← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 106

Sashe 29

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abun da ya sake ɓullowa dangane da yaran nata shi ne, yanzu ba sa dawowa gida da wuri duk da ba tare suke ba amma kowa dai yanayin zamansa a gida ya sauya, idan ta yi wa kowane daga cikinsu magana sai ya kare kansa da cewa yana school ko dai ya ƙirƙiri wani abu da ba zai gamsar da ita ba, ta yi faɗan ta yi nasihar amma bata sauya zani ba. Abin ya fara ci mata tuwo a ƙwarya ya fara tsamarin da take son tuntuɓar mahaifinsu a kan abin da ya shafi ƴaƴan amma tana tsoron mai zai biyo baya, tsawon wata biyu tana fama da hakan shi kuma ba mai zaman gidan ba ne idan ma ya dawo gidan ko bai gansu ba babu abin da ya shafe shi ba zia tambaya ba ma.

Yau ta kama talata, a yau ne kuma ta yi ƙarfin halin yanke hukuncin tunkararsa ko da zai bata wata mafita tun da tunaninta ba zai zama ɗaya da nashi ba, duk da ta wannan ɓangaren yana so ya bata shugabancin!.

Tun da ta fito falon yana zaune yana karatun jarida, da ta yi sallama ma bai É—ago ya kalleta ba ya dai amsa amma a ciki-ciki. Daga gefensa ta zauna ta juya ta kafe shi da ido sai ta ga babu annuri ko walwala a fuskarsa. Idanu ta mayar kan dining da Æ´ar aiki take ta aikin jera abincin yanzu lokaci na tsakanin magriba da isha'i amma daga Zalika har Mubin babu wanda ya dawo kuma yau shi ne karo na farko da suka kai ya haka basu dawo gidan ba, shi ya sa ta rasa sukuni da natsuwar zuciya ta zo domin tattaunawa da mai gidan nata, duk da ta san da wuya ya bata haÉ—in kai.

Idanu ta É—auke daga kan dining É—in ta mayar kansa tana mai sauke ajiyar zuciya, kamar mai tsoron furta kalmomin bakinta ta yi ta maza dai ta ce

"Barka da hutawa" Bai amsa ba kuma bai daina abin da yake ba. Ita dai burinta su samu mafita a kan canjin da rayuwar ƴaƴansu ta yi, ko da a ce bai yi komai ba shi a matsayinsa na namiji idan ya tsawatar wataƙila su daina.

Duk da banza ya yi da ita kuma ta ji haushi duk da ba wannan ne karo na farko ba, amma ta danne ta ce

"Ya gajiyar kasuwa?"

A taƙaice ya ce

"Lafiya" Ta É—an nisa ta ce

"Wallahi dama ina tafe da magana ne mai muhimmanci, a kan maganar yaran nan wallahi al'amarinsu ya fara bani tsoro ta yaya za a ce...

Wata tsawa da ya daka sai da ta tsorata!. Ya yi wurgi da jaridar hannunsa yana mai É—aga mata hannu ya ce

"Ya ishe ki haka, ta yaya duk inda kika ga na samu nutsuwa sai kin rusa shi? Na tafi kasuwa nema na dawo amma ba za a barni na huta ba sai a zo a sakani a gaba da matsalolin gida, mai kuka nema kuka rasa a gidan nan, komai akwai babu ta inda na tauyeku Allah ya min arziƙi na rufin asiri kuma ina muku komai, amma saboda son zuciya a ce hatta matsalolin ƴaƴa ma tare za mu raba? Ke ba za ki ji da tarbiyarsu ba?" Tun da ya fara maganar zuciyarta take ƙuna.

Kafin ta ce wani abu ya cigaba da kora mata warning yana cewa

"Kamar yadda na faɗa miki a baya, duk wata matsala da za ya kunno kai ke za ki magance ta, tarbiya ta mace ce shi uba abinci da sauran ɗawainiya yake yi don haka idan har kika ci gaba da damuna da lamuran gidan nan walllahi wallahi wallahi kin ji na yi rantsuwa kuma ba zan yi kaffara ba to igiyar aurenki tana rawa" Idanunta sun kawo ƙwallah amma ta rasa ma mai za ta furta masa ya gane cewa ba ƙaramar matsala ba ce yake mayar da ita ƙarama.

Yana gama faÉ—ar hakan ya tashi a fusace ya nufi dining da ido ta bi bayansa da kallo, yana zuwa ya yi saving kansa ya ci ya tashi, ya fita masallacin isha'i don har lokacin yaran babu wanda ya dawo.

Lokacin da aka fito daga masallaci ya dawo gidan, yana zuwa ya zauna a falon ita kuwa har lokacin tana wajen a zaune kamar an dasa ta dama tana hutun sallah amma kuma abinci ma bata da nutsuwar cinsa, hankalinta yana wajen inda yaranta suke musamman Zalika wacce ta kasance mace!.

Yana zama ya fito da waya yana ta magana tana raha, tsaye ta miƙe tana son barin falon sai kawai aka buɗe ƙofa aka shigo, ganin Zalika riƙe da jaka da sauri ta nufe ta tana kiran sunanta, amma sai ta ga Zalikar hankalinta kwance ta amsa da faɗin

"Na'am Mamy"

Hankali tashe Mamyn ta ce

"Daga ina kike Zalika, mai ya zaunar da ke a makaranta har zuwa wannan lokacin?" Ta jero mata tambayar zuciyarta cike da fargabar amsar da Zalika za ta bata tana riƙe da kafaɗar Zalikar.

