Sashe 99
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Ya furta zuciyarsa da wani irin nauyi ga farin cikin da yake lulluɓe shi. Sabuwar soyayyar Humaira na ƙara huda dukkan wata ƙofa ta jikinsa tana shiga tana mamayarsa. A ɓangaren Humaira kuwa ba ta san sadda yatsunta suka sauka a kuncinsa ba, dauke masa hawayen ta yi yayinda itama nata su ke zuba. Ita ya kamata ta koka ba shi ba, ta wahalar da shi iyaka, ta kuma yi mishi cin fuska kala-kala, sai dai dukkan wadannan bai sa ya juya baya ya haƙura da ita ba. Sanadinsa za ta iya cewa ta samu warakar zuci da gangar jiki daga cutar da ake tunanin iskokai ne masu sanya ta tsanar dukkan wani ɗa namiji a rayuwa. Ya riƙe yatsunta idanunsa a cikin nata gami da kai su baki ya sumbata. Ta runtse idanun tana jin kamar ta kwace yatsunta amma kuma roƙon da ya gama yi mata na kar ta yi mishi kowane iyaka ne ya sanya ta daurewa. Tana jinsa ya dinga yin yanda ya so har sai da suka nemi faɗuwa sannan ya bar ta. Ta yi saurin zama a kujera mafi kusa da ita. Shi kuwa durƙuso ya yi a gabanta gami da riƙo dukkan yatsun hannayenta yana dubanta kai ka ce ranar ya soma ganinta a rayuwa. Murmushi sosai yake yi yana kallonta yayinda ita kuma ta kauda kai zuwa gefe guda, kallonsa na haifar mata da yanayi mai kashe kuzarin jiki.
"Nagode, nagode da kika aminta da aurena. Ina mai miki albishir da cewa kin dace in sha Allahu, kamar yanda dama ni tun tuni na sa a raina samunki a rayuwa shi ne dacewar da zan yi. Alhamdulillah. Yau ga Fadeel ga Humaira. Kin ga ranar haƙuri ko?"
Ta ɗan yi murmushi. Ya kai hannu ya shafi leɓɓanta.
"Soyayyata kaÉ—ai ta isa mu rayu cikin farin ciki da aminci. Nidai na san koda ace har yau ba a wani sona, toh ana ji da ni."
Ta yi ƙasa da kanta, shiru ya biyo baya, shi bai bar wasa da yatsunta da kuma bin ta da kallo ba, ita kuma ta kasa furta abin da ke yawo a zuciya da saman leɓɓanta. So ta ke ta ba shi tabbacin cewa itama fa tana so da kaunarsa wanda ta san ya sani kawai so yake yi ya ji daga bakinta.
Miƙewa ya yi ta bishi da idanu har ya je fa ledojin da ya shigo da su yana fadin shi yunwa yake ji saboda tun safe bai ci komai ba murnar an ɗaura aurensu.
Suka ci har ta miƙe ta bar shi, yana jinta tana masa sai da safe ya gyaɗa kai kawai yana bin ta da murmushin da shi kaɗai ya san ma'anarsa. Ɗakinta ta shiga ta ɗan tura ƙofar, laffayar jikinta ta warware ta ninke ta buɗe sif dake manne jikin bango ta sanya. Rigar da ta ji Hajjo ta ce mata ta sanya shi ta fiddo, warware shi ta yi, doguwar riga ce mai hawa biyu kalar maroon. Gefenta wani gashi ne mai laushi. Ta shiga bandaki ta sauya shiga sannan ta fito ta nemi wuri ta kwanta bayan ta kashe fitila. Ba ta fi mintoci da kwanciyar ba ta ji shigowar Fadeel, kirjinta ya hau bugu tara-tara, wai yana nufin anan zai kwana? Shi ne tambayar da ta yiwa kanta, ta runtse idanunta tamau alokacin da ya hau gadon sosai, fitilar ya kunna haske ya karaɗe ɗakin, da kallo ya bi fuskarta, ya sani ba bacci take yi ba, runtse idanun na dole ne. Ba ta yi aune ba ta ji ya yaye gaba ɗaya bargon, da sauri ta dora hannuwa saman fuskarta. Ya yi murmushi ya kashe fitilar kafin ya maida bargon ya rufa musu. Janyo ta jikinsa ya yi sosai, ya fidda hannuwanta saman fuskarta, duk kuwa da cewar dakin da duhu ba ganin idanunta zai yi ba.
