← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 106

Sashe 90

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Saboda ba kayanki ba ne ko, shi ya sa ma kuke nuna bai dame ku ba, na lura kamar ma ni kaɗai abin ya dama ban da lalacewar zamani a ce mace kadarar mijinki ta ƙone amma babu wacce cikin ku ta matse hawaye ko da ba na gaskiya ba ne, a ƙalla a kowacce ko da kukan kissa ne ta yi na ƙarya ai na ɗan ji daɗi amma kowacce fuskarta washe kamar gonar auduga ni kaɗai nake shan kuka da takaicina" Kallon kallo aka shiga tsakanin Mama Talatuwa da Mama Habiba ganin shi tsaninsa da Allah yana so su taya shi kuka a kan kayan abincin da sai ranar da ya ga dama yake ciyar da su, Mama Sa,ade da Mama Bilki kuwa dama tuni suka ba banza ajiyarsa kowacce tana ɗakinta haka ma ƴaƴan.

Mama Talatuwa ta ce

"Malam ko mu yi kuka ko kar mu yi wannan ƙaddarar ba mu isa mu kankar ta ba, kai da Allah ya tseratar da kai da iyalanka babu wanda wutar ta ƙone ai an ci ta varka, baka ga ko gidan jaje aka je ba idan iya dukiya ko amfani wuta ta ci ba har barka ake yi wa mutum saboda ba ƙaramar ni,ima ba ce saboda ubangiji yana iya yin komai amma ya tsayar iya haka wato ya taƙaita"

Yana kallon ta da jajayen idanunsa ya ce

"Barka fa? Kika ce a yi barka to duk wanda ya tako gidan nan ya yi mini barka sai ya cire masa ƙafa" Mama Habiba ta ce

" Kenan baka godewa Allah da wannan abin da ya maka ba, da ka gode masa sai ya dawo maka da abin da ka rasa ta inda baka yi zato b... Kafin ta ƙarasa ya ce

",Rufe mini baki Habiba ai ina ga ma ke ce kika mini baki, da kika zo riƙona in bada abinci a dafa baki da kuɗin da za ki sayi abin da za ki ce wataƙila ma sanadinki ne gobaear ta kama, ni ban san ma wace jarabar ce ta sa nae zaune da ke ba har yau Habiba, to mace ke dai ba haihuwa kike ba sannan kawai dai ni ne nake ciyar da ke don haka kawai ina ga zan hukunta ki...

Mama Talatuwa ta katse shi da sauri da faÉ—in

"Haba Malam kaima ka san wannan dai son zuciya ne kawai ka yarda da ƙaddara saj ka samu sauƙi a zuciyarka, amma wannan zargi ne kake hakan kuma zai saka maka kokwanto a zuciyarka baka yarda da ƙaddarar da Allah ya aiko...

Ƙasa ya dafa ya miƙe tsaye duk da ƙafafunsa karkarwa suke saboda gabaɗaya abin da ya faru ya ruɗa shi.

Da yatsa ya nuna Mama Talatuwa ya ce

"Idan akwai shegen da zai faÉ—a min yadda zan yi a rayuwata sai in gani, don haka ni nake da damar yin abin da na so a lokacib da na so"

Mama Habiba tun maganar da ya faÉ—a ta gorin da ya mata hawaye ya daÉ—e da wanke mata fuska a zuciyarta tana addu,ar Allah ya bata haihuwa watarana, Baba ya kalle ta ya ce

"Habiba ki je na yanke igiya É—aya daga cikin igiyoyin da suke tsakanina da ke" Mama Habiba ta É—ago fuskarta sharkaf da hawaye ta ce

"Tohm Malam ina roƙon Allah ya sa haka ya zama mafi alkairi a garemu" ,Bai tanka mata ba sai Mama Talatuwa da tar rafka salati, ita kuma Mama Bilki da take jiyo abin da suke daga ɗakinta ta leƙo ta tsaya a ƙofar ɗakinta ta kama tsantsa ta ce

",Allah ya yanke miki wahala Habiba, yo ai ke gaba ta kaiki gobarar titi, zaman gidan nan ai jarabawa ne, duk lokacin da Allah ya yanke maka sai ka gode wataƙila gaba ta fi ba ya yawa!" ,

Baba ya ce

",To mai bakin reza, wato ke ishashshiya da mai to ai hausawa sun ce riƙon mahaukaci sai sarki, kuma wallahi kika cika baki kafin ta isa gidansu ke ma kin kama hanyar naku gidan" Baki sake take kallonsa.

Mama Habiba ba ta tanka musu ba ya wuce ɗakinta jiki sanyi ƙalau ranta duk bau daɗi tana tunanin ashe dama shi ya sa ubangiji ba ya son saki duk da abu ne halactacce, saboda gabaɗaya ta ji wani ɗaci a ranta lallai ta tabbata saki ba shi da daɗi.

Kayanta ta haÉ—o a jaka ta fito ta zo ta yi wa matan da yaran gidan da suka fito sallama ta kama hanya ta fita.

Tana fita Baba ya ce

"Yawwa yanzu kuma na ragewa kaina wahala amma dai ba zan gushe ba ina son ɗa namiji ko kan gararre ne sai ranar da na haifi ɗa namiji dole ne ma yanzu in samu budurwa ko sakin wawa in auro" ,Yana faɗar hakan ya ja ƙafafunsa yana yin ɗan kukan takaicin ƙonewar kayan abincin sa. A tsakar gidan kuwa Mama Talatuwa ce kaɗai take cike da jimamin barin gidan da Mama Habiba ta yi sai dai tana fatan ta samu sauyi mafi alkairi tun da ta lura rashin haihuwar ne kaɗai yake saka Baba yake mata yadda ya so.