Duk wannan abin da ake Baffa ko kallo basu ishe sa ba wayarsa yake hankali kwance.

Zalika ta ce

"Haba Mamy ki kwantar da hankalin ki mana" Hannun Zalikar ta kamo suka ƙaraso tsakiyar falon, Zalika ko a ranta bata ji fargabar tambayar da Baffa zai mata ba saboda ta san ma ba zai taɓa tambayarta daga ina take ba.

Lokacin da suka ƙaraso ya gama wayar ta ɗan rusuna ta gaishe sa, ba tare da ya kalle ta ba ya amsa mata, tashi ta yi ta nufi ɓangarenta Mamy ta take mata baya, Mamy da fara tafiyarta ta ji maganar Baffa ya ce

"Kike dai kulawa da nauyin da yake kanki don ni tuni na sauke nawa nauyin" Yana kai wa na ya yi shiru ita kuma bata amsa masa ba kuma bata juyo ba ta ci gaba da tafiya don dama ta san zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi wato yana nufi ta kula da tarbiyarsu shi ya sauke nauyin abin da yake kansa na ɗawainiya.

Zalika tana zuwa É—akinta ta jefar da jakar a kan gado ta zauna kenan sai ga Mamy kamar an jefo ta ta shigo ta zauna a bakin gadon kusa da Zalika tana kallonta ta ce

"Wai daga ina kike?"

Zalika ta ce

"Daga makaranta mana"

Mamy ta ce "Makaranta?" ya war haka mai kike a makaranta?", Hannu ta miƙa ta ɗakko jakarta wani littafi ta nunawa Mamy mai ɗauke da rubutu wanda a ƙalla ta yi sati ma da yin rubutun ta nuna mata ta ce

"Wannan rubutun na zauna yi, ina hostel wajen su Islam ina kwafar rubutun da na ce ta ara min littafin in taho da shi gida sai ta ce karatu za ta yi cikin dare wannan ne dalilin da ya sa na kai yanzu" Ƙuri Mamy ta mata da idanu kawai dai a ranta tana jin maganar bata gansu ba amma yadda Zalikar ta yi magana babu alamun ƙarya sai ta ji hankalinta ya kwanta. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce

"Amma mai ya sa wayarki a kashe"

Zalika ta ce

"Ai kuwa wayata a kunne sai dai matsalar netwrk"

Mamy ta É—aga wayarta ta kira Zalika sai ga waya tana ringing, bayan kuma duk tsawon lokacin tana kiran wayar amma a kashe, haka ta amince da maganar Zalika sai kuma hankalinta ya koma kan Mubin tana tunanin rashin nasa dawowar.

Shi ma wayarsa a kashe amma Zalika tana ta cewa da daina damuwa ai shi yanzu ba yaro ba ne, ita kuma tana zulumi da tunanin shi yaro ai ba a gama tarbiyarsa, sannan sai ka kwashe shekaru kana ba ƴaƴanka tarbiya amma sai a samu rana ɗaya wasu su warware maka tsohuwar saƙar da ka yi ta shekara da shekaru.

Baffa yana gama uzurinsa ya koma ɓangarensa hankali kwance ya kwanta, bai ƙara bi ta kan cewa Mubin ya dawo ko kuma bai dawo ba, Mamy kuma tana ɗakinta ta kasa sukuni, duk hankalinta a tashe, wajen sha ɗaya da rabi ta ji mai gadi ya buɗe get da sauri ta tashi ta leƙa window sai kuwa ta ga hancin motar Mubin ya shigo harabar gidan, hango motar Zalika a ajiye a rufe ya sa ta gane Zalika yau ba da mota ta fita ba. Har sai da ya fito daga motar ya rufe, ya nufo ƙofar da za ta sada shi cikin gidan, cikin sauri ta fito daga ɗakinta ta nufo falon domin jin abin da Mubin zai ce mata wato daga ina yake da wannan tsohon daren.

*SADIYA*

Rayuwa ta ci gaba da gudana yau fari gobe baƙi, har ila yau bata sauya zani daga wajen Nasir haka ma ɓangaren mahaifiyarsa da ƙannensa, sun mayar da ita wata banza kowa yana kwaso sharar da ya ga dama ya watsa mata, a ganin Sadiya ba kowa ba ne ya jaza mata wannan sai iyayenta wanda su suka ja mata raini da wulaƙanci a wajen miji!. Koyaushe tana zulumin kai musu damuwarta domin babu wanda zai magance mata matsalarta, watarana ma idan Nasir ya kuntuka mata wani abun, haka za ta zauna kwana da kwanaki tana ƙunsar takaici sai dai idan ta shirya da nufin ta je gida don a sama mata mafita, tana zuwa gidan dai ta tarar da gidan a kacame Baba yana ya masifa ya hana kowa sakat yana yi wa sauran ƙannen nata tijara a kan rashin mijin da basu samu ba, wannan dalilin yake saka ta danne tata damuwar ta koma gidanta. Ka zalika ita ma mahaifiyarta da ita take ganin mace ce kuma bahaushe yana faɗin ciwo ƴa mace na ƴa mace ne, sai dai idan ma ta yi ƙoƙarin sanar da ita sai ta dakatar da ita ta hanyar bata haƙuri ba tare da ta bari ta ji matsala da damuwar ba.

Sannan ita tana ma jin tsoron a tunkari Nasir da wata magana domin ba ya ganin kan kowa da gashi, ta san ma muddin aka masa magana tamkar an zubawa wuta fetur ne a maimakon a samu sauƙin lamarin sai abin ya ƙara hauhawa.
Chapter 29 · 0% Book details