Sashe 44
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
"Ayi hakuri zuwa lokacin da na faÉ—a. Ni kuma zan yi kokarin samun mahaifinta mu gaisa."
Alhaji ya ji abin wani iri, kamar ya yi magana sai dai ya fasa. Can kuma sai ya ɓige da nasiha akan kar ya biyewa soyayyar shirme da ake yi yanzu tsakanin matasa na wannan zamani. Abin har ya so ba Fadeel dariya don shi kam ya lura kamar ma Alhajin tunaninsa wani wuri daban ya tafi. Da wannan suka rufe babin zancen suka hau tattaunawa akan Hannatu dake shirin zuwa Kano don ganin mahaifinnasu da ta kwashi lokaci ba su sanya juna a ido ba.
***
Anti Amarya ta shiga har ɗakin Murja dake kwance tana juyi, tsayawa ta yi gaban gadon tana ƙaremata kallo rai a kuntace sai kuma ta ja mugun tsaki ta soma magana tana ji tamkar ta shaƙo ta.
"Aikin wofi kike yi fa Murja, na faɗamaki ke za ki wahala a banza muddin ki ka ce ba za ki kokarta ki ɓoye kishinki a kan Humaira ba a gaban Fadeel. Ke ba ma kishin ba, hatta da son da ace za ki yi hakurin dannewa babu abin da ba za ki iya cimmawa ba. Ke an faɗamaki koda ace asirin za ki yi masa zai ci shi idan ba ki kasance gwanar kissa ba? Ai komai ɗan dabara ne. Yanzu kiga, daga ganin hoto gaba ɗaya kin susuce har abinci sai kin yi dagaske kike iya ci? Yanzu idan kuma ace zancen auren kika ji ya za ki yi da ranki?"
Murja ta miƙe zaune, gaba ɗaya idanunta sun kumbura. Ta dafe kirjinta.
"Wallahi Anti ji nake yi kamar kirjina zai fashe, Anti ban san haka kishi yake da tsananin zafi ba sai akan Fadeel. Na rantse a yadda nake jin zuciyata zan iya sa wuƙa na tsire Humaira da ranta muddin aka wayi gari ta kasance matar Fadeel balle kuma har abada hakan ba za ta afku ba idan har ina numfashi a doron ƙasa."
Kausar dake bakin ƙofa wacce ta yi niyyar shigowa don duba lafiyar Murjar da ta ji Anti Amarya na cewa ba ta da lafiya, kawai sai ta ja baya ta juya jin maganganun da suke fitowa daga bakin Murja, iyakar abinda ta ji kenan, koda ace ma Anti Amarya ta yi magana kafin nan toh ita kam Allah bai nufe ta da ji ba. Ita gaba ɗaya gidan ma ya ishe ta, Fu'ad wanda ya je Abuja da niyyar kwanaki uku, sai gashinan har ya cinye satin ya ƙara shiga wani satin. Burinta kawai ta bar gidan ta koma nasu, ita sam ba ta gane rayuwar da ake gudanarwa a gidan ba, Anti Amarya dai lamarinta kamar gaske kuma wasu lokutan takan ji kamar kawai wasan kwaikwayo ne. Ga Murja a gefe wacce kallo dubu idan za su yi wa juna a rana babu abin da take samu a wajenta sai harara. Su Khadija ne abokan hirarta sai kuwa wayarta, sannan Fadeel wanda ba kasafai yake shigowa falon ba. Hakan yasa duk ta ke jin ta a takure.
A daki kuwa, motsin mutum ne ya sa Anti Amarya saurin fitowa, bayan Kausar ta hango lokacin da take barin wurin, ta dawo ciki ta rufe ƙofar. A fusace ta kalli Murja.
"Kin gani ko? Zai wahala idan Kausar ba ta ji abin da muke tattaunawa a kai ba. DaÉ—ina da ke ba kya iya É“oye abin da ke ranki ko na sakanni. Kin san ba mu kaÉ—ai ke zaune a gidan ba amma ki yi ta faman suÉ“ul da baka. Mtsw, don Allah ji yadda kika maida kanki, babu wanka balle kwalliya, akan É—a namiji kamar wacce ba ta yi karatu ba kina son ki zautar da kanki. Ke idan da ace ni ce ke, ai wannan ne lokacin da zan soma shigewa Humaira da hujja. Ki raÉ“e su, ki zama tamkar yar uwarsu, ki yawaita kai musu ziyara daga haka sai ki dinga gano sirrinta. Ke daga haka ma idan ma wani aikin ne sai kiga mun ci nasarar yi mata a sauÆ™aÆ™e mun farraÆ™a tsakaninsu. Æangaren Fadeel ki kwantar da kai ki ba shi haÆ™uri ki nuna masa cewa ke fa kin haÆ™ura da shi tunda ba ya kaunarki. Ki yi iyakar Æ™oÆ™arinki wajen ganin kin danne abin da ke zuciyarki a kansa, ki rage shige masa. Ladabi, rage kulashi da ma ba shi girma matsayin yayanki shi zai sa ki shawo kansa ya sakar maki fuska kamar yadda ku ke rayuwa a baya. Ki nuna masa kin fi shi so da kaunar Humaira, ki koÉ—a ta a gabansa da ma duk sauran kissa da kisisina na mata, wannan kaÉ—ai idan ki ka aikata babu mai zarginki koda nan gaba wani mugun abin da za a yi ya kawo Æ™arshen soyayyar Fadeel din da Humairar. Komai fa É—an siyasa ne."
