Sashe 62
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Momi ni dai zan yi iya iyawata don ganin ba a tozarta ni ba duk da na san wani lokacin duk ƙoƙarin mutum na gujewa natsala sai ta afka masa sannan matsaloln gidan aure ba kidahumanci ne yake kawo su ba ko rashin wayo, sai dai ya danganta da wanda ka dace da shi a matsayin abokin rayuwa ko kuma suruka da dangin miji, duk da akwai matan da suke bayar da kansu suka sakin jiki a musu kowane cin kashi duk da cewa mace ƴar biyayya ce amma ba ce ta bada fuskar da za ta zama baiwa ko kuma abar wulaƙantawa ba" Tun da ya fara bayani Momi take jinjina mata daga na ta hau faɗin
"Kar ki kuskura ki ragawa Hajiya na faÉ—a miki daga ita har É—anta ki koya musu karatun ta nutsu don na ga da sauransu a karatub duniya sun É—auka don kina Æ´ata za su ci kashi a kanki ko su juye kowace bola a kanki to ba haka take ba"
Meenal ta hau ba mahaifiyarta labarin yadda abubuwa suka wakana tsakaninta da Hajiya da Nasir har ma da zuwan Hajiyar gidan ta kawo mata magani wai bata cikin hayyacinta sai dai bata faÉ—awa Momi wayar da ta yi a gaban Hajiyar ba.
"Magani Meenal hauka ake za ki karɓi magani a wajen wani barw ki yi amfani da shi, karki manta ni da Hajiya tif da taya muke hakan ba zai hana ta tarwatsa ko farraƙa tsakaninki da ɗanta ba don son zuciya irin nata kin sani bata ƙaunar a ɗanɗani arziƙin ɗanta ta fi son koyaushe daga ita sai ƴaƴanta don haka tana iya karɓo maganin da za ta rage miki matsayi a wajensa don kar yake kyautata miki, ko kuma ta yi maganin da za ki koma kina mata biyayya kamar vaiwa ta taka ki yadda ta so kamar yadda suka mayar da wannan uwar gidan marar ƴanci da galihu a wannan gidan"
Meenal ta ce
"Momi dama ina sane ba zan yarda ma na yi amfani da shi ba, sai faman faɗi take wai bana hayyacina ta fi so in ci gaba da ƴasƙantar da kai irin yadda nake nuna mata kafin ya aureni bata san kawai shigo shigo ba zurfi ba ne"
Momi ta ce
"Ai na san kin haifu a cikina gwara ki nuna mata shayi ruwa ne, sannan ki nuna mata tsakanin zuma da maɗaci akwai bambanci, kuma dole ne ki bambanta mata tsakanin aya da tsakuwa banda zubar da girma mai za ta je yi gidan yara a ranar farko ga ƙawayenki nan bata tunanin za a rainata duk son abin ɗanta ya rufe mata idanu""
Meenal ta ce
"Ai da ni take zancen sai na gasa mata aya a hannu in shayar da su ruwan mamaki in bata kauda idonta ba sai na bayar da darasi a kanta yadda uwayen miji za suke barin matan ƴaƴansu su sake da mijinsu, ni ba zan lamunci cin mutunci ba ni babu wanda zan ragawa ko ita matar tasa sai ta san da zamana" Suna cikin haka Meenal daga wutsiyar ido ta hango Hajiya ta leƙo kanta cikin ɗakin, da sauri ta yi sallama ta kashe wayar ta nufi wajen tana faɗin
"Hajiya dama baki tafi ba?" Wata ajiye zuciya da har sai da Meenal ta ji ita Hajiya ta yi a fili kafin ta ƙaraso tana faɗin
"Ƴata Meenal baki karɓi magani ba ina na samu damar tafiya, kuma bakya tunanin ƙawayen can naki su yi aika-aika a store da kika basu mukullin?" Hajiya ya faɗa don jikinta sai yake bata kamar za su yi sata a store ɗin ko su yi almubazzaranci don ta ga ita Meenal ɗin bata ma damu ba da mukullin da ta basu.
ÆŠan yatsina fuska ta yj ta ce
"Hajiya bari na miki gwari gwari yadda za ji fahimta, wallahi summa tallahi rass nake babu wani fitar hayyaci idan kuma akwai wani abu da kike so in tabbatar miki ki yarda za ki iya faɗar abin da kike so na faɗa miki, sannan kuma mukullin store ɗin ne sai an bi mutum don an bashi aika-aika a kan abinci sai kamce wasu ɓarayi to ni ko ɓarawo in ya saci abinci gani nake ba sata ba ce tun da idan ya ci ma maganin yunwa ya yi kuma za ka samu ladan sannan ai abinci kashinsa za a yi ba kadara ba ne da za ake alkintawa"
Tsabar mamaki Hajiya kallon Meenal kawai take dakyar ta yi yaƙi da bakinta ya iya furta
"Abincin ne ba kadara ba Meenal baki san mace ana so ta zama mai adana dukiya da komai na miji ba yanzu idan abincin ya salwanta a taron nan na amarcinki sai fa Nasir ya sake fafutukar kawo wani ai a tausayawa miji, sannan da kike batun É—aukan abinci ba sata bane ai duk abin da mutum zai É—auka in har ba nashi bane kuma ba a bashi ba sunansa sata k...
