← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 106

Sashe 81

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya fita Meenal ta kalle ta ta ce
"Ya kamata ki fara shirin haƙura da wasu abubuwa da dama daga cikin gidan nan domin ni da ke za mu yi wani zama da ba lallai ki jure ba, amma zai fi kyau ki haɗa kayanki ki nufi gida don sai hakan ya fi zamar miki kwanciyar hankali, amma a shawarce idan kuma kin ga za ki jure to ga fili ga mai doki...

*Idan Allah ya sa muna raye a page 30 za mu gama Book 1 sai mu tafi book 2 wanda shi ne za mu yi har ƙarshemkn labari, sai dai tafiyar tamu tana da nisa, domin labarin yana da ɗan tsayi sannan akwai sarƙaƙiya da abubuwan mamaki al,jabi tausayi dasussa, sai wanda ya bibiyi labarin ne zai gane abin da nake nufi.*

MAMAN AFRAH
*09025576222*

https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=hqrt1

*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 2️⃣5️⃣

ALIYA

Zaman dirshan ta yi a tsakiyar dalon tana kuka haiƙan, gabaɗaya duniyar ta mata matsi da ƙunci ji take tamkar ta kashe kanta ta huta wannan wace irin ƙaddara ce a cw Ibrahim wai ko ɗanɗanar tuwon bai yi ba don baƙinciki da takaici ma a ce wai wurgi ya yi da cokali me ɗauke da asirin a jiki kawai saboda an faɗa masa rashin lafiyar ubansa zai shikenan zai jiƙa mata aiki. Bayan ta sha wuya da kuma kasada wajen zuwa ta sauya cokalin da kuka mai ƙarfi ta rushe tana faɗin

"Na shiga uku na lalace Allah ya isa tsakanina da uwar Ibrahim da ta kira shi ta faɗa masa rashin lafiyar ubansa har ya yi sanadin fasa cin tuwon da ya yi, daman ma uban nasa mutuwa ya yi mu ga tsiya" ,Ta faɗa tana haura ƙafafu duk ta cakuɗa gashin kanta, ɗifff ta yi kamar ruwa ya ci tw, tana saƙa da warwara ranta in ya yi dubu a ɓace yake gabaɗaya sai tsanar mijinta Kasim mata maza ya turnuƙe mata zuciya tana tuno irin yadda ta bashi haɗin kai a gadon su na sunna a daren jiya duk don tana cike da ɗoki da farincikin cikar burinta na auren Ibrahim ashe dai bata san tufkar da ta yi an warware mata ita gabaɗaya ba!.

Sai da ta sha kukan takaicin ta tsagaita sannan ta janyo wayarta ta kamo sunan Umma ta doka mata kira Umma tana ganin kiran ta É—auka cike da murmushi ta ce

"Tilon ƴata ki ce aiki ya kammala yanzu za mu fara baza capacity, wallahi naira sai ta ci ubanta a wajenmu, motoci da gidaje masu kyau sai sun san mun yo kuɗi mun kerewa wulaƙanci!" Ta faɗa tana jiran Aliya ta fara kora mata bayani Maimakon ta ji muryar Aliya cikin farincki tana mata bayani sai ta ji Aliya ta fashe da kuka Umma hankali tashe ta ce

"Kukan me kike Aliya? BuÉ—e bakin ki ki faÉ—a min wallahi gabana faÉ—uwa yake kar dai ki faÉ—aa min mummunan labari mai ya faru?"

Aliya cike muryar kuka ta ce

"Umma bai ci tuwon ba" Umma tana zare ido tamkar kwarton da aka kama ta ce

"Bai ci tuwon ba to uban mai ya ci ko dai Jidda ce ta yi wani mugun tuggun da ya sa bai ci ba, ko dai ta harbo jirginki Aliya ke kike haukarki?" Ta tambaya cike da zaƙuwar son jin dalilin.

Aliya ta ce

"Wannan tsohuwar tasa ce ta masa waya wai ubansa bashi da lafiya ya yanke jiki ya faɗi shi ne ya jefar da cokalin tsabar ruɗewa a sibiti ma ya kwana tuwon ya lalace an zubar" Ta faɗa tana kwashe komai ta faɗawa Umma da take jin ɓacin rai tamkar ta yi ƙaramar hauka, sosai ranta ya ɓaci ta ce

"Ki daina kuka Aliya in har ina numfashi a doron ƙasa saj kin cika burinki, ko ma in ce burinmu sannan a shirye nake na yi fatali tate da tarwatsa aniyar duk wani wanda zai kawo tsaiko a lamarin nan" Aliya sai ta ji ta ɗan samu ƙwarin gwiwa hakan ya sa ta sauke wata nannuyar ajiyar zuciya nan Umma ta yi ta bata baki a kan cewa ta kwantar da hankalinta in dai gidan Ibrahim ne ta gama shiga ta gama.

Sun yi sallama bayan sun jajantawa juna Aliya saboda takaici ko da Jidda ta ƙarasa asibitin ta kira ta don ta ce ɗazu suna magana basu gama ba ta daina jin ta amma sai Aliya ta ƙi ɗaukan kiran don yanzu kawai haushin Jidda take ji.

Washe gari Umma ta kira Aliyar tana faɗa mata tare za su je ajen bokanyar don ta faɗa musu abin da ya dace a yi domin ita yanzu ta gwammace ko salwantar da rayuwar Jidda ne a yi in har za a samu biyan buƙata duk da tana son a bar Jidda a rayw domin su ƙunsa mata baƙinciki irin baƙincikin da za ta gwammace gwara mutuwarta amma in hakan zai zama matsala gwara ta bar duniyar ma su su ci tasu duniyar da tsinken tsire mai tsini. Daga Abba har Kasim babu wanda aka faɗawa fitar hanya suka sata suka tafi yana kowane ya fita kasuwa. Ko da Amatullahi ma ta tambayi Aliya sai ta faɗa mata da Umma za su je wannan karon.

