ,Jidda ta ce
"Subhanallah ki yj haƙuri Mummy in sha Allahu zai samu lafiya" ,Mummy tana share hawayen da ya gangaro mata ta ce
"Allah ya sa amma na tsorata da lamarin nan, gaskiya rayuwa abin tsoro ce "
A haka Ibrahim ya shigo direban gidan Mummy yana biye da shi riƙe da ledar magunguna sai kuma katan ɗin ruwan roba.
Har lokacin Daddyn bai farka ba don dai yanzu numfashin sa ya dawo kawai dai bacci yake, Ibrahim ya ce zai je masallaci ya yi sallah direban ma dama yana ajiye ledojin ya fita Jidda ma sallar ta yi ita dama Mummy tana hutun sallah ne
Wajen ƙarfe tara da rabi Mummy ta ce au tafi gida saboda Jidda sai Ibrahim ya ce zai kaita gidan ya dawo ita ma Jidda ta ce a asibitin za ta kwana amma Mummy ta ce a kaita gida..

Suna tafiya tana ta kwantar masa da hankali ga tausayinsa ya kamata, ko abinci bai ci ba ga rashin lafiyar Daddy mai gadi yana buɗe musu get ya shiga da motar mai gadi yana rufe get inda mai ba flowers ruwa ya taho da sauri ya zo yana ƙoƙarin buɗe masa motar cikin girmamawa amma sai ya dakatar da shi yana faɗin ba fitowa zai yi ba. Jidda ce ta juya ta kamo hannunsa ta sanya cikin nata ta matsa yatsunsa tare sa rausayar da kai ta ce

"Annurin zuciyata idan fuskarka ta zama babu walwala sai na ji komai ya sare mini, sannan sai na ga gabaɗaya duniyar ta mini ƙunci tare da yi mini wani irin duhu" Iska ya fesar daga bakinsa ya riƙe sitiyarin motar da hannu ɗaya duk da ba tuƙi yake ba, ya saka ɗaya hannun da take murzawa ya riƙe nata gamgam ya ce

"Ki bari har na dawo daidai Jidda yanzu damuwar Mummy da halin da Daddy yake ciki ya rufe komai amma ki sani zuciyata a buÉ—e take tana sane da ke sannan da ke take rayuwa"

Kallonsa take yadda fuskarsa ta yi fayau ta ce

",Plss mu shiga ciki na haɗa maka shayi mai ɗan kauri ka sha" Kai ya shiga kaɗawa alamar ba zai sha ba, amma ganin ta shagwaɓe fuska sai ya ji yana so ya faranta mata hakan ya sa ya yi na,am sai suka fito a tare tana riƙe da hannunsa suka shige cikinm gidan, a falon ƙasa ta masa masauki a kujera ta nufi kicin ko hijabin bata cire ba, shayi ta haɗo masa ta ɗoro a ƙaramin kofin tamgaran da ɗan ƙaramin plate ɗin kofin ta zo tana juyawa da tea spoon.

Ko miƙa masa bata yi ba ta shiga bashi a baki har sai da ta ga ya shanye tasss sannan ta ajiye a ƙasan kafet tsaye ya miƙe yana mata sallama ya juya zai fita yana dab da fita daga ƙofar falon ya juyo sai kuwa ta ƙarasa da sauri ya buɗe mata hannunsa ta shige ya rungumeta sannan ya yi kissing goshinta ya ce

"Ni zan tafi sai Allah ya kaimu gobe" Amsa masa ta yi ya É—aga mata hannu alamar bye-bye ita ma ta É—aga masa ya fita.
Tsakiyar falon ta koma ta aunkuya za ta ɗauke kofin shayin sai ga Saude ta zo ta karɓa ta je kicin ta wanke ta ajiye, ta fito sai ta ga Jidda zaune hakan ya sa ta mata ya mai jiki bayan ta faɗa mata da sauƙi sannan ta masa fatan samun sauƙi.

Sama ta haura jim kaɗan ta fito da kayan tuwon nan bayan ta ɗauke cokali da tuwon da Ibrahim ya gutsiro zai ci lokacin da Mummy ta kirashi wanda kiran ya yi sanadiyyar rasa nutsuwar zuciyarsa sanadin rashin lafiyar mahaifinsa. Tana sakkowa ta yi kiciɓis da Saude hakan ya sa ta ba Saude kayan tuwon ta ce ta kai kicin, karɓa Saude ta yi Jidda tana komawa sama Saude ta shiga kicin har da rufe ƙofa ta tsaya ta ƙarewa tuwon kallo tana ganin gurbin da akamcire a jikin tuwon wanda da alama cokali ɗaya ne kuma ga gutsuren lomar nan a gefen plate ɗin, wata ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala don ta san akwai abin da Aliya ta yi a saman, wanda tana zaton hakan zai kasance wani abu ne ta barbaɗa a miyar tuwon sannan zarginta da take ta rayawa a ranta cewar cokali duk da ba za ta iya hasashen ainihin abin da ya yj silar ganin cokali a bra ɗin Aliya ba amma kawai ta gwammace ta salwanatar da cokalin haka ta juye tuwon duka da miyar a baƙar leda ta wanke kwanukan ta gyara kicin ɗin. Ta fita da wata doguwar wuƙa a hannunta da kuma ledar da ta sauye tuwo da miyar sai wannan cokalin. Sai da ta je garden ɗin gidan can tsakanin wata bishiya ta haƙa babban rami ta jefa ledar da cokalin ta yi addu,a ta mayar da ƙasar ta rufe wajen sai da ya yi kamar ba a taɓa tona wajen ba, sannan ta bar wajen tana jin wani shauƙi.

