← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 106

Sashe 21

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya nisa tare da sakin wata ajiyar zuciya yana duba naira miliyan uku a gabansa wanda 500k guda shida kowanne nannaɗe da kyaure, yana tunano yadda suka gabatar masa da kansu a matsayin baƙinsa da suka yi waya cewa za su zo bayan sallar isha'i bai taɓa saka ran zai gansu ba shi ya sa da ya ga zuƙeƙiyar mota ma bai kawo cewa baƙin nasa ba ne.

Yadda suka karrama shi duk da yana da labarin Alhaji Sule bashi da wulaƙanta ɗan adam ya san mutuncin mutane amma sai ya ga abin ya fi yadda ake faɗa, tabbas zai yi alfahri a ko ina da mijin da Jidda za ta aura saboda ko da ya zo ya gaishe shi haƙiƙa ya yaba da hankali da tunaninsa, kuma a yadda ya ganshi bai taɓa tunanin masu hannu da shuni ne har haka ba, amma ya zo gidan talakawa neman aure haƙiƙa duk wanda ya auri Jidda ya dace da mace kamila kuma ta gari, duk da ba shi ya haifi Jidda ba amma yana alfahri da ita, kuma ya yi wa su Alhajin bayanin wace ce Jidda kuma sun ji sun gani.

Kuɗin ya fara tattarawa yana tunanin yadda zai yi da wannan kuɗin, tun da shi kaɗai ya karɓi baƙin nasa, duk da naira miliyan goma suka bayar a matsayin kuɗin gaisuwar uwa da uba da kuma kuɗin kuɗin saka rana gabaɗaya suka kawo amma ya ce shi ba zai karɓi miliyan goma ba ya yi yawa dakyar ma ya ɗauki miliyan uku.

A fili ya furta

"Alhamdulillah, Allah na gode maka da ka bani iko zan sauke nauyin marainiyar nan, zan damƙa ta a hannu na gari Allah ka taya mijinta riƙo ka bashi ikon kulawa da ita!" Gabaɗaya ya kwashe kuɗin ya saka a babbar riga bayan ya ware dubu goma ba don komai ya yi hakan ba sai don kar ya saka Umma ko Aliya jin wani abu marar daɗi a ransu saboda shi kansa bai zaci haka ba kuma ya ga suna farinciki da abin da Kasim ya mata, kar su fara raina abin da ya yi.

Gidan ya shigo ya same su suna zazzaune, suna cin abinci ɗaki ya shiga ya ɓoye gabaɗaya kuɗin yana sakawa a ransa cewa bayan bikin zai samu kadara ya sayawa Jidda da kuɗin wannan don bai yarda ya ba kowa kuɗinta ba.

Bayan ya fito ya zauna ana hira yana cin abinci sai da ya kammala ya yi gyaran murya ya ce

"Ummar yara" Umma ana washe baki aka ce

"Na'am" Ya É—an nisa kaÉ—an tare da zaro dubu goman aljihunsa ya ajiye ya ce

"Ga kuɗin gaisuwa da saka ranar ƴarki Jidda!." Gaban Jidda ne ya bada wani rasss a inda Umma da sauri kafin ta furta komai ta miƙa hannu ta ɗauki kuɗin a fili ta fara irgawa tana cewa

"Dubu ɗaya, dubu biyu, dubu uku, dubu huɗu, dubu, biyar" Da ta zo kan dubu biyar sai da ta ɗago kai ta kalli Jidda wacce kanta yake sunkuye saboda kunya ita kuma Aliya bakinta washe tana kallon hannun Umma saboda tana ganin kuɗin hannun Ummar da take irgawa ya kusa ƙarewa. Umma ta ci gaba da irgawa tana murmusawa cike da ƙeta a ranta ganin dai kuɗin bashi da maraba da sadaka, da ta zo dubun ƙarshe sai da ta ƙara sautin ta ta ce

"Dubu goma cass" Ta faÉ—a tana kallon Abba da yake murmushi kafin ya furta wani abu Jidda ta tashi da sauri saboda kunya ta nufi É—aki. Umma a zuciyarta ta ce

'Shegiya aniyarki ta biki wato ba za ki iya kukan baƙin ciki a gaban mutane ba sai kin shige ɗaki taɓɗi lallai iska tana yawo da mai kayan kara in banda matsiyaci kika kwaso har yaushe zai kawo dubu goma' Maganar da Abba ya mata ne ya dawo da ita daga maganar zucin da take ya ce

"Kin gama irgawa" Tana dariya mai sauti ta ce

"Wallahi na gani abin arziƙi yarinya ta yi goshi" Aliya ta ce

"Umma dubu goman ne goshi" Ta faÉ—a tana Æ´ar dariyar yadda Jidda za ta ji, Abba ya ce

"Ke ba na son shashanci tashi ki tafi ki ba mutane waje" Da sauri ta tashi ta shige É—aki tana shiga ta rungume Jidda ta ce

"Amarya ta ango ya kawo mata dubu goma" Jidda duk sai ta ji kamar ta nutse ita kuma Aliya murna take ganin ta fi Jidda komai dama ta san babu yadda za a yi ita kyakkyawa mummuna ta fi ta komai na aure!.

