← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 41 OF 101

Sashe 41

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

***
Tun karfe goma Humaira ta je kasuwa yin cefane bisa umarnin Mami wacce ke ta shirin tarbar Futuha da za ta zo. Tana dawowa kicin kawai ta shiga ta soma shirin girki, tuwon semovita miyar kuɓewa danya wanda ya ji nama da busassan kifi, shi Futuhar ta ce tana muradi sai ko lemun kwakwa. Wuraren karfe ɗaya ta kammala komainta jera a saman tire ta kai falon ta ajiye. Daga nan ta koma dakinsu. Ita ko kusa ba ta wani zumuɗin ganin Futuhar kamar yanda su Ummita ke yi. Tun dawowarsu daga makaranta jin ance tana hanyar zuwa suke faman rawar ƙafa. Ai kuwa ko awa ɗaya cikakka ba su yi da dawowa ba sai ga mota direba ya kawo ta har farfajiyar gidan. Da gudu Raihana ta fice tarbar yar uwarta, itama Ummita ta mara mata baya a nutse take tafiya. Humaira sai ta ja guntun tsaki ta cigaba da danna wayarta tana ganin sabbin likes da comment da sabon hotunan da ta dora na girke-girke suke samu. Ta shagala sosai sai ji ta yi an warce wayar, ta juya da sauri. Raihana ce. Dariya ta yi mata.

"Ki taso inji Mami ku gaisa da Futuha. Ashe Dubai za su wuce da mijinta sati na sama."

Ta É—an yi murmushi, ba ta fiye son kushe su a gaban Raihana ba don haka ta taya murna a fili.

"Kai amma na mata murna, Allah ya kai su lafiya. Muje toh. Bani wayata kuma."

Raihana ta mika mata suka yi dariya. A falon ta iske Futuha zaune, masha Allah ta ƙara ƙiba da kyau, kumatunnan har wani kyalli suke yi. Wani arnen leshi ne a jikinta fari da ruwan toka ya sha aikin stones sai faman baza ƙamshi take yi, hira sosai take yi da Mami. Ƙassim ma na zaune banda Yassar da Dawud wadanda sula tafi Camp a can garin Jigawa. Humaira ta karaso ta gaida ta, ta amsa mata tana yamutse fuska kaɗan daga nan ta maida hankali ga uwarta su na cigaba da hira. Humaira wacce dama ta san a rina kawai sai ta mike ta saci jiki ta koma daki, Ummita ta mara mata baya.

"Ke kuwa daga gaisuwar sai ki taho?"

Harara ta dan watsa mata.

"Idan na zauna me zan mata? Goyata zan yi? Ai dai kinga yanayin amsar gaisuwar da ta yimin ko? Toh ni kuwa marar zuciyar ina ce da zan tsaya?"

Ajiyar zuciya Ummita ta yi.

"Allah ya kyauta, kinsan Allah na yi zaton aure zai sauya su, amma naga har yanzu da sauransu."

Taɓe baki Humaira ta yi ta ce.

"Toh yaushe ma aka yi daren? Ke ta dai samu duniya ne kawai shiyasa abinta ya ƙara gaba. Nifa kinsan ba abin da ke ban mamaki face irin yadda matarnan ba ta yiwa kanta faɗan ta nutsu ba take faman ɗora hotunanta a media. Shi ma mijinnata soloɓiyo da ya biyemata."

Ummita ta kama baki har da É—an waigawa ta ga ko babu wani a kusa da ya ji kalamin Humaira.

"Kinga ki rufamana asiri. Mutum ba shi ya ga zai iya ba? Kar ki manta har da shi din Ogan nata ake wannan taɓargazar kinga kuwa abu nasu maganin a kwaɓe su. Wayewar yanzu ce ta shirme ta zo da haka."

Dariya Humaira ta yi.

"Kenan kema haka za ki yi da Sahabinki ko?"

Duka ta kai mata a cinya.

"Allah ya sauwaƙe, mu aurenmu ko party ba zamu yi ba, walima kawai a cikin gida ta isa. Albarkar auren muke nema. Hum, nifa yanzu duk ya dameni akan zai turo a sanya rana kafin nan da shekara idan mun kammala nayi Candy a yi auren. Wallahi kwanakin nan duk akan hakan muke ta rikici. Na rasa yanda zan ɓullo masa."

Humaira ta mike zaune sosai. A duniya ta tsani ta ga Ummita cikin damuwa ko na sakan, don haka ta ce.

"To me kike jira? Me zai hana ki ba shi wannan damar? Kina sonsa yana sonki fa. Kuma sa rana ba shi ne auren ba, don Allah ki yi shawara da Mami tunda kinga ta san da zamansa, na tabbata za ta goyi da bayan ya turo."

