← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 73 OF 101

Sashe 73

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Ai ka ji abin da nace. Fisabilillahi ta yaya yarinya za ta tashi cikin gida babba kamar haka, miji ya yaudareta ya soma kai ta wuri mai kyau daga baya kuma ya sauya mata muhalli zuwa ƙasƙantaccan wuri sannan ta dawo da kokenta ta sanar da mu amma mu kasa magance mata mu ƙwatar mata haƙƙinta? Wannan yanzu daidai ne a wurinka?"

Abba ya dan yi jim yana duban Mami, ya lura tun lokacin da suka tattauna a ɗazun dangane da batun tsaida ranar auren Humaira da Fadeel take tattare da rashin walwala ya kuma fi kyautata zaton rashin sanar da ita kan lokaci ne ya jawo hakan amma kuma sabon zancen da ta yi a yanzun shi ya sa shi tunanin damuwarta kala biyu ne. Wato har da lamarin Futuha. Uzuri ya yi mata ganin bai taɓa samun matsalar ja in ja da ita ba har kuwa a shekarun baya da ya je mata da batun ƙarin aure. Can dai ya nisa ya ce
"Idan dai muhallin da diyarki take ciki shi ya zama dalilin ɓacin ranki shikenan, gobe zan je naga gidan bisa adalcin da kika nema."

Duk da haka ba walwala ta dora ƙorafinta na gaba.

"Sai na biyu, idan har ni Maryam kana yimin kallo na matsayin Uwa a wajen Humaira ba mariƙiyarta ba, ka janye batun auren Fadeel da ita saboda ina da wanda na zaɓa mata ya kasance abokin rayuwarta."

Maganar ta shiga kunnuwan Abba a bazata, sai da ya yi É—an shiru na lokaci kaÉ—an yana jin muryar Mamin na masa amsa kuwwa cikin dodon kunne.

"Maryama, kinsan abin da kike faÉ—i kuwa?"

Ta dube shi tsakar idanu, ta koma Maryam dinta ta Agadez sak wacce ba ta ragawa kowa balle kuma ganin kowa da ƙima ta ba shi amsa kanta tsaye.

"Yes Isuhu, ni Maryam na faÉ—i na yiwa Humaira mijin aure. Idan kuma kana son nunamin ni ban isa da ita ba saboda ba ni ce uwarta ba toh bismillah."

*_Aikinki akan yarinyar ya ɓaci gaba ɗaya kuma ba komai ya jaza hakan ba face samun tsayayyen matashin da yake tsananin sonta kuma ya jajirce wajen yi mata addu'a da ma koyamata yanda za ta ƙarfafa ibadunta.*_ *_Ina mai tabbatar maki Hajiya Maryam matukar kika bari auren Fadeel da Humaira ya afku toh ki tabbata rushewar dukkan tubalin ginin da kika dauki tsawon lokaci kina ginawa zai afku._*

Waɗannan maganganun na Babandi su ne suka ƙara assasa wutar ƙiyayyar Fadeel a zuciyarta, har shi din waye? Me ya taka da zai iya ɓata mata ɓoyayyen shirinta? Yau dai gashinan a sanadiyyar baƙin nacinsa ya soma maida mata hannun agogo baya, ta soma fiddowa Abba ainahin kalar Maryam din da bai taɓa sani ba. Daga sama ta ji muryar Abba.

"Ki faɗi ƙwakkwarar hujjarki koda kuwa guda ɗaya ne tak, ni kuma idan na duba ƙarfinta na maki alƙawarin zan yi yanda kika ce koda kuwa zan ji kunyar mutanen da bani da tamkarsu a yanzu wato iyayensa."

Kai tsaye ta ce.

"Saboda na yi mata miji, sannan ita kanta Humaira ba ta sonsa."

Cikin É—an haÉ—e gira Abba ya ce.