Tun da aka saka rana wata guda sai soyayya da shaƙuwa suka ƙara tsananta a tsakanin masoyan biyu wato Jidda da Ibrahim, kowa ƙoƙarinsa ya ba ɗan uwansa kulawa tamkar ƴan biyu haka suke rayuwarsu kamar dai ƴan uwa ba wai wanda soyayya ce ta haɗa ba!.

Abba ya yi ƙoƙari ya saya musu kayan ɗaki iri ɗaya daidai ƙarfinsa, a inda ya saya kayan kicin ma komai babu bambanci. Sai dai Umma tana ta sayan kayan kicin tana turawa ƙasan gado don bata yarda a ce da Jidda marainiya da kuma Aliya mai uwa a raye an musu komai da komai iri ɗaya ba.

Jidda sosai suke murna ita da ƙawarta Salama Jidda za ta yi aure!.

Mummy yau saura kwana biyu su dira a Nigeri'a za su dawo daga Dubai inda suka tafi sayyayar kayan lefe.

Yau saura kwana biyu a kawo lefe don ranar ta kama gabaɗaya tare za a kawo domin Abba ya sanar da kowanne ɓangare na maza cewa rana ɗaya za a kawo. Aliya da Amatallahi suna ta rawar kai sanadin wasu hotuna da Kasim ya turawa Aliya na wasu lesuna ya ce kaɗan daga cikib kayan da aka saka a lefe ne sauran sai an kawo ta kashe ƙwarƙwatar idanunta. Wannan dalilin ya sanya Amatullahi da Aliya cewa ranar kawo kayan lefen a ɗakin Umma za su ɓuya babu inda za su tafi domin a kawo a kan idanunsu saboda Aliya ta sanar da Kasim cewa a samo motar da za ta kawo masu kawo kaya, hakan ya sa ya ce ai dole ma ya samo motoci, kanta ya fashe suna ta yadawa Jidda magana wacce ita bata wani damu da abubuwan da suke faɗa ba. Har yau bata san waye Ibrahim ba shi kuma yana jin daɗin mu'amala da ita a hakan rayuwar duniya bata dame ta ba kuma har yau ko ɗankwali bai bata kyauta ba bare naira biyar sai dai yana mata wani tanadi na musamman a cikin gidanta wanda farinciki ne da kwanciyar hankali in sha Allah.

Yau ya kama alhamis ranar da za a kawo lefen Jidda tun da rana ta shirya ta cewa Umma ta tafi gidan su Salama, suna can suna ta murna da kuma sakawa a ransu cewa duk abin da aka kawo za su karɓa su yi farinciki!.

A zaure Abba da ɗan uwansa da kuma amininsa da maƙota guda biyu. Umma ita da ƙawarta sun kasa zaune sun kasa tsaye suna ta tunanin yadda za a kawo kayan nan sun da Umma tana ganin kayan saka rana ma an yi musu bajinta bare kuma lefe mai kankat.

KuÉ—i ma sai da aka É—ora dubu ashirin.

A can gidan Daddy zuƙa zuƙan motoci kuma galla galla sabbi dal, sai sheƙi suke na sabunta da kuma gani ka san sun ci kuɗi. Guda uku aka ware inda ma'aikatan gidan suke fito da wasu kyawawan kwatuna suna lodawa a motocin sai da suka gama saka wa tas, maza biyar ne wanda za su tafi kai kayan inda kowacce mota da direba. Wata baƙar mota sabuwa wacce ita ma gabaɗaya kujerunta ledojin sabunta ne za an buɗe get motocin za su fita Daddy ya zaro mukullin daga aljihu ya miƙawa wani direban da yake a tsaye karɓa ya yi ya shiga motar suka jera suna tafiya a laye sabuwar baƙar motar ce a tsakiya suna fita aka rufe get ɗin suka lula a saman titin da tamkar domin su aka yi shi, suka tasamma gidan su Jidda.

Ibrahim da yake kallonsu ta saman windown a bene ganin fitarsu ya ɗaga hanni yana godewa Allah tare da fatan Jidda ta ci gaba da amincewa da shi don ya san yau kayan lefensa za su tabbatar mata da waye shi, tun da ta faɗa masa an kawo dubu goma kuma bai ga alamar rainuwa a tare da ita ba, tabbas ya san Jidda tana masa wani ɓoyayyan so duk da tana bayyanawa amma ya san baki ba zai iya furta yawan son da take masa ba. Duk da ya san wanda take masa ba zai kai wanda yake mata ba.

A can gidan su Kasim, Kasim ne tsaye a ɗakinsa ya rasa yadda zai yi saboda ya faɗawa mahaifinsa cewa ga abokansa nan za su zo su kai su a motoci shi ne yake ta masa faɗa yana mene ne wani abin motoci kar wani mai motar da ya zo masa ƙofar gida, a ƙafafunsu za su je suna tafiya suna hira, haka yana ji yana gani Baban nasa ya kirawo wani mai ruwa ya ce ya zo da zai yi hayar baro, haka ya ɗakko baron aka ɗora akwatuna biyu sai ƙaramin kit guda ɗaya suka nufi gidan su Aliya.

Mai baron yana gaba maza guda uku suna binsa a baya shi kuma Baban Kasim É—in ya koma cikin gidan.

MAMAN AFRAH
09025576222

https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=ems_copy_t

*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 9️⃣

*SADIYA*
Chapter 21 · 0% Book details