Ummita ta zubamata idanu ta yi shiru cike da damuwa, ga mamakin Humaira kuma sai kawai ta ga hawaye sun soma zuba daga kwayar idanunta.

"Lafiya? A maganata akwai wacce ta maki zafi? Kiyi hakuri don Allah kinji?"

Girgiza kai Ummita ta yi,

"Ko ɗaya Humaira, ke ce dalilin da yasa na kasa ba Sahabi damar turo iyayensa. Wallahi bana jin dadin mafarkaina a kanki kwanakin nan. Humaira na damu da rashin bada ƙofa ga kowane saurayi ya nemi aurenki da kike yi. Ba na so na yi aure na bar ki a wannan halin. Gaba daya na damu."

Shiru Humaira ta yi, toh ita da kamar abin yana damunta kamar kuma ba ta damu ba. Ta ma kasa fahimtar komai sai kawai ta dubi Ummita a sanyaye.

"Kin manta ke ce me nusar da ni idan na ɓata? Ke ce me ƙarfafamin gwuiwa akan imani da Allah a irin wadannan lokutan? Toh ki sani, har ga Allah ba na jin son kowane namijin ba balle na ji son auren a raina. Hakan ba yana nufin wata matsalar ba, ki kaddara lokaci ne, duk sadda na ji son wani a raina, watakila..."

Sai kuma ta ma rasa me za ta ce, kawai sai ta sunkuyar da kai ta riƙe hannun Ummita cikin nata. Karon farko da ta ji tana hawaye, hawaye mai dalili ba wanda ta saba yi a irin gaɓar nan babu dalilin ba. Ummita sai ta ji tausayinta ya lulluɓe ta, Humaira ai itama da zuciya a kirjinta. Dole akwai abin da ke damunta amma ba ta faɗa, ba ta magana sai dai ta yi shiru idan sun taso da zance ta maida su wasu cali cali.

"Ki tayani addu'a Ummita, ina da damuwa amma ban gama gane kan damuwar ba. Ina da abin faɗi, amma zuciyata na kwaɓa ta a koyaushe akan bai kai abin magana ba nayi shiru kawai. Na rasa meke damuna, idan na ce zan zurfafa tunani sai jikina ya hau rawa, kaina ya hau sarawa. Watakila iyakar abin da zan iya faɗa kenan. Nidai ki dinga sanya ni a addu'a."

Ummita ta É—an rungumeta suna kuka. Kowannensu da kalar tunaninsa, dakyar suka rarrashi junansu suka share hawayen.

Sai kuma Humaira ta cigaba da karfafa mata gwuiwa akan ta bari Sahabi ya fito a yi magana. Ta kara da fadin.

"Kinga itama Raihana zan ce ta amince ta bar Imran ya turo. Shikenan sai ku bar min gida na huta."

Ummita ta harareta, ita kuma ta yi dariya tana kokarin danne radadin ciwon kan da take ji gudun kar ta kefa Ummita a wata sabuwar damuwar. Koda Ummita ta fita don amsa kiran Mami wacce ta turo Muhsin, sai ta zame ta kwanta ta runtse idanu tana tauna maganganun da suka yi da Ummitar, hannuwanta riƙe da kan da ke faman sara mata. Tana nan kwance har bacci ya sure ta, Raihana ta zo ta tashe ta akan ta je Mami na kira. Ta ci sa'a zuwa lokacin ya rage ciwon, don haka dankwalinta da ya zame ta maida ya rufe kan ta fita. Anan fa Mamin ta mata umarnin ta shirya za ta bi Futuha don ta taimaka mata da girki abokan mijinta za su je gidan nan zuwa jibi. Kamar ta cewa Mamin a bari mana sai jibin ta je ta dawo, amma ba ta son jan musu da ita kawai sai ta ce toh. Ranta na zafi haka ta shirya ta bi Futuha suka tafi. Tana ji Futuhar na yiwa Tasleem waya wai gatanan a hanyar gidanta, ita dai ba ta ce mata uffan ba sai kallon window da take yi zuciyarta na zafi, wani sashi na zuciyar na kokarin ce mata Mami ba ta kyauta mata ba yayinda wani gefen ke kwaɓarta yana nusar da ita irin kirki da mutuncin Mamin. Bai kyautu ta munana mata zato ba. Da haka suka karasa gidan Tasleem.

***
A yau Murja ta yi niyyar zuwa sashin Fadeel don ta rantse ko ta yaya sai ya saurareta ya ba ta damar amayar da abin da ke ranta ido da ido. Kwanakinnan ko bacci kwakkwara ba ta iya yi tsabar so da tunaninsa da ke neman zautar da ita, wannan ya sa ta zuri takalmanta kawai ganin an yi Magrib tana kuma da tabbacin yana nan ta nufi sashinsa.
Chapter 41 · 0% Book details