Sashe 30
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau ya kama asabar wanda ya yi daidai da kwana uku tana fama da zazzaɓi mai zafi, sannan ko naira biyar bata da ita shi kuma ya ƙi siya mata magani bare a yi maganar zuwa asibiti, sai dai ta ji su Baba suna batun ta basu kuɗin bayan ita ko naira biyar ba ya bata. Gashi ita har gajiya take da faɗawa ƙawarta Noor buƙatunta abin da kunya kullum ka ce a baka. Kwance take ta kasa tashi tun da ta yi sallar asuba shi ma a zaune ta yi, zafin zazzaɓin da ya dira mata har cikin ta rasa ya za ta yi, Kalifa yana kwance a gefe yana bacci. Nasir ne ya fito daga bedroom ɗin kasancewar a falo suke, cikij shirinsa na fita sai buɗaɗa ƙamshi yake yana mata wani kallon rashin mutunci ya ce
"Ni wallahi Sadiya ban san irinki ba a ce mutum bashi da aiki sai jinya, mace kullum tana bin katifa tana kwanciya haba" Idanunta da suke mata wani raɗaɗi tsabar zafin zazzaɓin ta ɗaga ta kalle shi ta ce
"To ya bawa zai yi da abin da ubangiji ya jarafce shi da shi" Wani kallon ƙasan ido ya mata ya ce
"Ke dai ce mai yawan jinya ai abin a jikin ki yake, yanzu dai yau kwana biyu kenan ina fita ina sayen abincin titi" Muryarta wacce bata fita sosai ta ce
"Amma Abban Kalifa ka san dai duk runtsi ina yin girki tun da ka ga haka abin ne ya ci tura!. " Wani tsaki ya yi ya ce
"Ragwanta dai" Yana faɗar hakan ya kaɗa kansa zai fita yana gyara zaman hularsa, yunƙurawa ta yi ta tashi zaune dakyar yana dab da fita daga ɗakin ta ce
"Dan girman Allah ka siya min magani, wallahi ina jin jiki" Kamar ba zai juyo ba sai ya juyo ya ce
"Aikin kenan ke kullum kamar asibiti baki da aiki sai ta,ammali da magani kamar wata Æ´ar shaye-shaye" Ta ji haushin maganar amma sai ta danne tana rayawa a ranta wataran sai labari, waya ya É—aga yana magana ya saka takalminsa ya fita.
Yana fita ya hangi wani al,amajiri a ƙofar wani gida yana bara kiransa ya yi da ya zo ya ce
"Gani"
Nasir ya ce
"Kai É—an malam ka san majamfari" Shiru yaron ya yi yana tunani sai Nasir ya ce
"Wani ganye da ake dafawa sai a saka zani a rufa da zafib ruwan ganyen" Da sauri yaron ya ce
"Na sanshi, mu ma malaminmu yana sawa mu cirowa matansa idan za a dafawa yaransa in suna zazzaɓi, ai har kwaɗonsa ana yi a ci in ana zazzaɓi"
Nasir ya ce
"Dakyau" Waje ya nema ya zauna ya ce yaron ya ajiye kwanonsa ya je ya ciro masa, da yake daga can gaba da su akwai wani gida bayan gidan kuma akwai gona amma sai an yi tafiya amma ba wani sosai ba kasancewar a kusan ƙarshen gari suke.
Zuwa can sai ga yaro ya taho hannunsa cike da ganyen nan ya ciro su, yana kawowa Nasir ya karɓa ya bashi naira hamsin almajirin yana ta murna ya karɓa ya tafi.
Yana kwasowa ya shigo gidan, Sadiya da ta ɗauka tafiya ta yi ta ji ya turo ƙofa sai gashi ya shigo ko sallama babu, labulen ya ɗaga ya ce
"Sai ki fito ki dafa ki rufa da zani ki É—auki ganyen ki yi kwaÉ—o ki ci" Baki sake take kallonsa yadda aka libgo ganyen kamar za ta yi kuka ta ce
"Mene ne wannan Abban Kalifa" Kallon kin raina min hankali ya mata ya ce
"Kar ki mayar da ni É—an iska mana majanfarin ne za ki ce baki sani ba?" Cikin sanyin murya ta ce
"Na sani" Ya ce
" To tun da ke baki da aiki sai jinya gashi nan naira hamsin ɗina ta biya min buƙata, idan kin ji kin ware sai ki ɗora abinci" Yana gama faɗa ya ajiye mata a ƙofar ɗaki ya juya sai ƙaran rufowar ƙofar gidan ta ji, tagumi ta buga tana tunanin ita dai ta san ana tafasawa a rufa da zani zafin ya bugi mutum amma bata taɓa jin ana ci ba.
Haka ta lallaɓa ta dafa ta rufa, cikin ikon Allah sai zazzaɓin ya sauka, sai rashin ƙarfin jiki, haka ta gyara gidan ta wanki Kalifa ita ma ta yj wankan ta ɗora girki. Da yamma sai ga Noor ta zo duba ta, suna hira sai ga Mama ita ma ta zo, bayan tafiyar Noor Mama ta yi ta yabawa Nasir a kan hidimar da yake yi da su, ita dai sai dai ta ce
"Allah ya biya shi"
Da dare tana zaune tana cin tuwon da ta dafa ba don tana jin daÉ—in bakinta ba sai don kar ta zauna da yunwa, Kalifa ya yi bacci da wuri tun ana magriba.
