← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 106

Sashe 50

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanka suka ƙara yi da ruwa mai ɗumi bayan sun fito yana shiryawa sai suka ji horn hakan ya sa ya gane saƙon Mummy ya iso, yana jin lokacin da me gadin ya buɗe ƙofa.

A saman ta baro shi yana shiryawa ta sakko ƙasa bayan ta saka kayan da ta cire, Ɗakin da aka kaita ta shiga, ita sai yanzu ne ma take ƙarewa falon kallo tamkar a wata ƙasa take da ban. Bayan ya gama shiryawa cikin farar shadda gezna sai sheƙi take tana ƙamshi ga turaruka masu aji da ya feshe jikinsa da su. Nocking ya ji a bakin ƙofar ya sakko cikin nutsuwa yana ɗaura agogo a hannunsa, yana buɗewa mai gadi ya gaishe da shi cikin girmamawa, amsawa ya yi ya karɓa kwandon da ya kawo yana sanar da shi direba ne ya kawo daga gidan Mummy. Faɗwa mai gadin ya yi cewa ya san da zuwan nasa shi kuma ya juya Ibrahim ya rufo ƙofar ya dawo ya nufi kan dining ya ajiye kwandon amma a ƙasa a gaban dining ɗin.

Ɗakin ta ya nufa lokacin tana gaban drower ɗinta bayan ta bar gaban madubi inda ta tsaya shafa kwalakca da humra da sauran body spray da shuwa masu bala,in ƙamshi don kan madubin ya sha jere tamkar an je shago, drower da ta buɗe yadda kaya suke a jere sai da ta ji wani iri yau ita Jidda ce wacce Umma take ƙwace mata duk wasu kaya masu kyau da nagarta idan Abba ya ɗinka musu amma gashi komai ya zama tarihi tun da gashi yanzu kaya masu tsadar da bata tama tunanin ko a mafarki za ya saka irinsu ba.

Tabbas komai na rayuwa idan ka yi haƙuri zai zama tarihi watarana!. Yanzu gashi komai ya wuce, yana sako kanshi ɗakin tsabar ƙamshin turarukan da suka bugi hancinsa hatta sallama suɓuce masa ta yi, kasancewar tamkar wanda aka yi ɓarin turare a ɗakin abin birgewar ma ba za ka taɓa gane wane irin ƙamshin turare ba ne. Jin alamun mutum ya sa ta waiwayo kasancewar tana ɗaure da towel da yake da ta shigo kayan ta cire ta ɗauki wani towel sabo ta ɗaura, ganin ya tsaya a rungume hannunsa yana mata wani kallo bata san lokacin da ta ce

"Sannu da zuwa" Maganr tata ta bashi dariya sai ya ce

"Kin manta kin gaisheni ɗazu yanzu kuma sannu da zuwan ta mene ne?" Bata amsa ba din ita kanta ta ba kanta dariya. Bata ankara ba sai ta ganshi ya zo dab da ita ya kama dantsen hannunta duka biyu sai gani ta yi ya janyo ta ya zaunar da ita a bakin gado, wucewa gaban drower ya yi ya tsaya yana ta ƙarewa kayan ciki kallo amma sai ta ga ya rufe, wata ya buɗe sai kawai ta ga ya ɗakko wata riga daga gani ba za ta wuce gwiwa ba sannan sai aka mata ƙaramin hannu, daga gaban rigar akanyi hoton heart babba daga ƙara aka rubuta GIRL da manyan baƙi.

Miƙo mata kawai ya yi ya ce

"Ita nake so ki saka" Karɓa ta yi a ranta tana cewa

"Ka ji kaɗan ka ji da yawa, ni Jidda dama a gidan auren miji ne yake zaɓa maka kayan da za ka saka?" Ta tambayi kanta sai ta ji yana cewa

"Ba zan ɓoye miki ba Jidda tun da na shigo ɗakin nan na tsinci kaina a wani yanayi mai wuyar fassara, sai dai ina tausaya miki kasancewar daren ki na farko ne kuma na yi dogon zango amma ba don haka ba, da sai kin mayae da ni ruwa" Kallon rashin fahimta ta masa ya ɗora da faɗin

"Ina shigowa da na shaƙi ƙamshin turaren nan sai ya sakani a wani yanayi, tabbas turare yana taka muhimmiyar rawa wajen haifar da yanayi a tsakanin mace da namiji, shi ya sa aka haramtawa mace ta saka turare ta fita waje maza suna jin ƙamshin, dalilinnda ya sa ake rubuta mata alhakin zina saboda ƙamshi yana tada sha'awa ne duk wani namiji idan ya ji ƙamshin turaren zai ji sha,awarta" Kai kawai take kaɗawa bayaninsa yana shigarta duk da mafi yawan mata sun yi watsi da wannan maganar suna cin karensu babu babbaka, musamman da ya kasance yanzu har kabbasamata suke yi a kayansu, su gama turara kaya su saka su fita sun manta da haramcin hakan.

Yana faɗa mata ya buɗe ɓangaren bra da panties ya ɗakko mata fararen set ya bata, bra ɗin pant ɗin, ganin tana wani juyawa kamar kunya take ji sai ya fita yana dariya, ta saka tare da ɗora rigar da ya zaɓo mata, jin yana kiranta ta fito tana amsawa wani mugun kyau ya ga rigar ta mata hakan ya sa ya ga tamkar dama don ita aka yi rigar tabbas aure rahma ne, Allah azurta kowa da mace da kuma miji na gari.

