Sashe 54
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun da aka watse gabanta yake ta faman dukan tara -tara domin abin ya ma zarce dukan uku-uku tunaninta guda ɗaya shi ne, kar a je Nasir ya fahimci sirrin da take ganin ta haƙa rami ta binne wato ya gane ɗanyen aiki da ta yi wa tinƙahon kowacce mace wanda ake fata da burin ta kai ga mijinta na sunna amma ita tuni ta ɓarar da wannan damar a titi. Sannan fargabar ma bata wuce cewa shi Nasir yana mata kallon mutuniyar kirki sannan mahaifiyarsa tana mata kallin mai ladabi da biyayyar da har suke ganin ta zarta uwar gidansa Sadiya bayan duk abin da suke zato ba haka ba ne.
Yanzu ta fi mayar da hankali ga cewar an ƙare lafiya ita da Nasir a daren faekon nan ba tare da ya fahimci cewa an masa riga malam masallaci a abin da yake ɗoki da zumuɗin samun a daren farko a wajen amaryarsa. Duk da ta san da wuya gyara ya yi kamar sabo amma dai an bata tabbacin abubuwan da ta yi amfani da su Nasir ba zai taɓa gane ita ba cikakkiyar budurwa ba ce, sannan uwa uba wani magani da za ta yi amfanu da shi wajwn daƙile masa wannan tunanin duk ƙwawa da ƙwaƙwarsa bai isa ya yi wannan tunanin ba, dole ko ya yi yunƙurin hakan abin ba zai yi ba. Tana zaune bakin gado abin duniya goma da ashirin ya kwaɓe mata sai saƙa da warwara take, jin lokacin da ya turo ƙofar falon tare da mayarwa ya rufe, tabbas gabanta ya bada sautin rasss ta yadda daƙyar ta iya saita kanta yadda ba zai fahimci yadda jikinta take karkarwa ba,duk da an ce marar gaskiya ko a cikin ruwa gumi yake amma dai za ta yi ƙoƙarin wajen daƙile wannan karin maganr na bahaushe ba tare da hakan ya faru ba don ba za ta taɓa barin Nasir ya gane ba.
Yanayin sallamarsa da ya yi zuwa bedroom ɗin ya sa ta fahimci tana cikin farinciki sannan a muryarsa ta gane yana cike da ɗoki, dunƙulallan maganin hannunta wanda shi ne zai gusar da tunaninsa wajen gane an ci da rabinsa tun a waje, shi ta yi dabarar sokewa a ƙugugunta kasancewar laffaya ta ɗaura a saman kayan jikinta. Tana zaunen tana ɗan qasa da yatsunta ya ƙaraso gaban gadon yan daɗin
"Amarya kin sha ƙamshi" Kamar yadda bata amsa sallamar tasa ba haka nan bata amsa kirarin amaren da ya mata ba tana son ƙara tabbatar masa da cewa ita mace ce mai kunya, wannan abin da ta yi na sunkuyar da kai ba tare da ta furta komai ba shi ya farantawa Nasir yana ji a ransa burinsa ya cika ya auri wacce yake so mace mai kunya da ladabi haɗe da biyayya ba irin Sadiya ba da yake ganin bata masa biyayya, sannan yana murnar zai ɓarje amarci sa sabuwar amarya tun da a nasa tunanin Sadiya ta zama tsohon yayi yanzu domin yana ganin ma ai an daɗe da cin moriyar ganga dole a yada korenta.
Babbar rigarsa ya cire ya samu wuri ya ajiye, ya ƙaraso gaban gadon ya tsaya a gabanta hannu biyu ya saka ya ɗaga mayafin laffayar da take kanta, ya kai hannu ya ɗago haɓarta sai ya ga ta rufe idanunta wani irin daɗi da farin ciki yake ji a ransa tabbas ka auri wanda t
kake fata da buri shi kaɗai ma abin alfahri ne. Saɓanin a zuciyar Meenal ba haka ba ne illa fargaba sai yanzu take tunanin dama haka ƴanmtan da suka watsar da mutuncinsu a waje suke tsintar kansu a fargaba da tashin hankali idan an kai su gidan miji.
Bata ankara ba ta ji hannunsa cikin nata, ya kama ta ya tada ita tsaye tana wani kauda kai ita ala dole kunya cike da wata murya da bata san ma yana magana da irinta ba, duk da ta san yau amarya take kuma a ranar farko don haka yana iya mata magana da kowane lafazai mai daÉ—i ji ta yi ya.ce
"Duk kunyar nan yau zan cire miki ita" Ƙara sadda kai ta yi a haka ya kamata ya kai ta ƙofar banɗakin bedroom ɗin, ya tsaya ya ce
"Za ki iya yin alwala mu gabatar da sallah ko ni zan miki da kaina" Kafaɗa ta ɗaga masa alamar a,a wato bata son fa mata alwala, hakan ya sa ya ɗan yi murmushi don ya gane kunya take ji. Nan ta bar shi tsaye ta shige banɗakin ta rufe ƙofar ya saki wani murmushi don shi ma ya mata uzurin ba zii bita ba don ya san dama yau dole a rina wai an saci zanen mahaukaciya wato dole kunya ta lulluɓe ta.