"Wannan biyun da kika lissafo ba su da matsuguni Maryam, eh tabbas ke kike riƙe da Humaira kuma kin yi abin a jinjina maki kuma a ƙara sonki dominsa kamar yanda wannan ya ƙara siya maki daraja da ƙima da ma kauna a zuciyata, amma fa ki sani, ni ke da haƙƙin yiwa yarana zaɓin miji kaf dinsu, soyayya kuma ina da tabbacin soyayyar da yaron ke yi gareta zai isa su rayu cikin aminci da kyautatawa. Ina kuma da tabbacin in sha Allahu koda a baya ta furta ba ta sonsa, a yanzun ko don irin halaccin da yake kan nuna mana shi da iyayensa, ta sauko daga dokin..."

"Ka ga Yusuf ya ishe ni hakanan! Na rantse maka muddin ba ka janye kudurin aurawa Fadeel Humaira ba ni Maryam ba zan ƙara kallonta da idanun rahama ba saboda ka nunamin ba ni na haife ta ba kuma ban isa na zartar da hukunci a kanta ba."

Ran Abba ya ɓaci, yau duniyar gaba daya ta yi masa ƙunci. Wannan wane irin tashin hankali ne haka kuma daga wajen wacce bai taɓa zato ba, wacce koyaushe sai dai ta kwantar masa da hankali idan ya shiga irin wannan yanayin. Meke faruwa ne haka?

"Wace irin ƙiyayya kike yiwa Fadeel haka Maryama da har kika kasa tankwara zuciyarki ki san da wanda kike magana?"

Mami ta kasa tankawa saboda ɗacin zuciya, ji take yi kamar ta shaƙo wuyansa ta kashe shi ko ta huta da wannan zazzafar ƙiyayyar da ta kwashi shekaru tana dannewa a ruhinta har sai da tura ta kai bango. Amma sai ta zaɓi ta miƙe kawai ta fice ta bar masa dakin. Ranar dai haka suka kwana kowannensu a ɓangarensa rai a ɓace. Ga Abba mamaki da al'ajabi ne suka lulluɓe shi, to ma waye mijin da take ikrarin ta yiwa Humairar? Shi ɓacin rai ma bai sa ya tambaya ba saboda bai ga amfanin tambayar da amsarta ba lallai ya aiwatar ba. Ga Mami kuwa haka ta yi ta zarya a daki ga dare ya tsala babu damar kiran Hajiya Lubna don kai mata kokenta balle kuma Babandi da take shakkar kira kar ya ƙara sanar da ita wani abin shiga ruɗanin da fargaba. Don haka sai ta ci alwashin sauyawa Humaira ko a fuska, a ganinta ko don kaunar da ta nuna mata a baya zai sa zuciyar yarinyar ta russuna ta hakura da Fadeel ita kuma za ta yi tunanin wanda ya dace ya yi daidai da Humairar su haɗa kafaɗa a wurin aure amma ba tsara ko fiye ma da mazajen da yaranta ke aure ba.

***
Abba kuwa ya cika alkawari domin duk da irin bacin ran da Mami ta ƙunsa mishi a daren jiya sai da washegari ya wanki ƙafa bayan sanar da Yakubu mijin Futuha (wanda ya cilla Abuja saboda yasan za a rina) ya yiwa gidan diyartasa tsinke tare da Mubarak da ya yi masa jagoranci. Ya tarar da mata kusan su biyar cikin shiga ta alfarma sai baza ƙamshi suke su na ta bugu amma ko gezau kamar babu rai a gidan. Ganin dattijon mutum bai sa sun damu da gaida shi ba, gogaggun ƴan duniya ne daga kallo daya sai faman yatsina fuska suke ana taunar cingam har ɗaya na fadin kodai ba nan ne gidan Futuhar Tiktok ba? Sunan da Abba ya ji sun fadi ya yi matuƙar ba shi mamaki, wato dai Futuha har yanzu tana sharafinta a sosha midiya kenan duk da ya hana? Mubarak kuwa da yake tun sadda zai yi jarrabawar karshe ya raba kansa da soshal midiya ya sa ko bayan dawowarsa bai damu da leka Tiktok ba kamar yanda bude buden status ba ɗabi'arsa ba ce hakan ya ƙara dalilin da bai san me Futuhar ke shukawa ba.

