Sashe 45
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ɓangaren Baba tun da ya yi turus ganin babu motar Nasir sai abubuwa da dama suka shiga masa gizo a ƙwaƙwalwa ya shiga saƙa da warwara sai dai idan zuciyarsa ta kissima masa abu marar kyau dangane da kawo Sadiya gida da Nasir ya yi sai ya yi saurin kawar da hakan, yana ƙara faɗawa kansa cewa ba da wata manufa Nasir ɗin ya kawo ta ba, tun da idan ya tuna fuskar Sadiya ai ya ga babu wata damuwa ko alamar ɓacin rai sannan ya ga Sadiyar ta murmure ta yi kyau abin ta babu wata rama ko yanayin da ya saba ganinta a can baya, ya ƙara haɗa hakan da cewa Nasir ne yake vata kulawa bai san cewa ita ce ta samarwa kanta mafita ba da taimakon Kaka, duk da ya san da maganar amma dai bai san sana,a ce mafarin komai ba, sana,a ce ta kaita ga wannan ɓigirin na walwala da mirmurewa don ta wuce jira a bata da kanta take yi wa kanta abubuwa babu ruwanta da jiran a bata bare a wulaƙantata, tun da wasu mazan masu son abin hannunsu wanda basa ɓanɓaruwa basa son sauke nauyin iyali wansa ya rataya a wuyansu suna yin hakan ne don sun gaji da bani- bami na mace koyaushe a ce ana buƙatar wani abu daga gare su amma in kina sana,a za ki ga sauyi domin ke kanki sai kin san akwai bambanci da ka ɗauki abinka da kuma bambanci da a baka.
Ba a taru an zama ɗaya ba amma dai Allah shi kaɗai ne ba ya gajiya da a roƙe shi.
Baba ya jima yana ɗan kaiwa da komowa gani yake kamar sai Nasir ɗin wani waje ya je ya dawo, har sai da ya kama hanya zai koma cikin gidan sai dai jin liman ya yi kabbarar harama sai ya nufi masallacin yana bazama riga kamar zai tashi sama, botocin da ya gani da ruwa ya ɗauki ɗaya ya yi alwala da sauri, saboda dama bai ƙarasa alwalar da yake yi a gidan ba, da ya ji Nasir ya zo ya fita. cikin masallacin ya shiga sa,arsa ɗaya liman ya ja doguwar sura shi ya sa ba a wuce shi ba. Tun da ya yi kabbarar shi dai gashi nan ne yana sallah amma dai sheɗan ya yi wa tunaninsa linzami don kawai bai ankara ba sai ya ji ya tafi tunani, kuma tunanin ba a kan komai ba sai a kan kawo Sadiya gida da Nasir ya yi. Tun da aka kai sujadar ƙarshen Baba ya daddage yana addu,a yana cewa
"Allah ka sa Nasir ba da wata manufa ya kawo yarinyar nan gida ba, Allah ka taimake ni kar ya ƙara min wahala a kan wacce nake sha ta riƙon ƴaƴan nan Allah ka dube ni ka bani ɗa namiji wanda zai tallafa mini ya ɗauki ɗawainiyata" Har aka kusa yin sallama bai ɗago ba sai can ya ɗago ya fara tahiya. Ko da aka idar babu wani azkar da ya yi shi ne na farkon tashi tsaye a masallacin, tamkar dama jira yake a idar shi ya fara fitowa daga masallacin idanunsa a ƙofar gidansa amma babu alamar motar Nasir don a tunaninsa ko zai dawo. Tsabar ya saka abin a ransa takalmin ma a juye ya saka yana jin wani maƙocinsa yana masa magana wanda ya fito daga masallacin amma bai waiwaya ba bare ya amsa don shi gani yake yana cikin gagarumin tashin hankali na rashin sanin matsaya kuma takamaiman maganar zuwan Sadiya.
Yana shiga gidan ya fara ƙwalawa Sadiya kira tamkar zai fasa gidan, bai ma damu da sauran wasu ƴan matan da basa gidan ba, don shi dama tarbuyar ba damunsa ta yi ba shi dai damuwarsa ya aurar da su ya huta kuma bai damu da nagartar miji ba sannan ko da mai zuwa wajen ƴaƴan ne bai damu ya ga wani nutsatstse ko wanda ya san mai yake ba babu ruwansa da nakasun mutum.
Sadiya wacce Mama Habiba ta kawowa tuwon ta da aka kasa aka bata ta tsoma hannunta kenan ta ɗauki loma za ta kai baki Baba ya ƙwala mata kiran da ya sa ta ji wata irin faɗuwar gaba, da sauri ta mayar da tuwon hannun nata ta miƙe tsaye tana amsawa amma bai daina kiran ba ita gabaɗaya ma ya tada mata hankali ba ita kaɗai ba hatta Mama Habiba tsaye ta miƙe tana zulumin anya lafiya? Mama Talatuwa ma mahaifiyar Sadiya gabanta ne ya faɗi dama tana ta tunanin inda Sumy ta tafi har yanzu babu ko da ƙurarta kuma yanzu bayan Sadiya ta sanar da ita da Nasir suka zo amma ta san kowa ya ji yanayin kiran da Baba yake mata to ba na lafiya ba ne, don duk wanda ya san Baba to ya san wannan muryar tasa ta ɓacin rai ce.
