← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 106

Sashe 93

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Meenal wa yake ta kumbuarar hannu, ki tashi mu kama hanya kar ya dawo ya iske mu a wajen nan, don wallahi wannan ya samu mace sai ya kumbura mata matantaka in ma bai ɓarɓarka ta ba" Babu yadda suka iya haka suka tashi cikin lallaɓawa suka kama hanyar da suka baro tun da ba zai yiwu su ci gaba da tafiya ba, gudun kar su yi arangama da shi!.

Gudu suka babu ƙaƙƙautawa har sai da suka ga sun zo bakin hanya" Sai haki suke suna da na sanin hawa amalanken Audu kwarto. Motoci suna wulgawa sai dai duk wacce suka tsayar sai su ƙo tsayawa don ana musu kallon kamar basu da cikakken hankali duba da kowacce babu takalmi sannan kuma kowacce ba ta da nutsuwa.

Dakyar suka samu wani mai mota ya ɗauke su da suka faɗa masa ziyara suka je ƙauyen ƴan uwansu a hanya ɓarayi suka tare su suka musu ƙwace tare da musu dukan tsiya, ya taimaka musu donnhat ƙofar gidan Momi ya kawo su, saboda ba motar haya ba c kuma shi kaɗai ne a motar. Godiya kamar za su ari baki. Sai da suka dawo gidan ƙofar gidan ma sai ɓalle ta aka yi don mukullin ma ba a san inda ya faɗi ba.

Bayan sun shiga gidan suka zauna suna mayar da yadda aka yi, a nan Momi tana nunawa Meenal kuskurenta na yin maganar kuÉ—i a gaban wasu tun da ta lura maganar kuÉ—in ce ta ankarar da su akwai kuÉ—in a atare da su, shi ya sa ake so mutum ya kama bakinsa idan ya je wajen da bai san mutane ba, tun da ba a goshin mutum za a rubuta waye shi ba, idan mugu ne ko akasin hakan.

Ruwan zafi Momi ta dafa suka yi wanka sannan suka ci abinci suna maganar za su koma wajen bokan don cim ma manufarsu domin ba su daddara da abin da ya faru ba, hakan ya san Meenal ta ce akwai wasu kuÉ—aÉ—e da za su shigo mata da zarat sun shigo za su koma, Momi ma da yakr zuciyar a bushe take ta goya mata baya.

Sai da Nasir ya dawo daga kasuwa ta biya suka ya ɗakko ta. Tana shigowa gidan ganin Sadiya tana shanya kafa ta aika mata saƙon mugun kallo, abin mamaki sai Sadiya ta ji Nasir ya yi sallama, amsawa ta yi ta juyo tana masa sannunda zuwa ya amsa da fuska a sake, yana tambayar ta Kalifa ta ce yana ɗaki yana wasa, maimakon ya shige ɗakin Meenal sai Meenal ta ga ya juya da ledojin hannunsa ya nufi ɗakin Sadiyar.

Gaban Meenal ne ya faɗi a take ta shigar zargin ko dai da saka hannun Sadiya a rugujwar shirin da suka yi yau, wani ɓangarr na zuciyarta yana zargin ko dai Sadiya ta je tanyi wani abu ne da har Nasir ya kula ta yau.

Abin da Meenal ba ta sani ba shi ne wani maƙocin Nasir ne a kasuwa suke tattaunawa a kan yana gobe zai kai matansa kasuwa za su yi sayayya kowacce ta zaɓi abin da ranta yake so, a nan maƙocin yake cewa

"Ina tsoron shanyewar rabin jikina a ranar
ƙiyama shi ya sa ba na nuna bambanci a cikin matana, ko da a ce ba zan iya daidaita matsayi da soyayarsu a zuciyata ba tun da dama Allah ba ya amfani da fifikon soyayyar a zuciya kawai adalci ne na zahiri shi ya sa nake ƙoƙarin kiyayewa" Wannan furucin ne ya sa Nasir ya tuna rashin adalcin da yake yi wa Sadiya hakan ya sa ya ɗan sakko domin ya mata adalcin ko da kaɗan ne ba da yawa ba, sai dai ita Sadiya ganin abin da Nasir ya yi bai ba ta mamaki ba domin ta san tana kai kukan ta wajen ubangiji don haka ta san addu,ar ta ce ta fara karɓuwa.

Tana gama shanyar ta nufi ɗakinta. Meenal tun da ta ga ya kama hanyar ɗakin Sadiya sai ranta ya hau suya, dakyar ta yi yaƙi da zuciyarta ta shiga ɗakinta, shi ma don kar Sadiya ta gane ainihin ta razana da alamarin duk da an ce labarin zuciya a tamabayi fuska!.

Tana shiga ɗakin ta yi jifa da mayafin Momi wanda ta sako don hatta kayan jikinta na Momin ne har takalmi. Da sauri ta shiga leƙo tsakar gidan don ganin abin da yake wakana, ganin Sadiya ta nufi ɗakinta da turtsetsen cikin ta sai ta ji zuciyarta tana zafi. Safa da marwa ta fara a tsakar ɗakin tana son kiransa a waya ta tamabaye shi wannan sabon salon fa, sai dai tunowa da crwa ɓarayi sun yi sama da faɗi da wayar sai ta rungumi na annabawa.

Ta kasa zaune da tsaye gabaɗaya ba ta da nutsuwa tana ganin wannan raini ne yake ao ya ja mata. A ɓangaren Sadiya ko da ta shiga ɗakin ɗauke da sallamaa bakinta, tana shiga ta ganshi zaune a kusa da Kalifa ya buɗe masa biskit ɗin da ya fito da shi daga leda wanda dama shi ya siyowa, yaron sai murna yake yana ta taɓa jikin Nasir ɗin ganin yau bai kyamace shi ba, kuma bai dakatar da shi ba daga taɓa shi sannan bai haɗe masa fuska ba, uwa uba har da biskit ya siyo masa, sannan yana ta biya shi suna magana duk da gwarancin maganar ta shi ba komai ne ake fahimta ba.

