Sashe 68
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun sauka a motar suka shiga napep kowa daban ta shiga tun da Amatullah gidansu za ta tafi ita kuma gidan Jidda. A ƙofar gidan Jidda napep ya sauketa ta fito ta bashi kuɗin tana lissafin sauran kuɗin nata ya kusa ƙarewa gashi bata san ma da mai za ta biya bokanya kuɗin aikin ba, duk da bata san nawa ne kuɗin ba sai dai ta san za ta yi ƙaryar da za ta yi ta ɓanɓari kuɗin aikin a jikin Jidda tun da ita ita ce mai kuɗi ita kuma Allah ya tauye mata nata samun sannan shi ma mijin fuƙara,u ne. Tana tsaye gaban tangamemen get ɗin tana ƙarewa gidan kallo ranta tana ƙuna tana ƙiyasto ranar da za ta tare a cikin gidan.
Ƙaran sohuwar wayarta ne ya dawo da ita daga tunanin ganin sunan Kasim ta doka wani uban tsaki, a zuciyarta tana faɗin
'ÆŠan anace uban shegen naci ko mai zai bani zai kafa mini kira' Ta faÉ—a sai dai kiran yana dab da tsinkewa ta É—aga tana karawa a kunnenta ta ji hucin iskar sa ya busa yana faÉ—in
"Aliyata sarauniyata" Wani É—aci ta ji a zuciyarta tana galla masa harara tamkar yana ganinta, sai kuma kamar an mata dole ta ce
"Uhmmm" Ya ce
"Fatan kina cikin ƙoshin lafiya, baki koma gidan ba?" Ya tambaya yana sararon amsar ta. Ɗan jim ta yi sai kuma ta ce
"Eh dama ai ban jima da fita ba kuma Amatullahi ce ta ɓata mana lokaci yanzu ma ko asibitin bamu ƙarasa ba" Fatan alkairi ya mata yana faɗa mata yadda ya yi kewarta baki ta taɓe a zuciyarta tana raya shi aka bari da yawo da zance don ita yanzu tana nan tana yaƙin yadda za ta samarwa kanta kyakkyawar rayuwa.
Ƙaramar ƙofar get ɗin ta tura amma sai ta ji a rufe gam hakan ya sa ta yi nocking. Mai gadi da yake zaune kan benci yana ɗann gyangyaɗi ya taso ya buɗe mata tun da lokacin ƙarfe ɗaya saura. Yana ganinta amma bai bata hanya ba sai ya tare ta da tambayar
"Baiwar Allah wa kike nema?" Maimakon Aloya ta bashi amsa sa ta shiga ƙarewa kanta kallo tana duba ko akwai wani waje da ya gani wanda ta yi kama da mai neman taimako da har zai jefe ta da wannn tambayar cike da gadara ta ce
"Matsa min in wuce ko ka ɗauka irin mutanen da suke neman taimako ne ai ban maka kama da mai allazi ahidin ba " Ta faɗa tana neman bangaje shi ya ƙara tare ƙofar yana cewa shi a kan aikinsa yake, nan ta shiga ɗaga murya tana faɗin gidan ƴar uwarta ne, shi dai bai kulata ba ya fito da waya a aljihunsa ya kira Jidda yana faɗin
,"Hajiya akwai wata baƙuwa a waje tana cewa sai ta shigo kina da baƙuwa ne Ta ce ƴar uwarki ce?" Jidda da take kicin ta ɗan yi jim sai ta ce
"A,a amma ka barta ta shigo" Cike da girmamawa ya amsa.
Matsa mata ya yi ta wuce tana faman faɗin da bai matsa ta shiga ba da sai ya rasa aikinsa. Nocking ƙofar ta yi jim kaɗan Saude mai tayata aiki ta zo ta buɗe dama tare suke da Jidda a kicin tana taya ta aiki. Buɗe mata ƙofar ta yi tana mata sannu da zuwa Aliya ko amsawa bata yi ba ta ce ta wuce cikin babban falon inda tana shiga wani ƙamshi mai daɗin gaske ya baibaye mata hanci, fitowar JIdda ta hango Aliya a tsakiyar dalon da sauri ta ƙaraso fuska cike da fara,a bakinta ya ƙi rufuwa. Aliya kuma ganin Jidda ta yi ƴar ƙiba ta murmure ga wani kyau da fatar ta ta yi tamkat wacce take rayuwa a ƙasar waje wani tuƙuƙin baƙin ciki ya cika mata ciki tana tunanin da yanzu ita ce a wannan daular ita ce ta yi kumari ta warware.
Danne abin da ya É—arsar mata a zuciya ta yi domin ta san wannan damar tana dab da zuwa gare ta ta kusa ta shuga tsakanin ma,auratan biyu wato ta zo ta kafa tata fadar a birnin zuciyar Ibrahim ba tare da wani ta kawo mata cikas ba.
'Oyoyo Aliya shi ne ma ko sanarwa " Ta faɗa tana ƙarasowa suka zauna a kujera a tare Aliya sai yaƙe take, don ita zuciyarta cike take da yadda za ta ɗauki cokali.
Tana Æ´ar dariya ta ce
"Yanzu don zan zo ganin ƴar uwata jinina sai na sanar da ita? Ai dama na ce bari na zo tun da ke har yanzu kin gagara zuwa na ce wataƙila ku masu kuɗi bakwa ziyartar gidan talakawa" Jidda tana mata ƴar hararar wasa ta ce
"Haba dai wannan wace irin magana ce dama ranar juma,ar nan nake cewa zan je gida in gaishe su sai na ratsa gidanki, daga nan sai na je gidansu Ibrahim na gaishe da ita" Ta faÉ—a tana kallonta.