Kai tsaye Abba ya kira ta a waya, ta amsa da murya ciki-ciki don sosai Abban ke ba ta haushi. Ya ba ta umarnin lallai ta zo ta bude masa ƙofa yana tsaye a bakin kyaurenta. Jin haka hankalinta ya tashi, ga kuma matan Tiktok da suka yi cirko-cirko a gaban gidanta su na jira ta bude, ta rasa uban wa ya ba su adireshin gidanta kuma cikinsu har da Ƴar Snow don ta dauki muryarta ta kuma ji an ambaci sunanta. Babu yanda ta iya hakanan ta bude kyauren cikin rawar jiki.

"Don ubanki shi ne kika shanya mu muna ta buga maki ƙyauren gida? Lallai ai dole ki kasa buɗe mana ƙyauren saboda kin gama cika shegen baki kin yi mana kurin gida. Toh bari mu shiga mu ga uwar dake cikin gidan mu yiwa jama'a bidiyo."

Duk wannan zantukan na fitowa daga bakin Ƴar Snow kuma kishiyarta mai zuwa, da kissa da kisisina ta samu Yakubu ya ba ta kwatancen gidan da zummar za ta je taya ta murna.

Abba ya yi shiru ya kasa magana kamsa har wani sarawa yake yi, wannan tashin hankalin har ina? Ƴarka ta jawo an zageka a gaban idanunka? Mubarak kuwa da ya zo wuya ya daka musu tsawa da ba su umarnin barin wajen tun suna shaida juna. Kasancewarsu tsageru suka hau duramasa ashariya yayinda Ƴar Snow ta bude motarta ta shiga tana masa zagi na uwa da uba, Abba ne ya dakatar da shi daga tankawa har suka ja motarsu suka bar wajen. Futuha kuwa kuka sosai take yi, duk rashin kirki da mutuncinta ba za ta so a zagi iyayenta ba. Yau gashinan sanadiyyarta an zage Abbanta tas a kan idanunsa. Abba ya dago ya dubeta da idanunsa da suka kaɗa, sai kuma ya kada kai ya juya ya nufi mota bayan ya ba Mubarak umarnin ya zo su wuce kar yace mata komai saboda makwafta da kuma masu wucewa duk sun fito gulma har da matan aure. Tun a hanya kirjin Abba ya yi wani irin nauyi da zafi, nan da nan kuwa idanunsa suka soma kakkafewa hakan ya yi mugun tashin hankalin Mubarak kai tsaye ya nufi asibiti da shi. Sai da aka shawo kansa ya dawo hayyacinsa kafin ya kira gida ya sanar da Mami. Hankalinta ya tashi, ko babu komai duk da irin guma mata da ya yi tana son abinta, dalilinsa ne ta aikata duk abin da ta aikata a rayuwa hankali tashe ta sanar da mutan gidan ta yi shirin tafiya.

"Mami ina iya binku?"

Wani banzan kallo Humaira ta samu daga Mamin wanda ya kara sanyata shan jinin jikinta amma tana ji a ranta duk runtsi duk wuya ba za ta iya rayuwa babu Fadeel ba. Ta kara jinsa a rai musamman da ta yi istihara a kan lamarinsa bisa shawarar shi kansa Fadeel din da ya kirata a daren ta kara jin ta samu nutsuwa da lamarinsa. Wannan ya sa ta nufi dakinsu ta a hawayen ciwon Abba da addu'ar Allah ya tashi kafaÉ—unsa.
Chapter 73 · 0% Book details