Nasir da ya zo kamar abin arziƙi ya zauna ya gama ƙare mata kallo ya ce
"Sadiya ina da magana da ke" Dakatawa ta yi da cin tuwon tana kallonsa ta ce
"Ina ji" Ya ce
"Sadiya ya kamata ki kama sana'a zamanki haka ba zai iyu ba, a ce ke komai sai dai a É—auki É—awainiyarki ke babu abin da za ki taimakawa mutum da shi" Tana masa kallon rashin fahimta ta ce.
"To taimakon kuma na mene ne, sannan ai sana,a sai ana da jari... Tun kafin ta kai ƙarshen maganar ya katse ta da faɗin
"Ba dole ba ko an faɗa miki mace bata taimakawa a cikin gidan, zamanki haka ba zai iyu ba sana,a ita ce mutuncinki dole ki kama sana,a domin ɗaukan ɗawainiyar kanki ni ma har kya taimaka min da buƙatub cikin gidan, a wannn zamanin macen da bata sana,a bata da daraja in ma baki sani ba ki sani, mace idan tana kama kuɗi ta fi daraja a idanun miji in mace bata da sana,a namiji gabansa har faɗuwa yake idan ya ga ta buɗe baki sai ya yi zaton buƙata za ta tambaya" Idanu ta ɗago tana binsa da kallon mamaki ta fara fahimtar nan gaba ɗawainiyar kanta ma ita za take ɗauka tun da gashi tun ba a je ko ina ba har ya fara gajiyawa da wasu abubuwan duk da dama wani haƙƙin yana tauyewa ne.
Tana kallonsa ta ce
"Amma ni da ba zaman kaina nake yi ba zaman aure nake sai in ke ɗaukar ɗawainiyar kaina" Sheƙeƙe ya kalleta ya ce
"To Sadiya kar ki nemi sana'a ki zauna a haka" Yana gama faɗar hakan ya tashi ya nufi ɗaki da kallo ta bi bayanshi har ya ƙulewa ganinta, wani uban tagumi ta doka tana tunanin mafita, ita dama tana son sana'a sai dai rashin jari, ba ma wannan ba ita tun da ta yi auren nan tsawon shekara uku bata da wata nutsuwa sai dai damuwa.
Ko da ta shiga ta kwanta haka ya zo mata da buƙatarsa, babu yadda ta iya ta sauke nauyin haƙƙin duk da bata da wani ƙwarin jikinta sai dai tana tsoron kwanciya da nauyinsa sannan tana fargabar mala'iku su kwana suna tsine mata idan ta bijirewa umarninsa.
Washe gari da safe ta gama ɗumama tuwon ta zuba ta kawo masa har ta zubawa Kalifa ma, tana zaune ta yi shiru tunani ya yi awon gaba da ita ƙamshin miyar ne ya daki hancinta tana shaƙa kawai sai ta ji zuciyarta ta tashi, wani amai ta ji yana yunƙuro mata amma saboda ƙarfin hali take ƙoƙarin mayar da shi sai dai hautsinawar da cikinta ya yi shi ya sa babu shiri ta yi waje a gudu-gudu domin jin aman bashi da niyyar dakatawa.Tun da ta je bakin makwaranya take sheƙa amai kamar za ta amayar da ƴaƴan hanjinta, Kalifa ne jin ƙaran ƙololon aman tashi ya fito ya zo ya tsaya yana kallonta, har ta gama ta gyara wajen bayan ta wanke baki da fuskarta, duk sai ta ji jikinta ya mata nauyi hannun Kalifa ta kamo yana cewa
"Momma amai" Amsa ta bashi kawai, suna shigowa falon ta ga Nasir ya dakata da cin abincin da yake tana shigowa ya zuba mata idanu tamkar yau ya fara ganinta, ba ma wannan ba yadda yake mata wani irin kallon tuhuma shi ne abin da ya É—aga mata hankali duk ta ji ta tsargu, duk da bata gama gane inda kallon nasa ya dosa ba.
Saurin kawar da kanta ta yi ta nufi inda ta tashi ta zauna, tana cewa Kalifa ya zauna ya ci gaba da cin tuwon. Kamar daga sama ta ji Nasir ya ce
"Kin san dai ba na son amai, a kan mai ina cin abinci za ki wani ƙwaƙulo amai kawai ki sa duk abincin ya fita daga raina, ai sai ki zo ki ɗauke tun da burinki ya cika na daina ci sai ki ajiye kw kya ci anjima" Danne abin da ta ji ya yunƙuro mata na takaici ta yi, ta tashi ta ɗauke ta fita ta kai kicin ta dawo, tana shigowa ya ci gaba da mata kallon ƙwaƙwaf sai da ya bari ta zauna ta ji ya jefo mata wata tambaya da ta saka ta tafi wata duniyar tunanin da bata yi shi ba, ya ce
"Wai aman mene ne kike yi Sadiya, kar dai ki ci min ciki ne da ke?" Wannan tambayar da ya mata ta sanya ta luluƙa duniyar tunani da zargin kanta, na farko tabbas wannan watan bata yi al'ada ba (priod) Sannan ta lura ma sai take ta jin kasala sannan kuma daga ta ci abu ma sai ta ji babu maganar da ya yi ce ta katse mata tunani ya ce
"Magana nake miki Sadiya" A tsorace ta ce
"Ni bani da wani ciki" Wani kallon ƙurilla ya mata ya ce
"Ai dama kar ma ki fara don ni ba na son haihuwa a kai a kai, yaro shekara biyu a masa wani ƙani, ai haihuwa ma kamar mage bashi da wani alfanu shi ya sa ake son tsarin iyali" Kallonsa kawai take bata ce komai ba, har ya tashi ya haɗa kan wayoyinsa ya ajiye ya je ya sake wanke bakinsa saboda tuwon da ya ci ya ɗauki abubuwansa ya juya zai fita ta ce