"Please faÉ—amin koda sau É—aya ne naji. Kinji?"
Ya na maganar tamkar mai raÉ—a. Ta yi shiru sai bugun kirjinta da yake ji, yanayin maganarsa sai ya ba ta tausayi, ta tuna dukkan gwagwarmayar da ya sha a kanta. A hankali ta bude baki ta ce.
"Ina matuƙar so da ƙaunarka Fadeel."
Ya yi ɗif na lokaci ƙalilan, ita kuwa ta samu wani irin kuzarin da sai da ta ƙara maimaitawa, kaunar tasa take ji yana fisgarta sosai. Ai ba ta yi aune ba ta ji sauran kalaman bakin nata sun maƙale adalilin toshe nata bakin da ya yi da gurbin nasa.
Daren dai sun raya shi tamkar ba za su yi bacci ba. Washegari suka tashi zuciyoyinsu cike da walwala da soyayya mai tsafta. Humaira kuwa jikinta ya yi mugun sanyi don tuna ƴar uwarta Ummita. Wannan abun shi Wizzy ya kwatar mata da ƙarfin tuwo. Wannan dai ƴancin da Fadeel ke ta cin alwashi da alƙawarin kyautata mata saboda shi? Dakyar ta samu lamarin ya fice a ranta sakamakon kulawar da Fadeel ya dinga ba ta tamkar ya haɗiye ta. Sun kira waya ta gaisa da Raihana ta kuma tabbatar da samun saukinta, hakanan da su Hajjo suka zo yi mata sallama sun ba ta tabbacin Ummita ta ɗan saki ranta har Abba na fadin zai haɗa ta da Anti Maijidda su wuce Bichi.
Hakan ya yiwa Humaira dadi kwarai domin ita kanta ba ta kaunar ganin Mami a wannan gaɓar, zuciyarta ba ta amince da ita ba kamar a baya.
***
Kafin su Hajjo su kai ga dawowa gidan Mami, sai ga Jannat sun dawo gidan har da Futuha gaba ɗaya. Sun samu labarin komai dangane da zargin da ake yiwa Mami na satar su Ummita. Futuha da Tasleem waɗanda suka san da zancen hankalinsu ya tashi ainun domin sun san komai ba kuma zargi ba ne. Jannat kuwa ashariya ta dinga zundumawa gami da yiwa Mamin Allah ya ƙara.
"Kin fifita su akan yaranki na cikinki ai ga sakamakon abin da kika yi nan kina gani."
Ita dai Mami ba ta ce uffan ba, Tasleem ko da tun a gidan Futuha take fama da lemun tsami a baka saboda tashin zuciya, wani amai ne ya taho mata da ya yi sanadin miƙewarta a guje ta faɗa banɗakin Anna. Gaba ɗaya suka bi ta da kallo. Mami kirjinta ya yi wani irin duka da ƙarfi.
"Wannan tashin zuciyar da kike ta yi dama tun a can ai nasan ba a banza ba. Sai ki tattara ki koma gidan Hamza tunda akwai sauran rabo tsakani."