Meenal hannu ta É—agawa Hajiya wanda ya sa ta dakata da maganar cike da mamakin hannun da ta É—aga mata tamkar wata sa,arta sai kawai ta ji ta ce
"Hajiya ya kamata kisan inda dare ya miji karki manta nan gidan mijina ne ina da damar yin komai, sannan ba huruminki bane da zaki baro naki gidan sabodan zubar da girma ki zo kina bin diddigin abin da yake faruwa a gidan ɗanki sannan shi Nasir ɗin ai tun da kika ga ya yi aure ya shirya tarɓar kowace buƙata dole ta nemo idan babu kuma wallahi summa tallahi babu mai mini shamaki da abinci ko wani abu a gidan mijina, yadda kike taƙama ɗanki ne haka nake taƙamar mijina ne na ma fiki iko da shi yanzu" Furucin Meenal na yanzu ya sa Hajiya ta yi tsai tana lura da yanayin maganar ta a nan ta fahimci cewa tabbas a hayyacinta take babuwwasu alamu na fitar hayyaci a tare da ita kawai tsabar rashin kunya ne da fitsara hakan ya nuna ba ma sai ta ɓata loakci wajen cewa Meenal ta yi wani abu da zai nuna tana hayyacin ta hakan ya sa a zafafe Hajiya ta ce
'Wallahi ƙarya kike Meenal! Babu wanda zai yi iko da Nasir sama da ni"
Meenal ta kalle ta ido cikin ido ta ce
"Kina musu da hakan?" Bata jira amsar Hajiya ba ta ce
"Idan kin musa ki zo ɗakin nan da daddare akwai wata shegiyar rigar bacci da nake da ita da kuma shu,umar humra mai tada kan maza zan saka rigar in shafa humrar zan faɗa wa Nasir ya zauna a wuri ke kuma ki ce ya tashi in zai bi umarninki mu gani!." Wani salati da Hajiya ta kwasa sai da ya so ba Meenal dariya son ta lura Hajiya ta shaƙi takaici kuma abin ya ɗaure mata kai Meenal ta murmusa ta ce
"Ki saka takalmanki ki koma gidanki sannan ki ɗauke idanu a kan lamuran gidan nan idan kina son kanki da girma da arziƙi in ba haka ba wallahi takaici sai ya kusa kasheki" Tana gama faɗar hakan ta fito falo ta bar Hajiya tsaye kamar ta saki ihu tana fitowa falon ƙawayenta suka hau mata kirarin amarya har da masu mata waƙar amarya da Ali Jita ya yi wa amarya. Suna ta abin su Hajiya tana bedroom tsaye da jaka maƙale a hamata ƙullin magani guda biyu a hannu, waiwayawa ta yi ta kalli ɗakin ta ƙare masa kallo sai ta hangi gajeran wandon Nasir da rataye saman ƙofar banɗakin juyowa ta yi ta fito falon ko kallon tarkacen ƙawayen Meenal na falon bata yi ba ta yi waje don zuwa lokacin ma Meenal ɗin ta yi tsakar gidan.
Sadiya tana alwalar azahar a famfo Meenal tana tsaye wajen ƙawayenta da suka ɗakko kayan abincin a store suna nuna mata, suna cewa abincin da yawa tana faɗa musu dama fa ba wai za a kai gidansu ba ne yau kawai ta faɗa ne don ta cusawa Hajiyar haushi. Fitowar Hajiya daga falon Meenal za ta saka takalmi ya yi daidai da shigowar Nasir da ya kinkimo silindar gas yana tafiya a ɗan duƙushe alamar mutum ya ɗaga abu mai nauyi bayansa wasu matasa ne guda uku suna ɗauke da katan ɗin lemo coca cola biyu mirinda ɗaya sai fanta biyu.
Hajiya tsabar yadda ta ruɗe da ganin lemukan da ya siyo ga gas tana tunanin kenan dai maganar Meenal ta zama zanen dutse sai da ya aikata, a ƙwaƙalwarta tana ƙiyasin kimanin nawa aka kashe a hakan ta saka takalminta ɗaya nata ɗaya kuma na wata daga cikin ƙawayen amarya sannan kowanne ba ƙafarsa ba ce.
Kiran sunan Nasir take Sadiya da ta gama alwala dariya tana neman ƙwace mata da ta ga ƙafar Hajiya ta yi saka takalmi kamar ƙafar ƙananan yara sannan takalman daban-daban ne uwa uba yadda ta tikce tana kiran Nasir.
Nasir faÉ—i yake
"Ina zuwa Hajiya" Ya yi hanyar kicin ya daidaita musu silindar a jikin gas É—in, tsakar gidan kuma samarin nan suna tambayar inda za su ajiye lemukan Meenal ta yi karaf ta ce
"Ku kai ƙofar wancan ɗakin" Ta faɗa tana musu nuni da ɓangarenta sannan ta hau ƙwalawa wasu daga cikin ƙawayenta ta ce su karɓa su saka a frige har tana musu tsiya wai sun zauna a ɗaki ba za su fito su yi aikin abincin ba. Suna faɗin sai sun ci wani abu hakan ne ya ankarar da saƙon su da Nasir ya bari a mota.
Yana zuwa gaban Hajiya ya sassauta murya ya ce
"Hajiya kin ga ƙafarki kuwa?" Hajiya wacce duk takaici ya ishe ta ta san Nasir da izza da nuna isa a kan Sadiya amma yau ta ga ya zama kamar wani sauna sai abin da aka ce masa. Sadiyar da ko kuɗin magani ba a bata idan bata da lafiya haka ma idan Kalifan bashi da lafiya suna idon a bata kuɗi duk ƙanƙantarsa sai gashi wata ta zo rana tsaka za ta kawo wargi a lamarin aljihun Nasir ɗin duba da yadda ya siyo komai da aka faɗa babu musu.