Meenal tana shiga banɗakin ta ɗakko wannn dunƙulallan abun ta tura a matancin ta, ta ɗan ji sawaba a zuciyarta jin da za ta saka abin ya shiga dakyar alama ce ta matain ya yi sai dai tana ta wasi-wasin anya hakan ya yi kuwa. Ruwa ta kama ta ɗaura alwala ta gyara laffayar ta, ta buɗe ƙofa ta fito sai da ya kama hannunta ya kaita har falo ya zaunar a akan kujera kafin ya koma yana cewa ta bashi mintina kaɗan yanzu zai ɗauro tashi alwalar, jim kaɗan sai gashi ya dawo ko sallaya basu shimfiɗa ba suka yi sallar kasancewar komai sabo ne wato wajen yana da tsafta tun da kafet ne. Bayan sun idar suka ɗan taɓa kayan maƙulashen su duka babu wanda ya ci abin kirki shi yana zumunɗin amarci ita kuma tana fargabar ya ji ba daidai ba, don ta san muddin ya gane akwai matsala saboda komai ya kwance mata duk wani ƙuduri da za ta aiwatar a gidan ba za ta samu dama ba komai zai ɓalɓalce wanda bata fatan hakan.
Suna gamawa bai bari ta taka da ƙarfarta ba ya sungume ta gabanta yana dak-dak-dak bayan sun yi shirin kwanciya ya kashe wutar ɗakin, daga nan kuma abubuwan da suke da wuyar durtawa a baki suka fara faruwa, shi dai Nasir a hankalce tun da ya kai ziyarara wannan waje ya so dai ya fahimci wani abu sai dai ya kasa gane mene ne sai ya ji kamar ya manta mai yake so ya gane wanda kamar dai akwai matsala amma ba zai ce ga matsalar ba. Ko da komai ya lafa Meenal ta ga bai nuna komai ba hakan ya sa ta gane maganin da ta karɓa wajen malamin nan ya yi aiki duk da ta san ya ce mata abun zai iya warwarewa amma dai ta san in aka wuce wannan ranar to ita bata da wata damuwa.
Ko da safe haka ta narke ta ƙi fita ko falo wai ita ala dole ƙafafunta basa haɗuwa, ko banɗaki za ta shiga kamar ƴar shayi haka take tafiya tana son nuna masa cewar shi ne dai farkon wanda ya fara saninta a mace. Abu kaɗan za ta hau raki shi dai duk ya kasa ganewa.
A ɓangaren Sadiya tun da ta sha kankanar nan duk da bata wani sha da yawa ba, sai ta mayar frige ta je ta yi shirin kwanciya, bayan ta kwanta sai ta ji zuciyarta ta mata ƙunci, tana ta mata saƙe-saƙe cewa yau ce ranar farko da za ta kwana ita kaɗai a ɗakin sannan ita kaɗai a gadon ba tare da Naair ba. Zuciyarta tana azalzalarta a kan cewa yanzu yana can tare da wata matar da ita ba, yanzu haka suna kaza da kaza sun yi kaza jin dai shaiɗan yana neman haddasa mata baƙinciki haɗe da rashin bacci sai ta shiga karanto addu'o,in a take ta ji duk wani ƙunci da baƙinciki ya yaye tamkar bata da wata damuwa. Bata ma san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ita ba.
Bata tashi ba sai da asuba, dakyar ta sakko daga gadon saboda jikinta ya mata nauyi cikinta yana ƙara girma sosai. Bayan ta idar da nafila raka,atainil fajr ta yi sallar asubar sannan ta zauna ta yi ta addu,oi haɗe da karatun qur'ani. Bayan ta gama ta ɗan jingina da jikin gado bayan ta miƙe ƙafafunta da ta ga yau sun kumbura bacci ɓarawo ya sace ta. Ko da ta tashi daga baccin wanka kawai ta shiga ta saka wata doguwar riga marar nauyi, Kalifa har lokacin bacci yake, madara da ta bayar aka auno mata kwata da milo sacet guda ta haɗa shayi mai kauri ta sha domin har lokacin akwai nepa hakan ya sa ta jona ruwan, jin yunwa abin cikinta sai motsi yake.
Ɗakinra ta gyara tass ta kunna turaren wuta ɗan tsinke, lokacin Kalifa ya tashi ta wanke masa baki ta masa wanka sannan ta haɗa masa shayi ta bashi da biredi ya cinya ƙoshi tun da jiya ana taro bata yi tuwo ba.
Har ƙarfe goma babu alamar amarya da ango, wajen goma da kwata Sadiya tana wanke-wanken ƴan kwanuka da suka rage babu wanki don jiya sai da aka wanke duk kwanukan da aka ɓata. Nocking ɗin gidan aka shiga yi, ta tashi tana ɗan jin yadda bayanta yake riƙe mata, Kalifa kuwa yana ta wasan sa, tana zuwa zauren ta ce
"A nan ne? Waye?" Ta tsinkayi muryar Husna cike da gadara ta ce
"To sarkin ƴan ƙarfin hali ɓarawonda sallama, ki buɗe mana gidan tun da yanzu dai ya zama mallakin ku, ku biyu" ,Bata ce komai ba ta buɗe, ko tsayawa bata yi ba ta juya su kuma Husna da Hibba suka shigo sai da suka zo ƙofar ɗakinta sannan suka yi sallama a daƙile amsa musu ta yi ba tare da ta ƙara bi ta kansu ba ta wuce wajen da take wanke-wanke Hibba ta kalli Kalifa don ganin ta ƙular da Sadiya ta ce
"Yaro É—an sabuwar amarya yau babanka ya kwana yana shan amarci ko?" Shi kuma kawai kallonsu yake don ba wani sabawa da su ya yi ba.
Sadiya ko kallo basu ishe ta ba ta cigaba da É—aukan kaya tana shiga da su kicin ta baiwa banza ajiyarsu, ta fito ta sunkuya dakyar tana wanke wajen sai Husna ta yi karaf ta ce