← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 106

Sashe 60

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka tafi da wannn silindar a sako gas" Ɗan dimm ya yi abu ne da bai saba ba shi har ya manta ma da ya sayi wani gas tun lokacin da Hajiya ta dakatar da ake sakawa Sadiya ta ce ta koma amfani da gawayi ai kuɗin ya yi wani amfanin da shi sai gashi kuma yanzu za a ɓallo masa ruwa, tunanin da yake kenan ita Meenal ɗin ba za ta yi amfani da gawayin ba ko yaya? Tunaninsa ya katse ne daga inda ta ce
"Amma fa karka sako mana have a ciko shi sosai" Da alamun tambaya a fuskarsa don ya kasa jurewa ya ce
"Dama ba a gidansu amarya ake ciko silinda ba?" Wani yatsin fuska ta yi ta ce

"Haba Alhaji Nasiru uwata ce za ta cika maka gas ɗin ma sai ka ce ita za a dafawa abincin" Bai tanka mata ba ya wuce ya ɗauki silindar ransa duk babu daɗi, yana kusa da ƙofar zaure ta ce

"Nasir ka siyowa ƙawayena snacks da drinks masu sanyi saboda yanzu rana ta yi idan suka ci sai su yj girki sun ce min basu karya ba, kuma iya sauran abin da muka ci da dare suka ci" Tsabar mamaki ma sai ya ji kamar ya wanka mata mari yana ta tunanin to ita bata da aiki sai kawo buƙata daga tarewarta jiya bayan sun kwaso yuya guda babu izininsa sun cika masa gidan sannan banda abincin da za su girka ake batun ya siyo wani bayan shi abincin ma bai samu natsuwar ci ba sai ma yake ga kamar bata damu da shi ba.
Ƙarfin hali ya yi ya ce

"Haba Meenal yanzu ƙawayen nan naki kusan rai goma duk ni zan siyo musu abu?" Tana masa kallon ko dai ka kasa ta ce

"Nasir su goma sha biyar ne fa, wasu ma don basu zo ba yadda nake da farin jinin ƙawaye ai baka ga komai ba wasu ma a gaba za suke kawo mini yini ka ga kuwa ai dole a tarɓe su don ni ba zan yi abin kunyar da ƙawayr za su yi gaba suna gulmata ba" Ta faɗa ba tare da ta jira cewarsa ba ta juya ta shige falo sai shewarsu ya jiyo. Kai ya kaɗa ya fita ya buɗe but zai saka silindar tsayuwar napep ɗin Hajiya ya dakatar da shi, fitowa ta yi tana ba mai napep kuɗinsa.

Bakin Hajiya kamar ƙofar gari haka yake a buɗe don tana miƙawa mai napep kuɗi ne amma idanuta suna a kan silindar gas. Da sauri ta juyo tana rufe bakin jakar hannunta ta ce

"Nasir mene ne wannan ? Ina za ka je da shi"
Cikin sanyin murya ya ce

"Gas zan sako"

Hajiya da mamaki ta ce

"Gas kuma Nasir na É—auka ma siyar da silindae za a yi" Nasir ya ce

"Meenal ta ce in ciko musu da gas"
Hajiya ta c

"Ka ciko musu kuma, yaushe yarinyar nan zuciyarta ta zama kare ya ɗauke yanzu har ta ɗauki kishiya wata tsiya da za ta ce a ciko musu gas, ni yanzu dama an saya mata kuka gas ne Meenal ɗin to mai ya hana a ciko mata da gas ɗin daga gida wannan ai ɗora nauyi ne ko zazzaɓin haɗa lefe bai bar aljihunka ba hallaw za a ɗora maka wahala" Ta faɗa tana kumfar baki Nasir ya ce

"Hajiya ba fa ita da Sadiya ba ƙawayenta ne fa a gidan suka zo za su yi girki" Har da dafe ƙirji ta ce

"Girki kuma? Ni ina tunanin abincin da na aiko da safe ya isa ku ci har rana kai da ita dai don cikinku kaɗai, shi ne yanzu za ta tsiro da girki bata san ni duk abin da zai hargitsa lissafin aljihunka ba so nake ba, su ƙawayen biyu ne ko uku, wannan ai tada mai gida tsaye ne ba don ba a hayyacinta take ba wallahi ba za a yi wannan rashin hankalin ba" Ta faɗa tana kumfar baki.

Nasir ya ce

"Su goma sha biyar ne ƙawayen kuma ta ce in taho musu da snacks da drinks kafin a ɗora abinci" Haɓa ta riƙe tana nuna da sake amma babu mai nakasta mata aljihun ɗa fon haka sai ta ce ya je ya tafi za ta yi wa tufkar hanci don sai dai idan ya kawo snacks da drink ɗin kowacce shegiya ta ɗauka ta nufi gidan ubanta amma ba za a zauna a dafa musu abinci ba su masa ƙasa da tattalin abincinsa.

Yana jan motar ita kuma tana shigewa gidan duk ranta a ɓace da a ce ba Meenal ba ce ta yi wannan ɗanyen aiki da sai ta saɓar mata, da sallama ta shigo Sadiya da za ta je ta duba tukunyarta ita ta amsa mata da fara,arta cike da girmamawa wani irin taɓe baki Hajiya ta yi a zuciyarta tana faɗin

'Gulmammiya uwar Æ´an kissa" Ta juya ta kalli Kalifa ta masa magana tana mai É—aga masa hannu ta ce

"Biyoni É—akin Æ´ar gwal sabuwar uwarka ka ga É—aki kamar a turai yarinya ta sha jere iya ganin mutum, duk hassadarsa sai ya yaba ko da a zuciyarsa ne ba a fili ba" Ta faÉ—i hakan ne dama don ta faÉ—awa Sadiya magana Sadiua kuwa bata ce komai ba sai ma ta
ce

"A fito lafiya" Shi dai Kalifa bai bita ba, tun kafin ta shige É—akin take jin hayaniya da shewa irin na Æ´an mata. Da sallama ta shuga amma tsabar surutun da suke basu amsa ba kuma ba wai don basu ji ba suna ji kawai ba za su iya katse hirar da suke ba.

