Sashe 10
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aliya ma duk da haÉ—uwarta da Ibrahim yau hakan ya sauya mata tunani daga auren Kasim amma dai ta san ita ko da a ce mai za a yi ba za ya kasa samun miji na kerewa sa'a ba ko da a ce ana gobe É—aurin aure ne ta tabbata ba za ta yi kwantai ba.
Haka dai aka tattauna kafin daga bisani kowa ya je ya kwanta.
Bayan kwana biyu.
Misalin ƙarfe biyu da minti ashirin na dare ne, alarm ɗin da Jidda ta saita a wayarta ya shiga ruri, cikin bacci ta ji ƙaran da sauri ta tashi ta danne wajen sifikar wayar da ƙarfi kafin ta saka hannu da dakatar da alarm ɗin. Duk da wannan namijin ƙoƙarin da ta yi amma hakan bai hana Aliya tashi daga bacci ba cike da ɓacin rai ta buɗe idanu lokacin har Jiddar ta kunna fitilar wayarta.
Zaune ta tashi tana mutsirtsika idanu, gaban Jidda ne ya faɗi amma bata ce komai ba, wata doguwar hamma Aliya ta saki ko bakin ta bata rufe ba, bata taoron shaiɗanu su shige bakin su samarwa kansu mazauni a bakinta. Cike da bala'i murya ƙasa-ƙasa gudun kar iska ta kai maganar ɗakin Abba, don ta san Abba kamar mai kunenn miciji haka yake wajen jin magana, bare shi ma da ba wani baccin dare ba yake don ta tabbatar yanzu da za a je ɗakinsa ko rantsuwa ta yi ba za ta yi kaffara a kan sallaya za a same shi ko dai yana sallah ko kuma yana karatun qur'ani.
Tana mata wani kallo ta ce
"Jidda wai mene ne hakan? Sau nawa zan ce miki ki dajna saka wannan ƙaran alarm ɗin yana katse mini bacci da mafarkai masu daɗi, ni wallahi ban taɓa jin wannan al'amari ba a zo gidan mutane a hana su sakat da sakewa ake damunsu da shiga haƙƙinsu" Ta faɗa cike da wulaƙanci tana wani kauda kai gefe, ruwa ne ya taru a kwarmin idanun Jidda ta tsaya tana ƙarewa ƙeyar Aloya kallo da yake ta juyar da kai gefe irin na wukaƙanci. Murya a dishashe ta shiga faɗin.
"Aliya ni kike yi wa gorin gida?" Kamar an wanda Aliyar take jiran tambayar ta ce
"To in fitsari banza ne kaza ma ta yi mana" Furta furucin wannan ya yi daidai da gangarowa maƙalallun hawayen da suke cikin idanun Jidda, cike da jin babu daɗi a ranta ta ce
"Aliya wai kam ko kin manta Jiddanki? Ni ce fa Jidda wannan ƙawar taki tun ta yarinta, ni ce fa wacce kike so da tsananin ƙauna, ni ce wacce muke wasa bacci kawai yake rabamu, ni ce fa za mu wuni tare amma idan za mu rabu da kuka ake rabamu saboda shaƙuwa da ƙauna. Amma Aliya yanzu saboda iyayensa sun kwanta dama ƙasa ta rufe idanunsu shi ne kike min wasu abubuwa wanda ban taɓa zato da tunanina ba, shin ko kin daina so na ne? Muna rayuwa tamkar ƴan biyu babu mai shiga tsakaninmu muna son junanmu amma lamuran duk sun taɓarɓare sun jagule shin ina matsalar take?"
Duk wannan jawabi da kalami da Jidda ta yi ta vayan kunnen Aliya ya wuce don ko gizau bata yi ba, bare Jidda ta saka ran cewa kalamanta za su yi tasiri a zuciyar Aliya, don ta lura Aliya ta sauya gabaɗaya, zuciyarta ma tamkar wanda ta ƙeƙashe daga tausayi da jin ƙai!.
Yatsina fuska ta yi ta ce
"Yankan uwa ai ya ishi É—an tayi ishara, ke yanzu kina zaman jiran sai na furta miki kowace kalma da bakina, hankali da tunaninki basu isa su baki amssoshin tambayarki ba?"
Hawayen idanunta sun fara gudu tamkar an kunna famfo, tana jin yadda ruwan hawaye yake gangatowa har ta saman hancin ta, a gefw É—aya yana gangara har wuyanta.
Cike da alhini da damuwa haÉ—e da sanyin murya ta ce
" Au haka ne?"
Aliya ta ce
"Tabbas ya kamata ki fahimci RUWA CIKIN COKALI ya ishi mai hankali wanka" Tana faÉ—ar hakan ta juya baya ta kwanta abin ta.
Jikin Jidda sanyi ƙlaw ta juya za ta fita dama alwala za ta yi domin gabatar da sallar nafila, har ta je bakin ƙofar za ta fita ta tsinkayi muryar Aliya tana faɗin.
