← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 106

Sashe 17

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sadiya wallahi ki fita idona in rufe, mijin da ya rufa miki asirin kike zagi, shin wuta balbal kike son shiga Sadiya?" Kallonta ta mayar kan Nasir da ya kaÉ—a kai alamar ta dai ji rufa mata asiri ya yi.

Kafin ta samu zarafin furta komai Baba ya ci gaba da cewa

"Wallahi idan ba so kike in zo har gidan in saɓar miki ba ki masa biyayya ko wuta ya ce ki faɗa ba dole ki shiga ba Sadiya tun da mijinki ne aljannarki tana ƙasan ƙafafunsa, kin samu Allah ya tarfawa garinki nono kin yi aure amma kike tada fitina da dai ban san ki da haka ba ko ƙawaye kika samu suke hure miki kunne?" Jin Baban ya dakata ta gane kamar ya bata damar magana hakan ya sa ta ce
"Baba tun da na dawo yana ganina fa ya tafi da mukullin a titi muka wuni sai yanzu ya dawo kuma bani da damar da zan nuna ban ji daɗin abin da ya yi min ba sai ya kai min hannu? Marina fa ya yi Baba yana ta faɗa wa iyayena maganganu... Cike da faɗa Baba ya katse ta ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba yana ta ɗora mata rashin gaskiya a ƙarshe ya ce idan ya ƙara jin wata magana ta ɓullo sai ya saɓar mata.

Duk abin da ake Nasir yana ji, kawai murmushi yake saki jin Baba ya ce ta ba Nasir haƙuri a kan kunnensa ya ji haka ta buɗe baki ta bashi haƙurin cikin dashashshiyar muryarta, sannan Baban ya ce ta ba Nasir wayar tana jin yadda ya ringa ba Nasir haƙuri tamkar zai ari baki yana ta yi wa Nasir ɗin godiya kamar wanda ya masa kyautar kujerar makka.

Juyawa kawai ta yj ta koma kan sallayar ta fara sallar magriba, tana saddaƙarwa da cewa wannan gidan auren kamar kurkuku yake a wajenta, sai dai ta san ba za ta dawwama a haka ba akwai ranar ƙin dillacin ta san ko ba jima ko ba daɗe sai Allah ya mata sakayya a kan zalincin da Nasir yake mata, ko da bayan ranta ne kuwa.

Bayan ta yi har isha'i ya zo ya buɗe store ya ɗakko mata taliya rabin leda ya miƙa mata, karɓa ta yi ta nufi kicin ɗin ta shiga kunna gawayi don mahaifiyar Nasir ta yi uwa da makarɓiya ta hana ta kunna gas ɗin da Nasir ya saya tana amarya ɗan ƙarami, ta ce ita Sadiya bata dace da amfani da Gas ba saboda a gidansu da icce ake amfani. Dakyar ta samu gawayin ya kama ta ɗora tuwan zafi ta dawo falon, sai ta ji kamar ta rufe ido ta buɗe ta ganta a wata duniya daban. Tun da ya bata taliyar ya fice, ta gama dafawa ta soya manja ta zubo abincin ta ajiye ta ɗauki Kalifa ta ke ta wanke masa ido da baki tuni ya ware don dama yunwa yake ji, haka yake cin abincin kaɓr me saboda yunwa, ita kuwa kaɗan ta samu ta ci shi ma duk babu daɗi.

Haka ta yi shimfiɗa ta kwantar da Kalifa ta shiga ta yi wanka tare da ɗauro alwala ta saka rigar bacci marar nauyi ta yi addu'a ta kwanta har lokacin Nasir bai dawo ba, ganin an kawo nepa ta tashi ta saka cajin wayarta ta koma ta kwanta tana rungume da filo tana ta tunanin lamarin gidan aurenta, rana zafi inuwa kuma ƙuna, hawaye yana ta bin kumatun ta mafita take nema ita dai da za a ji damuwarta a magance mata da da daɗi amma babu mai saurarenka iyayenka kawai burinsu ka zauna a ɗakin miji daɗi da wuya ko da kuwa a wulaƙance ne. Tana ta wannan saƙa da warwarar bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita.

Nasir sai wajen ƙarfe goma saura ya shigo gidan, yana can majalisa da abokai ana ta hira, yana shigowa ya rufe ƙofar gidan ya shigo gidan yana wani bada faɗi, sai kuma ya ga baiwar tashi bata ma falon tsire da coca colan da ya shigo da su ya zauna ya baje a falon ya cinye a shanye lemon ya tashi ya bar mata takarda da robar a wajen. Bayan ya gama abin da zai yi ya saka hannu a aljihu ya fito da wani ƙullin ruwan magani a farar leda ya tula ya shanye ya fito ya jefar da leda, kayansa ya cire daga shi sai singlet da ƙaramin wando ya haura kan gadon bayan ya kashe gabaɗaya fitilun. Kasancewar Kalifa a ƙasa take masa shimfiɗa a kan ƙaramar katifa da yake gidan ciki da falo ne, sai kicin da banɗaki kawai sai kuma ɗaya part ɗin inda ciki da falo sai ɗaki ɗaya wanda an fara ginin an kai linta amma ba a ƙarasa ba. Yana hawa gadon ya kwanta ya miƙa hannu ya shiga tashin Sadiya, cikin bacci ta ji yana buga mata ƙafa ta ɗago jajayen kumburarrun idanunta ta kalle shi ta cikin ɗan hasken farin wata da ya ratso ɗakin.