Mami ta juyo a ruɗe ta ƙara bin Anna da kallo mai maganar hankalinta kwance. Futuha da Jannat babu wanda ya dara don gaba ɗayansu zuciyoyin ba dadi, ga Futuha, baƙaƙen maganganun da ake yi mata da habaici a Tiktok ya fi ƙarfin kanta. Ga kuma Yakubu da ya ɗauki Ƴar Snow zuwa Saudiya inda daga nan za su wuce Dubai sai ko London. Kuɗin da ya bar mata a wannan tafiyar shi ne rabin abin da yake ba ta kyauta a wata, gaba ɗaya ya rufe bakin aljihunsa sai dan abin da bai taka ya karya ba yake ba ta. Ta kuma fahimci azabar da yake son gana mata muddin ta yi sake za ta dame ta shanye irin kalar na uwargidansa. Jannat ma dai rigima ce ake ta yi da nata mijin, inda mahaifiyarsa da danginsa suka dage akan lallai sai ya rabu da ita ko kuma ya yi aure. Zafi biyu ya haɗe mata ga tunanin inda za ta fara samu ta tattaro kan kudadenta da ta yi asararsu.
Miƙewar Mami ce ya sa duk suka dube ta, kai tsaye banɗaki ta je ga Tasleem, suka yi kiciɓus sadda take fitowa tana share baki.
"Ke, yaushe rabonki da al'ada?"
Tasleem ta ɗan yi shiru, ita dai ta san koda ta dawo daga gidan Hamza tana jego ne ba ta yi wanka ba, tun da ta yi wankan kuma ba ta ƙara ganin jini ba.
"Ina magana kin mayar da ni sakara! Nace yaushe rabonki da al'ada?!"
A firgice Tasleem ta amsa.
"Tun farkon dawowata da na yi wankan biƙi. Amma Mami ai shayarwa nake yi, shi ne dalilin rashin ganin al'adata."
Mami ta ɗan yi jim tana lissafawa, kai ba za ta taɓa yarda ba, hankalinta ba zai kwanta ba idan har ba bincikawar ta yi don kanta ba. Wannan yasa ta yi kiran Ƙassim a waya ba shiri ya zo. Su Jannat dai sun yiwa Mami caa wai akan me take zarginta ita dai shiru kawai ta yi. Har Ƙassim ya shigo ta ba shi kudi ya amso mata Pt-strip ba ta ko sauraron zantukan su, Anna har da su zaginta wai tana zargin ɗiyarta da bin maza alhalin tana idda? Ita dai ba ta tanka ba, Tasleem kuwa shiru ta yi ba ta ce uffan ba. Suna nan hira na gudana tsakanin Anna, Jannat da Futuha har Ƙassim ya kawo aiken. Mami ta karɓa ta ce ya fice, da kanta ta titsa ƙeyar Tasleem har bandaki. Tasleem a dole ta bi umarnin Mamin don itama tana son tabbatarwa, ana yi kuwa sai ga ranƙwalelan shaidar positive ya nuna a jiki. Mami ta kusan sakin ihu a bandaki, ciki dai ciki? Toh uban waye ya yiwa Tasleem din ciki?
A haukace ta ƙara tambayarta cikin fita hayyaci.
"Don ubanki wani abu ya shiga tsakaninki da Babandi ne?"
Ta kasa magana, jikin Tasleem ya hau rawa, dama ta soma zargin cikin ne ashe ko ya tabbata. Wannan ruɗewar ta Mami ya sa tsoronta ya daɗu. Ita kam ta shiga uku idan ciki ne ya shiga jikinta. Shirunta kuwa ya tabbatarwa Mami cewa eh, wani abu ya gifta tsakaninta da Babandi. Ai sai ta shiga duka Tasleem kamar an aiko ta, Tasleem har ta fito daga bandakin a guje Mamin na biye da ita har cikin ɗakin. Tana dukan tana tsinewa Babandi. Sai da su Jannat suka riƙe ta gami da yi mata inkiya kar mutane su dawo su ji.
"Wai waye Babandi? Me kike magana a kai? Ciki kuma?"
Anna ta nemi ba'asi a ruÉ—e. Nan Mami ta kora musu bayanin bokannata da yanda suka yi kaca-kaca akan aikin Humaira da Fadeel da ma yanda ta tura Tasleem wajensa har mai afkuwa ta afku.