Murja wacce a farko taje jingine da gado tana dafe da ciki tsabar horon yunwar da take yi wa kanta, ba ta san ya aka yi ba ta miƙe zaune sosai tana ƙara baza kunne ga Antin dake magana ƙasa-ƙasa kamar me raɗa duk domin tsaro da kuma gudun kar wani ya ji su. Anti Amarya na kawo wa ƙarshe ta rungume ta su na dariya, har ta ɗan ji ƙwari a jikinta, sai kuma ta ɗan yi sanyi.
"Amma Anti anya zan iya danne son Fadeel?"
Harararta Antin ta yi.
"Da ya kike rayuwa babu soyayyar tasa? Hakanan za ki danne muddin kina son ki cimma manufarki. Ku yaran yanzu babu kissa ba dabara, sai soyayyar kawai. Toh abinci ma ki dafa shi zallarsa babu wasu sinadaran da zai ƙamsasa shi ya ƙara mishi ɗanɗano ai lami za a ci. Balle kuma soyayya, ai idan kana da kyau ka ƙara da wanka. Ba kashe Humaira ba, ko tsire ta za ki yi da wuƙa a gabansa, wataran ba zai ko kalla ba balle ya ji abin a ransa. Ki soma wannan ni kuma na san inda zan je a yi maki aikin da zuciyar Fadeel din zai huce ya soma sanyi a lamarinki. A hankali za ki mallake shi."
Dariya Murja ta yi cike da jin dadi da annashuwa. Ta lumshe idanu tana jin wani sanyi a ruhinta, amma fa alƙawari ta ɗaukarwa kanta sai ta ɗanɗanawa Humaira azabar da sai ta gwammace kiɗi da karatu. Ba don tsoron kar ta kashe ta da hannunta itama a kashe ta ba, ai da tun a ranar da ta san Fadeel ita yake so sai ta je har gidansu ta shaƙe wuyanta har lahira.
Da wannan ƙarfafa gwuiwa na makirci na Anti Amarya ta samu nutsuwa har ta miƙe ta shige wanka ita kuwa Anti Amarya ta fice a ɗakin. Koda suka haɗu da Kausar a falon, babu abin da Kausar ɗin ta nuna koda wasa kuwa wannan ya cirewa Anti Amarya zargin ta ji tattaunawarsu.
***
MUƘADDARI...
Ummita da Humaira tsaf cikin shiri, gidan Tasleem suka yi shirin zuwa ba ta jin dadi. Bisa umarnin Mami, Humaira ta yi mata romon ɗanyen kifi mai ɗan yaji saboda ta ji daɗin bakinta, ta shirya shi a kwando, suka ɗibarwa Raihana kayanta kala biyu kamar yadda ta buƙata, tun soma ciwon Tasleem ta je gidan ta ɗan kwana biyu.
A hanya su na tafe Ummita na amsa wayar Sahabi tana faman doka murmushi, abin da ba ta saba ba kenan, wato waya a hanya. Asalima ta tsani su fito hanya Raihana ta É—au waya tana dannawa ko kuma amsawa, hakan ya ba Humaira mamaki. Ummita na ajiye wayar ta dube ta.
"Yau ke ce da kanki kike waya a titi? Lallai an gaida Sahabi, daga ranar da ya aiko aka sa ranar aure, shikenan sai soyayyarsa ta ƙara girma a zuciyarki har ta sanya kina karya sharuɗɗan da kika ɗorawa kanki."
Ummita ta yi murmushi karo na barkatai.
"Ke ni kaina yau jin soyayyarsa nake yi har cikin ƙoƙon raina. Kin san Allah, a yadda nake jin Sahabi a yau Humaira, da ace a karshen watannan ma a yi bikinmu da.."
Sauran maganar ta maƙale a fatar bakinta sakamakon wata mota da ta gifta su a guje, idanu waje ta bi motar da idanu. Humaira dake kallon hanya jin Ummitar ta yi shiru ya sanya ta dubanta don ta gani ko lafiya. Ganin hankalinta na wani wurin ya sa ta ce.
"Lafiya?"
Cikin alamar ruÉ—ewa kadan ta ce.
"Wallahi wata na gani kamar Anti Jannat a cikin mota ta wuce."
"Anti Jannat kuma? Ina ce sai jibi Mami ta ce za su taso?"
Ummita dai da har lokacin matar na mata gizo ta amsa.
"Eh, hakane, amma nidai sai naga kamar ita na gani a motar."
Cikin rashin ba zancen muhimmanci Humaira ta taɓe baki gami da ɗaga kafaɗa kaɗan.
"Wataƙila kama ce kawai ba wani abu ba."
"Hakane."
Ummita ta amsa, daga nan suka bar zancen.
Kafin su kai ga tarar abin hawa sai suka ji wani É—an sahu na magana.
"Siii, ina ku ka yi?"
Suka dube shi, ya sha jallabiyarsa ga wani a gefensa matashi cikin ƙananun kaya. Ummita ta zubamusu idanu ba tare da ta ce komai ba, sai Humaira ce ta amsa da cewa Kuntau.
"Ku taho mu tafi."
Har Humaira ta soma tafiya, Ummita ba ta tako ba don haka ta juyo ta dubeta.
"Ki taho muje mana."