Nan suka shiga ƴar hira Jidda tana jin kamar ta goya ta saboda daɗin sa ta ji. Saude ce ta zo da sallama tana ɗauke da plate wanda yake ɗauki da lemon roba guda biyu da ruwan roba guda ɗaya masu sanyi, sai kofi ta zo ta durƙusa ta ajiye a gabanta tana ƙara gaishe ta amsawa ta yi hankalinta a kan Jidda tana ta ƙare mata kallo kamar dai ba wannan Jiddar wulaƙantacciya ba a wajensu amma yanzu gashi ta samu ƴanci, ƴancin ma mai lasisi.
Lemon ta tsiyaya mata ta miƙa mata da hannu biyu kafin ta tashi ta bar wajen, Jidda ta ce
"Saude ki goge kan cooker gas ɗin idan wajen ya huce sannan ki kwaso kwanukan ki jera a kan dining" ,Cike da ladabi ta amsa ran Aliya yana ƙuna wai yau Jidda ce da mai aiki bayan a gida ita ce baiwar gidansu lallai wannan bahaushe yake kira rana ɗaya Allah kan yi bature.
Suna hira inda Jidda take tambayar Kasim wani ɓacin rai ne ya zicyarci zuciyarta ita ba don larura ba ta tsani a kira sunan Kasim ma. Ita ma ta daure ta tambaye ta Ibrahim kafin ra bata amsa wayar Jiddar da take kan ɗaya daga cikin kujerun ta shiga ringing, tashi ta yi ta tafi za ta ɗauko gabaɗaya idanun Aliya a kanta tana ganin yadda doguwar rigar rantsatstsan leshin ta kamata daga baya tamkar dama a jikinta aka yi ɗinkin tana murmushi ta amsa wayar, Aliya tana jin yanayin yadda suke wayar cike da kulawa ta gane da Ibrahim take magana. Sai bayan sun kammala wayar ta ce
"Kin ganshi ma É—an halak shi ne ya kira ai yana office" ÆŠan runtse idanu Aliya ta yi ta buÉ—e tana tunanin yanzu shi yana can a office cikin AC ita kuma nata mijin yana can cikin rana a kasuwa yana fafutuka.
Sun jima suna ɗan taɓa hira ita dai Saude ta koma ɓangaren su na ƴan aiki inda suke tare da wata dattijuwa kakarta mai suna Baba kuluwa. Kiran sallah ya sa Jidda ta ce su je su yi sallah, bedroom ɗin da aka ajiye ta ranar da aka kawo ta suka shiga Aliya ta shiga banɗaki ita kuma ta fito ta hau sama jim kaɗan ta dawo ta tarae tana sallah ita ma alwalar ta yi ta zo ya kabbara tata sallar. Bayan ta idar suka fito falo ta kawo musu abinci suna cikin ci Ibrahim da ya taho daga office yau da wuri kasancewar kansa yana ciwo bai faɗa mata ba sai ya taho don baya so ta tada hankalinta.
Da sallama ya shigo gaban Aliya y buga da ƙarfi Jidda kuma ganinsa yanzu ya sa ta gane akwai damuwa musamman da ta kalli yanayinsa, cokalin hannunta ta ajiye ta miƙe tsam Aliya kuma ta gaishe da shi fuska babu walwala ya amsa kawai sai take ganin kamar dai ya gane ita ce take kiransa ko kuma ya san ƙudurinta, da sanyin jiki Jidda ta nufe shi yana kallon yadda yanayinta ya sauya da idanunta ta shiga isar da saƙon tambayar dawowarsa a wannan lokacin amma maimakon ya furta mata komai sai kawai ya langaɓar da kai gefe yana lumshe kyawawan idanunsa da suka ɗan kaɗa suka ja tana ƙarasowa sai ta karɓa jakarsa ta office ɗin amma shi ba wannn tallafin ya fi buƙata ba ya fi son jin fatar jikinta a jikinsa ko ya ji sassauci don ya yi ammana Jidda wani tsagi ce na jikinsa yana ji a jikinsa tabbas idan babu Jidda ba zai rayuwa ba ko da ya rayun zai yi rayuwa ne irin ta akwai ruhi amma gangar jiki kamar gawa!.
Hannunsa ya kai ya rungumota jikinsa yana sakin ajiyar zuciya, hannunta ta saƙala a bayansa suka shiga takawa a hankali don ita tuni har yanayinta ya sauya ta fara jinta tamkar marar lafiya, ita da take ji ana cewa idan ɗa bashi da lafiya mahaifiyarsa tana jin jikinta tamkar marar lafiyar wani lokacin ma tare ake yin jinyar da uwa da ɗan ashe dai gaske ne tun da gashi ita ma da yae mijinta har ta ji nata jikin ya amsa.
Aliya kuma sai suka zame mata TV don sai ta zama tamkar mutuntumi a wajen tamkar dai ma basu san da ita a wajen ba, suna riƙe da juna suka fara haurawa sama, Aliya ta kafe su da idanu, har suka ɓacewa ganinta, wani haushi ya cika mata zuciya tana tunanin da yanzu ita ce wannan kyakkyawan yake gwadawa wannan soyayyar wannan a gaban mutane ma yana yi wa matarsa haka ina ga in suka keɓe a ɗaki ɗaya ta san ai sai dai a kira matarsa ƴar gata, don a haka ta fahimci tsantsar kulawa ce da soyayya.
Da nannuyar ajiyer zuciyar da ta sauke ta dawo hayyyacinta tana sakin wami tsaki a fili, duk da daÉ—in abincin da take ci a take ta ji ya zame mata maÉ—aci a fili ta furta