Mama Talatu a zuciyarta ta ce
'Ko dai wani laifin Sadiya ta yi Nasir ɗin ya kawo ƙarar ts, Allah sa dai ba a kan maganar aurensa ta yi wani abun ba, haka kawai muna zaman zaman mu za ta tada mana zaune tsaye' Ma ta faɗa tana kasa kunne don jin mai zai biyo baya domin ta san a wannan hargagin da Baba yake to tabbas maganrsa sai kowa ya ji don bai iya faɗa a hankali ba.
Sadiya da ta fito jiki sanyi ƙalau tana tafiya kamar ƙwai ya fashe mata a ciki, abubuwa da dama suna mata kai kawo na saƙa da warwara amma ta rasa makamar da za ta kama na dalilin wannan kiran da Baba yake mata.
Cike da masifa ya ce
"Sadiya mai kika yi wa Nasir?" Tambayar ta saka zuciyarta tsinkeww Æ´aÆ´an hanjinta suka hargitse tana zare ido cike da tsoro ta ce
"Baba wani abun Nasir ya ce na masa?" ,Ta tambaya kamar zuciyarta za ta fasa ƙirjinta ta fito. Baba takalminsa ya ciro daga ƙafa wanda na hagun ne amma a ƙafar dama tun da garin sauri ya sako a baibai da takalmin ya shiga nunata sai kuma ya ɗaga takalmin ya yi kanta zai kai mata duka da sauri ta tashi ta yi baya don dama da ta zo tsugunnawa ta yi a gabansa, Mama Habiba da sauri ta ƙaraso ta shiga tsakani gabaɗaya kowa ya fito ya yi carko-carko don yanayin yadda Baba yake hargagi babu abin da zai sa mutum ya kasa yunanin sakin Sadiyar aka yi kuma wani babban laifi ta aikata.
Kalifa ma fitowa ya yi hannunsa duk miyar da yake cin tuwo ɗaya hannun kuma riƙe da ƙaramar wata roba da Mama ta zuba masa tuwon don dama a nata ta ɗauka masa ta ba Sadiya sauran.
Baba ya ce
"Ina tambayarki kina tambayata",
Tana girgiza kai ta ɓuya a bayan Mama Habiba ganin kamar zai duke ta da takalmjn sai kumfar baki yake.
Mama Habiba tana bashi baki cike da jin haushin ta ya saka hannu ya matsar da ita gefe guda yana nuna ta da takalmin hannunsa ya ce
"Na sha faÉ—a miki ki fita sabgata da ta Æ´aÆ´ana amma rawar kai ya hana ki" Bai jira cewarta ba ya matsa kusa da Sadiya ya ce
"Uban mai kika masa ya kwaso ki ya dawo da ke gida?" Cike da rawar baki da na jiki ta ce
"Wallahi Baba iya sanina ban masa komai ba, ina zaune ina ba Kalifa kunu ya shigo muna hira da shi har yana dariya ya ce in zo mu zo mu gaishe da ku" Shiru ya yi yana nazari don wani ɓangare na zuciyarsa ya fara raya masa cewa ko dai da gaske babu abin da ta masa ko dai ya je wani waje ne ya dawo amma kuma hankalinsa ya ƙi kwanciya da hakan.
Cike da tuhuma ya ce
"Kuma kin tabbata babu wani tsohon laifi da kika masa? Ai sau da dama ana yi wa mutum laifi sai yake tarawa rana ɗaya ta yi hukunci" Kia kawai take girgizawa domin yanzu Baba ya ƙure duk wani ƙwarin gwiwarta musamman da yance ko tsohon laifi ne aka tara, tun ba a je ko ina ba sai ta ji gabaɗaya gidan ya gundure ta, kai a rayuwa a ce gidan mahaifinka baka da kataɓus ko ikon zuwa ka ji daɗi sai dai koyaushe ana tsoron mutuwar aurenka kamar a kanka aka fara aure, bayan aure babu inda aka haramta mutuwarsa sai dai kawai sakin halattacen abu ne da ubangaiji ba ya son sa saboda a duk lokacin da aka yi sakin aure sai al,aeshin ubangiji ya girgiza.
Jifa ya yi da takalamin gannunsa sai lokacin ma ya gane ashe ba daidai ya saka takalmin ba, yana jan wani uban tsaki ya gyara saka takalmin, gabaɗaya bashi da wata nutsuwa, waya ya ɗakko a aljihunsa ya shiga dokawa Nasir kira sai dai ba a cewa a kashe amma dai wayar bata shiga da alama dai Nasir ɗin ya saka lambar Baba a wani waje da baban ba zai same shi ba ko dai black list ma ya daka shi oho. Ya kira ya yi sau goma amma waya bata shiga ba, ƴan gida sai ƙusƙus ake, Mama Talatu tana daga bakin ƙofar ɗaki ko yawu ta kasa haɗiya tana fargabar ko dai Nasir ya saki Sadiya idan kuwa haka ne tabbas nata auren ma yana cikin jalala kamar yadda Baba ya sha jadda da mata a baya cewa matuwƙar dai ta zuga Sadiya ta kashe aurenta to tata igiyar auren ma tana cikin wani hali.
A zafafe ya ce
"Kira min shi in ji dalilin kawo ki gidan nan da duhun magriba ya tafi babu wani ƙwaƙƙwaran bayani" Duk ta rikice da masifar Baban hakan ya sa ta ma manta da batub wata waya. Sai da ta tuna sannan ta ce
"Am na...na... bar wayar a gida" Baba da ƙarfi ya ce
"Allahumma ajirni fi musiba" Kai Sadiya ta sunkuyar tana jin zafin furucinsa, sai kuma cike da gargaÉ—i ya ce