Washe gati da maƙota suka riƙa shigowa gidan suna jajantawa Baba. Duk magidancin da ya shigo sai Baba ya ce

",Kun ga dai yadda Allah ya jarafceni da ƙonewar kayan abincin, wannan lamari ne da yake buƙatar taimako da tallafin jama,a sannan kamata ya yi mutanen unguwa su yi gangami a yi meeting a sanar a masallaci ake haɗa kuɗin tainakon da za a bani wataƙila kuɗin su zama silar warakata dagaa baƙin talaucin nan" ,Duk wanda Baba ya faɗawa haka sai ya nuna ya yi na,am kuma hakan abu ne mai kyau sai dai babu wanda ya zauna ya ce a yi shawarar haɗa masa kuɗin domin Baba bai san cewa kaf unguwa babu wanda bai san halin da gidansa yake ciki ba, ya manta cewa yanzu kiwo na mutum ake yi ba dabba ba.

Ko da Mama Talatuwa ta kira Sadiya a waya ta sanar da ita abin da yake faruwa ta yi jimami sosai kafin daga bisani ta fawwalawa Allah komai dama ai ta san halin mahaifinsu na rashin wadata iyali wanda bai san hakan cewa ba iyalinsa kaɗai yake tauyewa ba hsr da kansa yake tauyewa domin sai ya sauke nauyin haƙƙinsu ne Allah zai ƙara buɗa masa, sai dai shi ya kasa fahimtar hakan gani yake rashin wadatarwar shi ne zai haɓaka arziƙinsa.

Ko da ta je gidan ta jajanta masa sai da ya ce

"Sadiya kin faɗawa Nasir ɗin na samu gobara komai na kayana abincina ya ƙone? Na kira wayarsa sau biyu bai ɗaga ba kuma bai biyo kiran ba, ai kin ga a matsayinsa na surukina ɗaya ƙwallin ƙwal ya kamata ya kawo ɗan wani abu mana, don na ga jama,ar unguwar nan babu niyya ango ya kwana da wando, tun jiya an gagara kawo ko ƙwayar gero bare a saka ran kawo shinkafa, ni wallahi na ɗauka zuwa yanzu an tara buhun shinkafa ƴar gwammani buhu bakwai a lalace na hatsi biyar dawa huɗu amma har yanzu shiru maƙatau, ko dah taimakon ƴan siyasa zan nema ne?"

Sadiya ta danne takaicin da ta ji ta ce

"Baba wataƙila ko yana kasuwa lokacin da ka kira shi, amma dai maganar kawo tallafi dama ba lallai ba ne tun da yanzu rayuwar ce sai a hankali kowa ta kansa yake...

Hannu ya É—aga mata ya ce

"Ke dalla rufewa mutane baki, ba ta kai ba idan ma ta ƙafa ake ai ba za su rasa amfanin abinci a gidansu ba a lalace ko kwano biyar biyar ce mutum in zai zo jaje sai ya taho da shi, amma don asara sai su taho babu komai kowa haka zai shigo hannu yana dukan cinya su zo su ishi mutane da cewa, ka yi haƙuri malam Bala haka Allah ya ƙaddara Allah mayar da alheri" ,Ya faɗa yana kwaikwayon yadda mutanen suke faɗa in sun zo masa jajan tare da jan wani dogon tsaki yana muzurai. Haƙuri ta shiga bashi ta ɗakko dubu goma ta ba shi, ya karɓa ko godiya bai mata ba bare ya saka albarka, saboda shi yanzu wasu kuɗaɗe masu kauri yake so su faɗo masa.

Kamar zai yi kuka ya ce

"Wllahi shi ma limamin nan na masallacin nan ba shi da tausayi ina ga ma in daina sallah a masallacjn nan in koma wani, mutumin nan yana kallo tun kan ladan ya kira assalatu na fita na je masallacin nan na ringa sallar nafila ina ɗaga hannuwa sama idan na idar ina ta addu,a amma na ɗauka da aka idar da sallar asubar zai yi sanarwa a lasifika cewa a taimaka mini amma shiru maye ya ci shirwa, haka da aka idar da sallar azzahar na kifa kaina da gwiwoyin ƙafata wai duk don a fahimci ina cikin damuwa da halin ƙaƙanika yi amma babu wanda ya bi ta kaina"

Haƙuri dai Sadiya take ta ba shi, bayan ta jo sallamar mutane a zaure ta amsa suka shigo don Baba yana jin sallamar ma ya ƙi amsawa ya rage murya ya ce

"Sadiya da kin ƙyale su, don ba wata tsiyar suka kawo ba in banda zance" Ita dai ba ta amsa ba haka suka shigo Baba kuwa ya haɗe fuska yana muzurai don dakyar yake amsa jajan da ake masa.

Sadiya sai da suka keɓe da Mama Talatuwa take faɗa mata sakin da Baba ya yi wa Mama Habiba, salati ta yi hankali tashe tana jimanta abin, don ita da ta shigo ta ga ɗakin Mmar a rufe ta ɗauka ko unguwa ta tafi cike da damuwa a fuskarta ta ce

"Mama wai su maza haka suke ne?"

Mama ta ce

",Kamar yaya?"

Sadiya ta ce
Chapter 90 · 0% Book details