Sashe 5
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Duka wannan zancen tana yi ne lokaci guda da sauri tana bincike dirowarta, littafi ta zaro ta dauki jakar makarantarta sai safarta a hannu da takalmi ta kama hanyar fita.
"Toh, sai kun dawo."
Faɗin Humaira, Ummita ta amsa ba tare da ta tsaya ba sakamakon hon din mota da ake faman dannawa. Ganin haka yasa Humaira ƙarasawa jikin windon wanda ake iya hango farfajiyar gidan, ganinsu tayi gaba ɗaya a motar sai Tasleem dake tsaye a waje rike da ƙugu, Ummita na karasawa ta hau ta da masifar wai tana ɓata musu lokaci.
"Allah ya baku hakuri."
Ta ji Ummitan ta fadi sannan ta shige motar da sauri, tsaki Tasleem ta ja ta bita da harara sannan itama ta faÉ—a ciki, direban ya ja suka fice. Ajiyar Zuciya Humaira ta saki ta bar jikin windon, mamaki fal a ranta na É—abi'un Æ´an matan. Ta lura ba su san wani abu wai shi kara da mutunci ba, haka dai ta ture zancensu ta hau gyaran É—akin. Abin ban haushi a saman gadon Futuha daidai da É—an kamfenta da ta cire anan ta bar shi a ajiye, aikuwa haka ta tsallake gadon, ba ta yi karambanin gyara musu gadajensu ba, da ace dai Ummita ba ta gyara nata ba to tabbas wannan kam za ta gyara mata, ita din mutum ce mai mutunta DAN ADAM.
Fita waje ta yi, falon babu kowa hakan yasa ta nufi hanyar kicin da ta nakalceshi tun jiya da Ummita ta tattara kwanukan abinci ta nufi ciki. Anan ta iske wata mata da ba za ta girmi Mami ba tsaye tana goge gas nan ta fahimci ita ce Ladidi. Ta gaisheta a ladabce, matar ta amsa fuska a sake.
"Baƙuwarmu Humaira ko? Sannunki da zuwa, ga abin karinki can."
Ta fadi tana nuna mata wani tireda aka É—ora filet da kofi sai kayan shayi da flask a kai. Humaira ta murmusa.
"Nagode, amma zan sharo dakin sannan na ci."
"Ai da kin bar shi, idan na kammala da nan sai na share."
Girgiza kai Humaira ta yi.
"Babu komai kar ki damu zan yi ai ba wani girma ne da dakin ba."
Ladidi ta amsa da toh gami da yi mata sannu. Tsintsiyar ta nunamata da makwashin shara, ta dauka ta nufi dakin. Sai da ta kammala tas kafin ta koma ta wanke hannu ta dauki abin karin ta koma daki don ba ta jin za ta iya ci a falon. Bayan ta kammala ne ta fito da niyyar maida kayan kicin suka yi karo da Ladidi.
"Yauwa, ki je inji Alhaji wai za ku yi sallama da Kawunki zai wuce."
Ladidi ta karɓi kayan hannunta ita kuwa jin haka jikinta ya yi sanyi, ta koma dakin ta dauki karamin mayafinta ta yafa a kai. Falon Abban ta nufa, Kawun ne kadai a ciki ya yi shiri tsaf na tafiya, sallamarta ya sanya shi dubanta.
03
Ta durƙusa ta gaida shi, ya amsa sannan ya ce.
"Toh Shatu, ni zan koma. Ina fatan zaman nan zai maki dadi fiye da rayuwar da kika yi a Maine. Ina kuma roƙonki da ki zauna da kowa lafiya, kamar yadda suka karɓeki da hannu bibbiyu, kema ina son ki rike su haka. Gidan mahaifinki ne, nan ɗin dai shi ne gatanki, ba ki da sama da nan. Sannan don Allah ki zama mai hakuri, na sanki sarai muddin aka taɓo ki ba kya kai zuciyarki nesa. Abu na gaba, kar ki sake ki bada kofar da za'a ga wallenmu, a ga kamar mun gaza a wurin ba ki kyakkyawan tarbiyya a iyaka zaman da kika yi hannunmu. Sannan addu'a, ki yawaita addu'a da ibada in sha Allah sun ishe ki."
Humaira wacce tuni fuskarta ta yi jage-jage da ruwan hawaye ta sa hannu ta share su. Gani take yi tamkar shikenan fa za ta yi nesa da asalin garin da aka haifeta, shi kenan ganin Kawu da Tanti Hafsatu matarsa zai yi wuya a gareta.
"Nagode Kawu, in sha Allahu zan kiyaye abin da ka ce. Amma ai Abba zai dinga bari na naje maku wataran ko?"
"Me zai hana na bar ki Mamana?"
Jin maganarsa gaba daya suka dub shi, sam ba su san ya shigo falon ba balle kuma tsayuwar da ya yi a bakin ƙofar da za ta sada shi da sashinsa na ainahi. Ya karaso da murmushi saman fuskarsa ya zauna, ta gaishe shi, ya amsa.
"Ban maki alƙawarin nan kusa ba, amma da yardar Allah duk sadda na tashi aurar da ke, zan kai ki har Maine ki kwana biyu. Nidai fatana yanzu shi ne ki saki jikinki ki zauna da mu bisa kauna. Kin ji ko?"
Ta gyaɗa kai tana murmushi mai dauke da kunya jin wai Abbanta ya ambaci aure. Ita duka nawa ma take yanzun a shekarunta goma sha huɗu? Koda dai, akwai sa'anninta su Murja, Fatsima da ma sauransu wadanda duka an aurar da su a can. Tashi tsaye da Kawun ya yi ne ya maido ta hayyacinta. Ta mike itama, Kawu suka yi sallama da Abba. Daidai nan Mami ta shigo da sallama, tana sanye da dogon hijabi har ƙasa, gaida Kawu ta yi sannan ta yi mishi sallama. Sai a sannan Humaira ta gaishe ta.
