← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 106

Sashe 47

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Juyawa kawai ta yi ta fita wanka ta yi amma na farin ruwa wato wanlan janaba, tana gamawa ta ɗauro alwala ta fito, a bakin ƙofa suka ci karo da Kasim ya matsa mata ta wuce, sallah kawai ta yi ta sake sauya wata rigar ta koma falo ta zauna ta harɗe ƙafa, har ya gama abin da zai yi ya zo ya yo sallar ya koma ya zauna a kan sallayar ya jingina da bango. Wajen ƙarfe tara ya fito ya zo ya ce

"Aliya mai za ki ci" Ko kallo bai iishe ta ba, ya ɗauki filas ɗin ruwan zafi a kicin ya jona ruwa a kyatil ya kunna ƙaramin gas ɗin ya ɗauki ƙwai guda uku ya fasa ya saka maggi da albasa ya shiga soyawa don shi ba ya jin ma zai iya cin wani abu. A lokacin da yake kicin lokacin ne kiran Umma ya shigo wayar Aliya Umma da ta ƙule a ɗaki saboda kar baƙin da suke tsakar gidan su ji wayar da za ta yi don Abba ya fita, bayan Aliya ta ɗauka Umma ta ce

"Aliya ya fita Kasim É—in?" Aliya ta ce

"Umma babu inda zai je yana nan fa" Umma ta ce bari na kira ki an jima" Tana faɗar hakan ta kashe wayar. Shayi ya haɗa mata ya ajiye a gabanta da wainar da ya yi amma ta saka ƙafa ta ture kofin shayin ya zube ta saka ƙafa ta taka wainar, wannan abin da ta yi ba ƙaramin ƙonawa Kasim rai ya yi ba har ta ga gabaɗaya fuskarsa ta sauya, amma sai bai ce mata uffan ba ya ɗauke ya zo ya gyara wajen, ɗaki ya koma ya kwaso kayan shimfiɗar ya wanke ya shimfiɗa wani zanin. Ganin goma ta yi ya saka takalminsa ya fita daga gidan ko magana bai mata ba.

Don yanzu zuciyarsa ta fara masa wasi-wasi a kan Aliya ya ga abin nata ba na ƙare ba ne, ya san a iya saninsa Aliya ita ta amince da aurensa ba ya manta ranar da aka kai mata kayan saka rana yadda ta yi ta gode masa kamar ta goya shi amma yanzu komai ya sauya tun daga ranar da aka kai kayan lefe kenan dama abin hannunsa take so ba shi b?

Ko da ya fita wuri ya samu ya zauna a waje ya kira Salis yana faÉ—a masa cewa Aliya ta ga halittarsa tana masa tijara sannan ya faÉ—a masa abin da ta masa da ya mata girki.

Salis cike da ɓacin rai ya kawo wani zagi mai maiƙo ya danƙara ya ce

"Wai wannan yarinyar mai take nufi da kai, ya za ka je kana neman zama matar kana neman bata matsayin naka da Allah ya baka na namiji, ai mace ita ce a ƙasan namiji amma kana neman mayar da kanka wani nusari, a wannan zamanin har ta samu namijin da zah shiga kicin ya sama mata abinci amma take neman ta yi wasa da damarta na lura Aliya ba albarkar zaman aure take nema ba, wallahi jiya sai da na zo na kwanta abin da ta maka a kunnen abokanmu ya ɓata min rai" Kasim kamar zai yi kuka ya ce

"Wallahi na ga abin nata ba na ƙare ba ne abin ma kamar dai ci gaba yake" Suka ci gaba da tattaunawa.

Aliya kuwa yana fita ta É—aga wayarta mai fashashshen screen ta shiga kiran wayar Amatullahi, bayan ta É—auka ta ce

"Ƙawata amarya wato an kwana ana kwasar amarci shi ne yanzu da aka wartsake aka kirani" Ta faɗa cike da zolaya Aliya ta ce

"Dalla can malama rufewa mutane baki ana ga yaƙi kina ga ƙura, mutumin da ya min fyaɗe" Amatullahi ta fashe da dariya ta ce

"Batun nawa dai ya zo wato an ci amarcin dai ai ni dama na san duk wayon amarya dole sai an sha manta" Wani tsaki Aliya ta doka ta ce

"Idan kika ƙara ambaton amarcin nan sai mun ɓata, na kira ki ne in faɗa miki wani sabon tashin hankali da na tsinci kaina a ciki"

Cike da ɓacin rai ta ce

"Subhanallahi Allah rabamu da tashin hankali ni fa dama jiya ganin kina kumbure-kumbure shi ya sa ban tsaya yi miki sallama ba, saboda na ga sai ki mini rashin m... Aliyanta katse ta da faÉ—in

"Amatullahi Kasim mata maza ne" Amatullahi zaune ta tashi daga kan doguwar kujerar da take kwance a falon gidansu tana mai saka hannu ta toshe bakinta ta ce