Suna isa bokanya ta musu izini suka shiga. Bayan Aliya ta gabayar da Umma a matsayin mahaifiyarta sai kuma ta shiga rattabo mata bayanin yadda al,amura suka kasance wato yadda ba a dace da cin abinci da cokalin da aka yi asirin nan ba. Ta yi mamaki kuma ta jimanta abin domin tana tabbatar musu cewa da a ce ya ci abinci da cokalin nan da matsalar su ta kau har abada!. Sai dai matsalar idan aka yi aiki ba a maimaitawa sai dai a yi wani sabo. Nan Umma tw ce kawai a yi wani aikin.

Bokanya ta yi jim ta ce

"Aikin da za a yi yana da hatsari kuma yana da ci, domin idan aka yi har sai ya fi na cokali zafi sai dai shi wannan aikin ana faɗar ladan da za a biya na aiki a nan take ta sanar da su za a biya kuɗin aiki dubu ɗari biyu. Daga Umma har Aliya kallon kallo ake domin kaf cikinsu babu mai dubu goma ma ta kansa a halin da ake ciki dai yanzu babu kuɗi sannan kuma suna buƙatar a yi aikin da gaggawa.

Bokanya ta basu kwana biyu a kan cewar idan an kawo kuÉ—i za a yi aiki. Tun da suka taho suka shiga zulumi da tunanin yadda dubu É—ari biyu za ta fito, idan suka yi hasashen kuÉ—in da yawa sai kuma su tuna tasirin da aikin zai yi, tun da idan Ibrahim ya shiga hannunsu sai sun fanshe abubuwa da yawa.

Sun rabu a kan cewa za su yi waya bayan sun tsara cewa Umma ce za ta kai wa Jidda kukan buƙatar kuɗin tun da suna ganin tana gidan daula ba za ta rasa kuɗi ba.

Washe gari aka sallamo Daddy daga asibiti ya ware tass sai dai É—an abin da ba a rasa ba. Jidda tana zaune a bakin gado Ibrahim ya zo ya zauna ya ce

"Habibty rufe idanunki" Wani kallon ƙasan ido ta masa sai kuma ta murmusa haɗe da runtse idanun, ya ce ta buɗe hannunta haka ta buɗe hannun sai da ya ajiye mata mukullin a kan hannun sannan ya ce

"Buɗe idanun" Tana buɗewa ta ga mukulli a hannunta mukullin mota, nan ta shiga tambayarsa ya sanar da ita cewa Abba ya siyawa mota, don dama yana da niyya. Wata iriyar runguma ta masa tana ta murna tare da jero masa wasu addu,o,i masu daɗi hakan ya sa ya ji matsayinta ya ƙara ƙaruwa a zuciyarsa. A ranar ne ta shirya domin zuwa ta isar da saƙonsa zuwa ga Abba bayan magriba tare suka je a motar direbansa yana biye da su don haka yana ajiye ta ya bata mukullin ya shiga motar da dirwban ya zo da ita ya ce an jima zai dawo ya ɗauke ta.

Da sallama ta shiga gidan lokacin Abba bai dawo daga masallacin ishsha,i ba. Umma da take zaune a tsakar gida a kan tabarma ta buga uban tagumi ko da ta ji sallamar ma sama sama ta ji sai da ta ɗago ta amsa duk a diririce musamman da ta ga Jidda cikin shuga ta alfarma cikin shigar manyan hajiyoyi wani dakkaken leshi wanda ya amsa sunansa leshi da ƙaton mayafinta da ya rufe mata dukkan ilahirin jikinta, sai takalmi da jaka masu aji sarƙoƙin gwal ɗin da ta saka suna walwali su ne suka saka Umma jin zuciyarta har wani ɗaci-ɗaci take, ita kuma Jidda ba ita ce ta ɗakko kayan ba gabaɗaya Ibrahim ne ya ɗakko mata a cewarsa gwara ta je gida a ganta a ce ya iya kiwo sannan ya riƙe amana haka ya faɗa mata cikin wasa lokacin da ya ɗakko mata kayan.

Umma dakyar ta yi yaƙi da zuciyarta ta ce

"Jidda sannu da zuwa farae amarya" Ta faɗa tana washe haƙora tare da nuna tsantsar murnar ganinta amma a zuciyarta baƙinciki ne fal domin jin wata tsanarta take ji, Jidda kuwa sai ta ji wani daɗi take ganin tamkar mahaifiyarta ce a gidan, sosai take jin Umma har ranta. Umma sai nan nan take yi da ita amma shigarta ta tsaye mata a rai kuma ta tsone mata ido!.

Sun gaisa ta É—akko mata ruwa, tana jin a ranta tamkar ta zuba maganin mutuwa Jidda ta sha ta mutu kowa ya huta a kan yadda take ganin ya sha gabansu, take ganin tana zaune cikin haÉ—aÉ—É—e kuma tsararren gida amma tata Æ´ar tana can gidan mata maza, mata mazan ma Allah baku mu samu.

Ruwan ta sha tana ta yi wa Umma godiya don har mamaki take idan ta ga Umma tana nuna mata so da kulawa tamkar ba waccan Ummar da ta bata wahala ba, tamkar ba Ummar da ta É—ora mata karan tsana ba.

Umma cike da wasa a zahiri ta ce
Chapter 81 · 0% Book details