Humaira ta takawa Kawu har wurin motar Abba inda direban Abban zai kai shi tasha. Tana hawaye haka ta tsaya har Kawun ya shiga motar, hannu ya É—ago mata itama haka har suka fice daga gidan. Ji ta yi zuciyarta ta yi wani irin tsinkewa, haka kurum ta ji wani irin tausayin kanta ya kama ta. Kanta Abba ya dafa da muryar rarrashi ya ce.
"Haba Mamana, kukan fa? Ya isa haka, ba fa rabuwa ku ka yi kenan ba, in sha Allahu zumuncin ba zai yanke a nan ba matukar akwai rai da lafiya, ki kwantar da hankalinki nan ma gidanku ne."
Ta gyada kai, daga haka suka shige gidan.
Mami dake tsaye a windon falon tana kallonsa, itama juyawa ta yi ta koma É—akin Abban hawaye a saman fuskarta wanda ita kaÉ—ai ta bar wa kanta sanin ma'anarsu.
A falon Abban suka zauna yana fadin.
"Bari dai nayi hira da É—iyata kafin na fita aiki ko?"
Ta yi murmushi har sannan yatsunta na saman fuska tana goge ruwan hawaye.
"Ba ni labari toh, meyasa ba ki shiga makarantar boko a can ba? Kawunki dai ya cemin kina zuwa islamiyya har kin yi sauka, na kuma ji dadin hakan."
Ta gyara zama ta amsa a nutse.
"Dada ce ta ce ba zan je ba saboda koda na fara ba lallai na ƙarasa ba. Ta ce kuma faransanci ne."
Abba ya yi shiru, ya gane sarai manufar Dada, wato dai ta san cewa ko ba jima ko ba dade ranar nan za ta zo da Humairar za ta dawo hannunsa, sai dai ya so ace ko na faransancin ne ta yi, da irin haka biyu babu. Ya tuna shawarar da Mami ta ba shi a daren jiya da suke maganar karatun Humairan.
_"Zai fi dai ka sanya ta a inda za ta koyi sana'a koda kuwa na girke-girke ne, kasan can idan ma ta yi karatun faransanci ne, nan kuwa turanci ake. Zai iya ba ta wahala."_
Toh shi ɗin ma dai ya ga hakan ya fi mishi sauƙi, yanzun ma dubunnan da yake fitarwa na karatun yaran kaɗai sai godiyar Allah kawai, ina kuma da ace ya sanya Humaira wacce ya tabbatar kafin ta fara sai an yi mata lesson a gida sosai, ɗaukar karatun ne ma abin tunani, bai san ya kaifin kwakwalwarta yake ba.
"Abba."
Ya tsinci muryarta wanda hakan ya katsemishi tunani.
"Na'am Mamana."
"Abba meyasa ba ka taɓa zuwa ka gan ni ba? Meyasa ko a waya ba ka damu da kira mu gaisa ba idan ma aiki ne ya tsare ka?"
Ya tsare ta da ido, yanzun ya gama raina kaifin kwakwalwar yarinyar, sai dai ya sha mamakin tambayoyinta duk kuwa da ya sani lallai ne dama watarana ta yi mishi su. Sai dai bai tsammace su nan kusa ba. Dogon numfashi ya ja ya furzar.
"Kiyi hakuri Humaira, eh na yi maki laifi amma hakan ba wai yana nufin ban damu dake ba ne. Sai dai nayi hakan bisa alƙawarin da na ɗaukarwa mahaifiyarki wanda hatta da bayan mutuwarta ban karya shi ba."
Cikin sauri ta ce.
"Wane alƙawari?"
Ya yi shiru sai kuma ya É—ago da niyyar magana, muryar Mami ta katse hanzarinsa.
"Wai nikam dai yau Abban yara ba ka da niyyar fita ko? Gashinan har goma ta gota."
Suka dubeta, a ɓangaren Humaira ji ta yi gaba ɗaya zuwan Mamin bai burgeta ba, sai da aski ya zo gaban goshi tana shirin ta san ta ya ya aka haihu a ragaya lokaci guda kuma Mami ta yi mata katsalandan. Mami kuwa ganin hankalin Humaira ba ya kanta sai ta girgizawa Abban kai cike da damuwa. Abba shi din ma jinjina kan ya yi, ya fahimci manufarta. Don haka ya dubi Humaira da murmushin yaƙe.
"Af, kinga na sha'afa har lokaci ya ja, kar ki damu Mamana, muna tare ai yanzu, a kowane lokaci idan na samu dama da kaina zan yi kiranki mu yi hirar nan kin ji ko? Yauwa Maminki ma ta ba da shawarar a sanyaki a makarantar koyon girke-girkenku na zamani, ina fatan za ki so hakan?"
Duk da yanayin rashin jin dadin da take ciki sai da ta yi farin ciki da hakan. Dama tana da son girki, ko a can gida ita ke yiwa Dada dahuwa daga lokacin da ta soma zama budurwa. Ta kuwa saki fuskarta har wushiryarta na fitowa muraran.
"Eh Abba ina so."
Abba ya dubi Mami suka yi murmushi, Mamin ta karaso ta dubi Humaira.
"Yauwa Æ´ar Abbanta, kin ga da girki adon mace ce. Kuma na tabbatar za ki iya sosai idan kika mayar da hankali. Ana samun alheri sosai da girki. Kar ki wani damu idan ba ki yi boko ba, da yawa babu bokon amma sun samu ci gaba ta fanni da dama a rayuwarsu."