Ranta ta ji ya yi wani sanyi, tana kallon Kalifa da tausaywa shi ma ga shi yau ya samu Æ´anci irin na sauran yara da suke samu a wajen mahaifinsu, shi ma yau yana ta dariya da farinciki sai ta ji gabaÉ—aya laifukan Nasir sun wanke daga idanunta duk da dama ba ta sakawa a zuciyarta amma dai ta san yana mata laifi. A rayuwa tana so a ce ko da ita ba ta samu komai ana kulawa ba to tana son Æ´aÆ´anta su samu hakan zai rage raÉ—aÉ—i.

Kalifa ya kalle ta ya ce

"Momma kalli Abba ya siyo mini biskit" Ya faɗa yana ɗago mata biskit ɗin fuskarsa a washe, har ƙwalla idanunta suka tara ganinncewa yaro ma ya san kyautatawa bare kuma babba.

Murmushi ta yi masa, sai ya taho yana ɗakko guda ɗaya ya nufi bakinta hakan ya sa ta buɗe bakin ta gutsuwa, shi kuma Nasir sai yake kallonsu yana murmushi. Allah kaɗai ya san yadda Sadiya take ji a ranta abu ne da suka rasa a iya zamansu a gidan amma yau rana ɗaya ga shi sun samu wannan yake nuni da cewa mahaƙurci mawadaci!.

Sannu da zuwa ta ƙara masa ya amsa yana murmushi, leda ɗaya ya ɗakko ya miƙa mata ta karma da hannu biyu. Kallonsa ta yi ta ce

"Za ka yi wanka?"

Ya ce

"Akwai ruwa mai É—umi?"

,Ta ce

"Eh akwai" Ta faÉ—a masa don ta cika filas É—in shayin, ruwan wanka ta je ta haÉ—a masa ya tashi ya je ya yi wanka ya yi alwala ya fito.
Bayan ya shafa mai dama kayan jikinsa ya mayar kasancewar babu kayansa a É—akin duk suna É—akin Meenal shi turakar tasa ma dama ba zama yake a ciki ba kawai É—akin Meenal ne yake zuwa. Bai ce mata komai ba sai ta ga ya fito falon ya É—auki É—aya ledar da ya ajiye a gefe ya juya zai fita sai Kalifa ya bi bayansa abin mamaki sai ta ga ya kama hannun Kalifan sun fita.

Gabaɗaya ta yi ɗiff tana ta mamakin abun kamar a mafarki. Ɗakin Meenal ya nufa yana shiga lokacin tana banɗaki, ledar ya ajiye a kan madubi, ya buɗe drower kayansa ya ɗakko kayansa lodi guda ya fito Kalifan yana biye da shi, kayansa gogaggu wajen kala goma ya shigo ɗakin da su, yana shigowa ta tashi ta karɓa, ta nufi bedroom don saka masa a drower. Yana bata ya ƙara komawa hannunsa riƙe da na Kalifa jallabiyarsa ya ɗakko guda uku, har lokacin Meenal ba ta fito ba, ita kuma ta ji shigowarsa domin ta ji motsi sai dai ta san shi ne ya shigo tana son sai ta gama abin da take ta fito ta zo ta sauke masa ruwan masifa.

Ba ta zaci kaya yake ɗauka ba, lokacin da yake shirin fita daga ɗakin yana riƙe da kayan da hannu ɗaya ɗaya hannun ya riƙe Kalifa sai kawai ta buɗe banɗakin ta fito, tana fitowa ta yi mugun gani da sauri har tana neman faɗuwa ta nufo shi ta ce

"Nasir mene ne nake gani haka?" Ta faɗa ranta a ɓace.

Yana É—an murmushi ya ce

"A ina fa?"
A gadarance ta ce

"Oh ni kake tambaya? Baka ga ko da muka shigo gidan nan ban sake saka ka a idanuna ba, sai yanzu ka shigo kuma yanzun ma kana shirin fita,wannan kayan fa ko na bayarwa ne"

ÆŠan jim ya yi sai ya ce

"Yau a É—akin Sadiya na sauka" Duk da ta san hakan amma yadda ya furta sai abin ya mata ciwo, hakan ya sa ta ce

"Mai kake nufi? Ba dai rabon kwana za ka fara mana ni da ita ba?"

Ya ce

"A,a kawai dai ita ma zan kwana a É—akinnta ne...

Ta katse masa hanzari da faÉ—in

"Kar ma ka fara wallahi"

Bai jira cewar ta ba ya juya ya bar ra a tsaye kamar ta rafka ihu tsabar takaici haka ta ji, wani tsaki ta duka tana juyawa ta yi ido huÉ—u da ledar kan mudubin ba ta yi wata-wata ba ta É—auka ta yi wurgi da ita kayan ciki suka tarwatse.

Ko da ya koma ɗakin bedroom ya shiganya sauya kayan jikinsa ya fito da jallabiya a jikinsa ya ce mata zai je masallaci ta ce masa sai ya dawo, yana fita Meenal ta jiyo rufowar ƙofar gida hakan ya ba ta tabbacin ya fita da sauri ta fito har tana tuntuɓe a barandar ƙofar ɗakinta, ta ji yadda yatsanta na ƙafa ya bugu amma ba ta damu da zugin da yake mata ba, burinta ta shiga ɗakin Sadiya.
Chapter 93 · 0% Book details