ALIYA
Wani irin bugawa da ƙarfi zuciyarta ta yi har numfashin ta yana barazanar mata wahalar shaƙa, jin furucin Amataullahi, a take bakinta ya bushe babu ko ɗigon lemar da za ta sanya laɓɓanta da suka yi gaggawar bushewa su jiƙu. Bata san tana da zafin nama ba sai da ta ganta tsaye ƙiƙam a kan ƙafafunta da zuwa lokacin sun fara karkarwar gaza ɗaukar gangar jikinta ba komai ne abin da ya razana ta haka ba illa furucin Amatullahin da ta ce tarayyarta da Kasim sau ɗaya zai ruguza mata abubuwa dubu, sannan in har a tarayyar da aka yi an samu ƙaruwa hakan yana nufin zai barta da jelar ciki da reno ma'ana shikenan ya yi sanadin rugujewar burikanta ciki kuwa har da mallakar Ibrahim matsayin miji da kuma zama kishiyar Jidda don ta mata gashin ƙuma!.

"Hannunta yana dafe da ƙirjinta ɗayan kuma tana riƙe da wayar da take kunnenrta ta ce
"Na shiga uku Amatullahi, wallahi ya yi tarayya da ni" Amatullahi ta ce
"Wato ya kalamance ki da kalamansu na maza ko har kika yarda ya karɓe budurcin, kenan daman jiya duk burin kunyar ƙarya ne kike yi?" Cike da takaici Aliya ta hau labarta mata cewar ita fa ba wai da saninta ba, gabaɗaya ma vata cikin hayyacinta abubuwan suka faru. Nana Amatullahi ta ce
"To kuwa ba a bori da sanyin jiki, za ki iya ƙwatarwa kanki haƙƙi, tun da wannan ai an yi zamba cikin aminci, an sakanyaudara a lamarin tun da an rufe ku, ta yaya za ki auri mata-maza Aliya, duk kyau da ajinki amma ki ƙare a mai mafitsara biyu, Allah dai ya sa ma dai bashi da breast a ƙirji a toh don idan mun zo gidan kar muke kasa bambance tsakanin aya da tsakuwa, ma'ana muke kasa gane ki da kuma shi tun da baku da bambanci a halitta" Kuka Aliya ta fashe da shi ranta yana ƙuna tana jin tsanar Kasim ta ce

"A yau ba sai gobe ba Kasim zai sakeni!. Ba zan zauna da shi ba, wannan ai yaudara ce tsantsa, ko kotu na kai shi ya cancanci kowane hukunci" Tana maganar tana kuka, ita kuma dama tana jin haushin Aliya ta yi aure ta barta hakan ya sa ta ringa zuga Aliya don ta kashe auren su zama É—aya.

Sai da ta gama ɗora Aliya a tamfa sannan ta kashe wayar Aliya ko kiran Umma bata tsaya yi ba, ɗaki ta nufa a sukwane ta saka kaya kala biyu a kit ɗinta ta ɗauki hijabi ta saka, hannu ta miƙa za ta ɗauki wayarta da ta ajiye wani takaici ya sake cikata ganin screen ɗin kwatsa-kwatsa tana tuna cewa wai yanzu ita Aliya ce da wannan ƙazamar wayar Jidda kuma da bata isa komai ba mummuna ita ce mai iphone, sannan ita tana wannan ƙazamin gidan Jidda tana katafaren gida, daɗin abin haushin shi ne Jidda lafiyayyan namiji take aure ita kuma mata-maza tabbas wannan yana nuni da cewa ba ƙaramar tazarw ba ce a tsakaninsu.

A zuciye ta ɗauki wayar kamar ta buga ta a bango sai dai ta lallashi zuciyarta don ta san yanzu dai bata da wata wayar sai wannan, fitowa ta yi lokacin tana tsakar gidan ta ga kiran Umma yana shigowa hakan ya sa ta kashe wayar ma baki ɗaya, don ta ƙudurta a ranta sai dai Umma ta ganta a gida, duk da cewa wata zuciyar tana bata shawarar kar ta je gidan saboda kar ta fusata Abba ya ɓata mata rai, amma kuma in ta tuna cewa lamarin mata-maza saj ta ga ba magana ce da za a yi sanya ba, watsar da shawarar zuciyarta tata ta yi kan maganar zuwa gidansu Kasim don ta fi so ta je gidansu in ya so idan Abba ya zo ya ji abin da yake tafe da ita sai ya yi magana da mahaifin Kasim a kawo mata takarda, don ta yi imani da Allah babu wani wanda zai do ƴarsa ta zauna da mata maza ga shi uwa uba ma ƙin sanar da ita da aka yi kafin auren.

Kasim da suka gama waya da Salis sai ya shiga wani shago da yake gefe yana son sayan alewa ya yi sadaka, domin wannan lamarin na Aliya sai da sadaka, shigewarsa shagon ya yi daidai da fitowarta don haka ko ƙofar gidan bata karo ba ta bar masa ita a buɗe wayam. Ɗaya ɓangaren ta yi ba inda shagon da Kasim ya shiga ba, don haka bai ganta ba, tana riƙe da kit ɗin tana tafiya kamar za ta ci da ka ta matsu ta ganta a gida ko ta amayar da abin da yake bakinta don bata gane cewa a babbar matsala take ba sai da ta yi magana da Amatullahi hmmm wai ita Aliya da ta gama shirya rayuwar gidan aurenta ta jin daɗi da holewa ita ce ta ƙare da auren mata maza har ana cewa wai ba za a bambance su idan yana da breast a ƙirji!.
Chapter 50 · 0% Book details