Ko da ta yi shirin kwanciya ta saka kayan bacci pink colour masu laushi sosai ta shafa turare, ta hau gadon ta kwanta sai ta ji gabaÉ—aya É—akin da gadon sun yi mata girma kasancewar babu tauraron zucuyarta Ibrahim.

Filonsa da yake kwanciya ta janyo kusa da ita tana shaƙar ƙamshin turarensa tana jin tamkar tana kusa da ita tun da basu taɓa nesa da juna ba tun da suka yi aure.
Daga ƙarshe ta ɗakko ƙafafunta ta sakko ƙasa ɗakinta ta nufa ta je ta kwanta a ganinta za ta samu sauƙi salama da sasaauci na tunanin Ibrahim da take ji tamkar shekara suka yi ba sa tare da shi.

Aliya tun da ta gama waya da Amatullahi sai ta kira Umma tana sanar da ita cewa aiki ya kammala, Umma ta ringa rawa da juyi a ɗakinta tana jin daɗin yau sun hau turbar zama masu arziƙi. Ko da Kasim ya dawo shi kansa ya yi mamakin ganin yadda fuskarta take a washe bata sai wani nan nan take da shi, bai san cewa tana yin hakan ne don ta hango tsantsar wata dama da za ta samu a rayuwa. Indomie ta dafa masa yau don badangarci da hannunta take bashi a baki ba ma da fork ba. Gabaɗaya daɗi ya cika Kasim ya kalle ta yana murmushi ya ce

"Haƙiƙa ni a cikin maza ɗan gata ne a wajen matata, matata tana sona!" Ya faɗa yana buɗe baki ta bashi indomie ɗin. A fili ta ce
,
"Idan miji bai zama É—an gata a wajen matarsa ba a ina zai zama" Ta faÉ—a tana kallonsa.

A zuciyarta kuma ta ce

'Wanda dai nake so da muradi yana can sai dai very soon zai dawo gare ni tabbas zan murza kan naira har sai ta tabbatar ta zo hannun da za a bata wahala" Suna ta hira har suka kammala don ita ko a bakinta ta ce a ƙoshe take wani irin farinciki take ji irin farincikin nan mai hana ka cin komai duk da dama bata tare da yunwa.
Ko da suka zo kwanciya ma bayan ta sha maganinta a ɓoye na hana ɗaukan ciki tana rayawa a ranta cewa ta kusa daina shan magani da zarar ta auri Ibrahim za ta yi ban kwana da shan magani domin ta je inda za ta saki jiki ta haihu ta zubar da ƴaƴa yadda za su ci gado son ransu, tamkar dai sun ƙauro duniya.

Ranar Kasim ya san ya yi aure domin kuwa zagewa ta yi ta nuna masa kulawa ta musamman a wajen mu,amala, sai ta sa yake jinsa na miji sak babu sirki kamar yadda ake kiransa mata maza. Duk bai san tsabar farincikin da take ciki ba ne.

Washe gari da safe har ta matau ya fita ya bar mata gidan saboda tana son dara shirin barin gidan saboda ta san abubuwan da bokanya ta faÉ—a mata na cewa Kasim zai sake ta sannan za a rufe bakin Abba da duk wani É—an tsurku da zai kawo tsaiko a lamarin. Yau Kasim shiga ya yi ta musamman son yau jinsa yake tamkar aabon angon da aka É—aurawa aure a ranar, ko da ya zo mata sallama ma ya daÉ—e tana ta furzo mata kalaman soyayya tana amsa masa a fili amma a zucuyarta wani haushi ma yake bata.

Yana fita ta doka wani uban tsaki ta koma ɗaki ta zauna tana duba waya don ganin lokaci so take ta kira ta tabbatar amma kuma ganin ƙarfe goma sai ta ba zuciyarta haƙuri a ɗan jima domin kar a zargi wani abu. Ahawara ta yanke ta kira Amatullahi ta ce
Chapter 78 · 0% Book details