"Mata maza fa? Ke yanzu Aliya duk bita da ƙullin da kike yi wa mutumin nan sai kin bishi da sharri?" Aliya cike da haushi ta ce

"Wai sharrin mai kike nufi? Ina miki maganar tsakani da Allah mata maza ne Kasim amma kina wani batu" Amatullahi ta ce

"Innalillahi mun shiga uku, kuma kika zauna a gidan Aliya?" Aliya ta ce

"To ya zan yi?" Amatullahi ta ce

"To ke ba shikann ba kin samu maƙalar rabuwa da shi sai ki ce ya yaudare ki bai sanar da ke ba in ya so kin ga kin samu hanuar yakice shege daga rayuwarki dole ya sake ki tun da babu wacce za ta zauna da mata maza, kin ga burinki yana dab da cika na auren mijin Jidda tun da ba uwa kuka haɗa da ita ba, sannan ba uba kuka haɗa ba bare a ce ya hakan ya haramta" Dididim gaban Aliya ya buga a take ƙwaƙwalwarta ta fara mata safa da marwa lokaci guda wani abu ya ɗarsu a zuciyarta, sai dai furucin Amatallahi ya katse matq hanzari in da ta ce

"Ina fatan dai babu abin da ya shiga tsakaninku, don mar a je yin abu sau ɗaya ya ɓata miki abubuwa dubu!" Aliya cikin rashin fahimta ta ce ban gane ba?"

Amatallahi ta c

"To idan yi ɗaya an samu ƙaruwa fa kin ga ko sakin ki ya yi ya barki da jelar goyon ciki da reno"

MAMAN FRAH
09025576222

[11/7, 9:00 PM] 😍: https://chat.whatsapp.com/GTq4oSxwxZfLKU7Amx5My1?mode=wwt

*RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka)
*NA*

*MAMAN AFRAH*

BOOK 1️⃣
PAGE 1️⃣6️⃣

Wannan grp ni
MAMAN AFRAH na buɗe shi ne domin masu soh saya kayan sallah su yi adashe, za ka zaɓi abin da kake so ka zuba kuɗinka ya danganta da yadda kake so. Duk abin da ka zuba a rubuce yake daga ka gama za a baka kaya.
1-Leshi 4-abaya
2-Atamfa. 5-kayan yara
3-shadda 6-Mayafai

7-Takalmi da jaka
8- Takalman yara

Da sauransu idan har kin san ba yi za ki yi ba karki shiga min grp don cire ki zan yi, ba wasa ya taramu a ciki ba.

Maman afrah
09025576222

*SADIYA*

Tun da suka ɗauki hanyar gidan gabanta yake faɗuwa, tunaninta ɗaya kar Nasir ya yi wa Baba tijara a gabanta domin ba za ta ji daɗin hakan ba, duk da shi Baban yana ganin yana musu ruwan kuɗi amma da alama har yau bai san waye Nasir ko kuma dai ya sani takewa yake yi. A ɓangare ɗaya na zuciyarta yana cike da fargabar ko dai Nasir ya sawwaƙe mata ne babu laifin fari bare na baƙi duk da cewa ita ba tsoron sakin take yi ba kawai tana shayin halin Baba ne yadda yake da son aurar da ƴaƴa tamkar rai da mutuwa. Duk da yanzu ta samu sassauci na zaman gashin ƙumar da Nasir yake mata a cikin gidansa kuɓa ba komai ba ne ya kawo mata wannan sauƙin sai sana'ar da take yi don ta lura da cewa idan har kana da sana,a to baka ma jin zugin ɓacin rai idan an maka saboda wani sa,in rashin zaman lafiyar da yake wanzuwa tsakanin wasu ma,auratan har da ganin matayensu basu da sana,a bare aikin yi, suna ganin duk wata ɗawainiyar mace su za ta ɗorawa amma ba duka aka taru aka zama ɗaya ba wani namijin ko kina sana,a ko aiki babu ruwansa da harkar kuɗinki kuma zai yi abin da ya dace da ɗaukan gabaɗaya ɗawainiyarki da sauke haƙƙinki da ya rataya a wuyansa. Wani namijin kuma shi yana jin daɗi ya ga matarsa tana da abin yi wato ta tsaya da ƙafafunta har ma da kansa zai ke ƙara mata ƙarfin gwiwa, wani kuma sai dai ma ya san duk yadda zai yi domin ganin ya murƙushe komai don kar ki ci gaba saboda yana baƙjn ciki wani kuma yana tsoron ki samu wani ci gaba ko ɗaukaka ki fi ƙarfinsa kowa dai da yadda ya ɗauki rayuwa kuma da yadda yake kallon ta.

Sadiya bata san sun shigo layin gidan nata ba domin ta yi nisa a duniyar tunanin da ta lula maganar Baba ce ta katse mata tunanin har hakan yansa mai napep É—in jan wani uban birki don ya tsorata da furucin Baba ya É—auka ma wani gagarumin abu ne ya faru, jin Baba ya ce
Chapter 47 · 0% Book details