Har ta ƙarasa tsakiyar falon wasu a ƙasa a zaune wasu duk sun baje a kan kujerar wasu suna danna waya, sai wata da taee riƙe da plate tana cin dankalin daga cikin wanda suka ci na wajen Hajiya da ta aiko. Ran Hajiya ne ya ɓaci ita da take son a cancana abinci amma dai waɗannan sun zo za su yi almubazzaranci. Ganin babu wanda ya bata waje ta zauna irin cikin girmammawa a matsawa babba waje ya zauna ko a tashi a bashi wajen, sannan ta lura babu Meenal a falon hakan ya sa cike da nuna gadarar ta ita a dole uwar miji wato mamallakin gidan ta ce

"Wai ku babu manya a gidajenku, ya kuna ganina babu wacce ta mayar da ni mutum kowacce tana sabgar gabanta?" Tamkar tana magana da bango aikuwa ta harzuƙa cike da masifa take faɗin

"Yanzu za ku haɗa ya naku ya naku ku san na yi" Ta faɗa tana dosar bedroom ɗin da take jin wasu suna hanyaniya a inda take jin har da muryar Meenal ƴarta. Daga mai taɓe baki sai masu mata shewa. Tana shiga ta ga su huɗu ne kowacce ta waigo tana kallonta biyu a bakin gado a zaune kasancewar an sauya bedsheet ɗin sai dai babu wanda ya share don a cewar Meenal ma ɗakin bai ci a shere shi ba bashi da wani datti.

Ɗaya tana tsaey gaban madubi tana shafa powder sai Meenal da take tsaye gaban gadon ta dafa kafaɗar ɗaya daga cikinsu suna magana, baki sake suke kallon Hajiya da Meenal ta ƙanƙance idanu saboda tsabar mamakin ganin uwar miji a ɗakinta ba ma falo ba, abun ya mata ciwo amma sai ta danne ta tsaya jin dalili don ta saka a ranta matuƙar tijara Hajiya za ta mata a kan maganar dankali da doya da ƙwai da kayan shayi sai ta yi wa Hajiya tass sai dai koma mai za a yi a yi don babu wani mahluƙi da zai taka mata birki dangane da cin kayan kowane abinci sai ta zaɓa ta darje.

Hajiya ta kalle su a gadarance ta ce

"Ku bamu wuri za mu tattauna da É—iyata"

Da kallo kawai suka bita sai Meenal cike da tsaurin ido na Æ´anmatan zamani ta ce

"Hajiya ni da su duk ɗaya ne ai za ki iya faɗar komai a gabansu waɗanann shaƙiƙan aminai na ne ko baki faɗa a gabansu ba sai na faɗa musu gwara ma ki rage min aiki kin ga in suka ji a kan kunnensu ba sai na maimaita ba" Hajiya kaɗan jakar hannunta ta suɓuce tsabagen mamakin kalaman Meenal amma kuma tuno da cewa ba hayyacinta take ba sai ta ce

"Haba ke kuwa wanna ai sirri ne tsakaninmu" Kafin Meenal ta ce wani abu ƙawarta Safiyya ta ce

"Ƙawata bari mu je waje bani mukullun store ɗin" Meenal ce ta miƙa mata mukullin ta ce

"Yawwa ku auno kayan abincin yadda zai isa, kun ga an jima wasu za su zo sannan da yamma ma ba za a rasa masu zuwa ba bana so abinci ya yanke in kuma za ku shiga kicin sau biyu to" Ta faÉ—a tana Æ´ar dariyar tsokanarsu don ta san ba za su yarda su shiga kicin sau biyu ba sai Safiyya ta
ce

"Kema kin san ba za mu shiga kicin sau biyu ba sai dai mijin naki angonki ya siyowa sauran baƙin da za su zo abinci, amma dai yanzu za mu lodo isasshe wanda kowa zai isa sai a juye sauran a kuloli"

Meenal ta ce

"Kuma za a kai gidanmu kun san akwai baƙin da basu tafi ba kuma ba na son Momi ta yi wahalar bada abinci tun da ina gidan miji kin ga ta huta" Juyawa suka yi suna mata na,am da maganrta Hajiya kuwa tun da suka fara tattunawa ta zama mutuntume, tamkar gunki haka ta koma, ta rasa ma abin faɗa tsabar mamaki wato mukullin store ne a hannun Meenal har take da damar ba ƙawaye su lodo ɗanyen abinci su dafa duk yawan ƙawayen nan a ce wai akwai wasu da za su zo, sannan ma wai har gidan mahaifiyarta za a kai don kar ta sha wahala wato ita nata ɗan ya wahala ya nemo tabbas da sake ko kima da badaƙala don ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, dole ta magance matsalar nan ta hanyar maganin dawo da Meenala hayyacinta ta san abin da take ta dawo mai ladabi da sanin ya kamata kamar yadda ta aurawa ɗanta ita a farko!.
Chapter 60 · 0% Book details