"Ba za ki gane ba Jidda tabbas babu ƙarya na ƙauna ce ki kuma tamkar ƴar uwa na ɗauke ki, sai dai ba zan ɓoye miki tun daga lokacin da muke zuwa makaranta tare sai kowa yake son ki ni ko oho, idan kika yi fashin rashin zuwa makaranta ko na kwana ɗaya baki da lafiya daga malamai har ɗalibai tambayar ki suke, idan na yi fashi ko shekara zan yi babu mai nemana daga islamiya har boko. Tsananin ƙoƙarin ki da farin jini ya sa Abba ma kika ciri tuta a wajensa, tun daga wannan lokacin matsayin ki a zuciyata ya ragu sannan uwa uba da muka isa munzalin ƴanmatacin samari suka miki caaa duk da kyau da diri da nake da shi na tsarin halittar ƴa mace wacce za ta ja hankalin duk wani cikakken namiji mai lafiya a jika amma sai ya zamana kowa ke yake kallo, duk inda muka taka sai dai samari su biyo mu gida idan kuwa suka zo kowa ya aiko yaro sai dai a ce ana yi wa Jidda magana!Tun daga wannan lokacin na fara kallon kyauna a matsayin muni tun da ga shi dai ana faɗin farar mace alkyabba ta mata amma ni nawa fari da kyan ya zama tamkat shuɗaɗaɗn lokacin"
Tun da ta fara magana bakin Jidda yake a buɗe ta rasa abin da za ta ce kanta gabaɗaya ya kulle tana tunanin shin dama wannn ne ummul aba,isin rabuwar kawunansu da Aliya, to ita ta ce samarin su zo nemanta ita da vata ma kula su hatta maganar malamai da ɗalibai ba ni na ce so ƙaunace ni ba ashe shi ya sa ko da muka fara karatun N.C E bata son kowa ya raɓe ni kenan hassada Aliya take min? Ta shiga jerawa kanta tambaya w zuciyarta, bata da amsar da Aliya domin tana ma tunanin lokacin sallar ta yana wucewa a banza ita kuma a rayuwa tana son ribatar lokacin ta kafin mutuwarta ta riske ta.
Ko da ta fita ta yi alwala ta dawo Aliya ta juya tana bacci bata sake cewa komai ba, sallah ta yi raka ',a huɗu ta zauna ta ringa jerowa iyayen ta addu'a domin ta san tsakanin ɗa da iyayen da suka riga gidan gaskiya babu abin da suke buƙata sai addu'a. Bayan ta gama musu ta yi wa kanta da Abba, ta yi wa Umma da Aliya tare da yi wa dukkan sauran musulmi.
Sai da ta yi sallar asuba ta yi karatun qur'ani sannan da gari ya yi haske ta koma ta kwanta bacci ya yi awon gaba da ita.
Bayan faruwar haka da kwana biyu, Aliya ta shiga wasi-wasi a kan tunanin Ibrahim da yake yawan addabar zuciyarta, sai dai ta yi sawun zuwan kamfanin da ta ga sun je an buÉ—e sun shige da motarsu amma ko barin ta ta shiga mai gadin ba ya yi, sai dai ta saka a ranta idan kere yana yawo zabo yana yawo watarana za a haÉ—u.
Ta ci gaba da riƙe Kasim ɗinta tana lallaɓawa tare da jiran gawon shanu na zuwan Ibrahim domin idan ta samu Ibrahim dole Kasim ya kama gabansa a cewar ta, shi kuma Kasim saboda ƙaunar da yake mata koyaushe sai hidima da kashe mata ɗan kuɗin da yake samu yake.
Rayuwa tana ta tafiya, yau fari gobe baƙi dama haka rayuwa take a wajen kowa ta kowane ɓangare, bijirowa da fitar da abokin rayuwa da Abba ya yi wa Aliya da Jidda shi ne abin da ya saka Jidda a wani hali, domin ta san bata da kowa, ita yanzu ko wuni za ta yi tana yawo ta dawo gida babu mai tsayar da ita bare a biyo ta gida, gashi dai ta san Abba bai san cewa bata da manemi ba, tun da shi yana wuni a kasuwa sannan ya san dai da Jidda akwai manema bai san cewa yanzu kiɗa da rawa sun sauya gabaɗaya ba. Ta shiga damuwa musamman yanzu da Umma ta sako ta a gaba da rashin manemi kuma mashini tana faɗa mata cewa sai dai a bada ita sadaka tun da baƙin jinin ta ya saka bata da manemi, duk da ita Jidda ta san Allah ne yake bayarwa kuma aure lokaci ne kamar haɓo yake idan ya zo sai an yi. Gorance gorancen da Umma take mata ya sa ko zaman gidan fita yake a ranta bare yanzu da sun kammala karatu sai islamiya Jiddan take zuwa Aliya dama ta yi bankwana da zuwa islamiya saboda ta ga Abba ba zaman gida yake ba ita kuma Umma bata takura msta wai ai ta iya karatun sallah, bata san cewa uwa ita ce makarantar farko ta ɗanta ba, ilimi ya zama dole ga kowa kuma wajibi ga mace domin ita ce makarantar farko ta ƴaƴanta da ma al'umma baki ɗaya.
Kamar kullum yau ma sa da ta gama aikin gidan tsaf ta yi wanka ta saka kaya tare da ɗora hijabin makarantar ta, fitowa ta yi tana riƙe da jakar islamiya, Umma da Aliya suna zaune suna tattunawa, sallama ta musu babu wanda ya kula ta, juyawa ta yi ta fita daga gidan, a zuciyarta tana tuno lokacin tata mahaifiyar tana raye yadda take ta mata addu'a da fatan alkairi idan za ta tafi makaranta amma yanzu saboda bata raye in har ba Abba ba ne to babu wani mahluƙi da yake mata addu'a ita damuwarta ma guda ɗaya ce da aba a san inda wani daga cikin danginta yake ba, tun daga kan dangin uwa kama zuwa dangin uba.
Tana ta zancen zuci ta nufi makarantar ta shiga aji lokacin har an fara É—orin karatun hadisi, kusa da aawarta Salama ta zauna ta fito da nata littafin suka ci gaba da sauraron malam.
A can gida kuwa Jidda tana fita Umma ta taɓe baki ta ce