Cike da gadara babu tausasa murya ya ce

"Haƙƙina na zo karɓa" Ranta ne ya sosu wai mutumin da ya gama ci mata mutumci har marinta ya yi amma yanzu kuma ya zo da wata buƙata, a kasalance irin na wanda yake cike da bacci da gajiya ta ce

"Dan Allah Abban Kalifa ka mini lamuni yau wallahi ba na jin daÉ—in jikina" Kamar wanda ta watsa masa wuta haka ya zaburo mata ya ce

"In baki taliya ki cika ƙundunki ki shi ne tawa buƙatar ba za ki biya min ba? To in dai wancan taliyar da na ga kin ajiye mini a ƙaramin filas ce kike yi wa ki je ki ɗauka ni nama da lemo na sha, idan kin cinye sai ki zo ina jiranki da alama ƙoshi ne baki yi ba shi ya sa kike mita" Cike da ƙosawa da kalamansa ta ce

"Ni ba yunwa nake ji ba kawai dai zuciyata ce babu daÉ—i"

Zaune ya miƙe ya saka hannu ya daki kan katifar kan gadon ya ce

"Ko zuciyarki da daɗi ko babu wannan ke kike sakawa kanki kuma ke kika ga za ki iya, ni dai yanzu haƙƙina dole ki bani tun da sadaki na bayar" Tun da ya yi wannan furucin bata ƙara furta komai ba ya cire kayan jikinta, babu wani ɓata lokaci ya shiga biyan buƙatarsa ya daɗe yana abu ɗaya sai da ya gaji don kansa ya ƙyaleta, ita kuma tana kwance kamar gunki don dama babu wani abu da take fuskanta a lamarin don damuwa ta gama yi wa zuciyarta katutu, shi kuma lamarin mu'amalar aure ana son gabatar da shi a lokacin da ake cikin walwala farinciki haɗe da annashuwa.

*IBRAHIM*

Kafin ya ƙarasa gidan su Jidda ya haɗa uban gumi sharkaf abin ka da wanda ya saba rayuwa cikin AC gida AC mota AC office ma AC.

Ko da ya zo bai ƙarasa saitin gidan ba daga ɗan can gefe ya tsaya yana hangar ƙofar gidan, sai lazimi yake a zuciyarsa, yana addu'ar Allah ya sa ya dace.

A can cikin gida kuwa Aliya ce take gwada wata doguwar rigar abaya maroon da takalmi haÉ—e da wata jaka sai murna take tana cewa

"Gaskiya Kasim ya iya zaɓe"

Umma ta yi karaf ta ce

"Wannan ai za a je da shi, kin ga duk da ba mai arziƙi ba ne ai yana da wadatar zuciya, daga ganinsa irin mazan nan ne masu bautawa mace, kika dai yadda yake miki wahala komai ya samu ke yake yi wa"

Aliya ta ce

"Umma ai wanna da kike gani bawan mace ne"

Umma ta ce

"Ai tun da dai yana da karatun digirinsa digirgir kuma yana da ƙashin arziƙi daga gani, gashi yana sonki yana bauta miki tabbas in kika aure shi kakarmu ta yanke saƙa, wuyarta ya samu aikin gwamnati da takardun nan basa ai shi kenan kin zama babbar mace" Wani uban tsalle Aliya ta daka tana murna tana sanar da Umma Kasim ɗin ma ɗazu ya ce zai saya mata sabuwar waya. Da gayya suke ta maganganun nan da yada magana duk abin da suke Jidda tana jin su, ita damuwarta ma da jiya da daddare Abba ya tara su ya ce kowacce ta fitar da miji shi bai san cewa Jidda bata da wani tsayyaye ba, ita kuma tana jin nauyin sanar da Abban.

Ta yi nisa a tunani Umma ta ƙwalla mata kira, tana fitowa ta saka ta wankin kaya, haka ta karɓa don dama yau Ummar ce ta hana ta zuwa islamiya saboda aikin gidan. Aliya ce ta gama saka kayan gabaɗaya a leda ta cewa Umma za ta je gidan su Amatullahi ta kai ta nuna mata Umma ta ce

"Yawwa maza kula ki je ki nuna mata kin kece raini kuma kina da mijin da xa ki aura na nunawa sa'a" Ta faɗa tana kallon saitin Jidda da ta duƙufa wajen wankin zanin Ummar. Ko da Aliya ta ɗauki ledar ta fito ƙofar gidan, Ibrahim daga can inda ya tsaya ya hango ta, kasancewar bai shaida ta ba sai ya taho domin yana son ya tambaye ta ko Jidda tana ciki, bai gane ta ba sai da ya zo dab da ita, ita kuma Aliya a lokacin da ya ƙaraso tana ƙoƙarin kara waya a kunne don Amatullahi take kira za ta ce mata gata nan za ta nuna mata kaya. Ganinsa ya sa ta fasa kiran wayar ta kashe tana ƙare masa kallo, tabbas ko daga bacci ta tashi ba za ta kasa shaida wannan fuskar tasa ba.

Fuska ta yatsina tana masa kallon ƙwaf, shi kuma gabaɗaya kansa ya kulle da ya ganta don tabbas ya shaida ta ita wacce ta ciwa direbansa mutunci ranar nan. Gabaɗaya ma sai bakinsa ya ƙi bashi haɗin kai wajen yin sallamar da ya yi niyyar mata, bare a kai ga tambayar da zai mata a kan Jiddar tana cikin gidan.

Aliya kuma sai ta shiga masa wani kallon raini tana yatsina, gabaÉ—aya sai ya tsargu da kallon nata amma sai bai ce mata komai ba, cike da mamaki da gatsali ta ce
Chapter 17 · 0% Book details