← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 23 OF 101

Sashe 23

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Shi kuwa Ibb babu abin da ya sanya shi murmushi illa gani da ya yi Humaira ta ɗan saki jiki da shi tana sanar mishi cewa ai kam daga ranar Musaddam bai ƙara shiga rayuwar ƴar uwarta ba.

"Alhamdulillah. Hakan na da kyau. Sai ki ci gaba da yi mata nasiha. Allah ya ƙara nesanta ta da ire-irensu."

Murmushi Humaira ta yi lokacin da ta ke amsawa da amin. Kallon Fadeel ba ta ƙara ba balle ta fahimci hankalinsa kacokam a kanta yake. Har za ta tafi sai kuma ta kara duban Ibb.

"Yauwa, nikam ranar da abin ya faru, akwai wanda ka ba lambata?"

Fadeel ya yi saurin dubansa, girgiza masa kai ya yi don haka ya dube ta kamar bai fahimce ta ba.

"No, meyasa zan ba wa wani lambarki alhalin ko ni ban taɓa kira ba?"

Ta É—an yi shiru, haka kawai ta ji abin kamar rainin hankali amma ta rasa tsakaninsa da wancan Fadeel din me kiranta a waya wane ya raina mata? Don haka ta ce.

"Ba ka da aboki mai suna Fadeel?"

Fadeel dake tsaye ya ji tamkar ta ci gaba da ambaton sunansa sanadiyyar hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mishi ba. Ibb ya ɗan yi gyaran murya domin ankarar da Fadeel ganin yanda ya harɗe hannuwa a ƙirji yana faman zabga murmushi. Sai kuma ya ce.

"Yau na fara jin sunan gaskiya, wani abun ya faru ne?"

Ta girgiza kai.

"Aa ba komai."

"Humaira."

Gaba daya suka juya ga inda kiran ya fito, Tasleem ce. Futuha kuwa idanunta sun cicciko da kwalla, ji take kirjinta na wani zafi. Mutumin da take kwana da tashi da tunani, shi dai wanda ya gagari kowace budurwa da ma zawarawa a jami'arsu, shi ne tsaye a gaban Humaira kucakar da ba ta kamo sawunta a kyau da hasken fata ba yana mata murmushinsa mai tsada da take ji a ranta za ta iya kashe ko nawa ne ganin ita ta sami wannan damar. Amma a banza gashinan ya na jifan Humaira da shi. Tasleem kuwa ta yi mutuwar tsaye wajen kallon Fadeel, sai yanzu take jin ba son Hamza D take yi ba, son ƙarya ne. Wannan abin da take ji game da Fadeel a yanzun shi ne so, soyayya kuwa ta haƙiƙa.

Fadeel ya nanata sunan da ya ji Futuha ta ambata. Humaira, shakka babu ta dace da masu sunan. Ibb kuwa ganin Futuha ya sanya shi tamke fuska kamar ba shi ke yiwa Humaira murmushin ba. Sai gaba daya matasan suka yi musu kwarjini, ita Futuha da ta yi niyyar wulaƙanta Humairar a gabansu sai ta yi laushi, yayinda Tasleem dama tuni miyan bakinta ya kafe, tunani take irin wadannan tsadaddun ai sai irin su masu zubin larabawa.

Dakyar Futuha ta yi magana.

"Mami ta ce ki wuce ki tafi gida tun da dai kin manta katinki."

Jin haka sai ta ji babu dadi kadan, ta kwallafa ranta a bikinnan ba don komai ba sai na son ta ga yanda tsarin biki yake a nan. Hatta da fuskarta ta nuna rashin jin dadinta.

Tasleem kuwa da sauri ta gaida Ibb da Fadeel har da ɗan ladabin ƙarya. Suka amsa.

"Sorry to ask, ba ta samu shiga wurin event din ba ne?"

Fadeel ya tambaya a sanyaye, tun zuwansu wurin sai a sannan ya yi magana. Humaira ta dube shi, kamar muryar mutuminta na waya, ya kauda kai ya kara shan mur kar ta samu fuskar tambaya. Tasleem da ta kusa shiÉ—ewa jin ya yi mata magana duk kuwa da cewa akan Humaira ne ya sa ta saurin tankawa da wata murya cike da yanga.

"Eh ta bar katin nata a gida ne, so shi ne Maminmu kawai ta ce ta koma tunda ba za ta samu shiga ba."

Humaira ta tsaya kallon ikon Allah kawai, mamaki da haushin irin wannan karairayar murya na Tasleem ya cika ta. Har sai da ta ja guntun tsakin da sautinsa bai fito sosai ba.

"Muje."

Yana  fadin haka ya yi gaba, Ibb ya kalli Humaira.

"Ku je za ki shiga yanzu in sha Allah."

Ta amsa da toh, ta bi bayansa ita da Tasleem, ita kuwa Futuha ta ja burki gefen Ibb. Ya kauda kai tamkar bai san da ruwanta ba.

"Amm, Malam ba ka gane ni ba ko? Ni É—alibarka ce a.."

"Ban sanki ba." Ya tari hanzarinta da sauri, daga nan ya taka ya nufi wurin motarsa ya tsaya. Futuha ido ya raina fata, ta dubi wasu maza a gefe tsaye da wasu ƴanmata da ma matan auren da ba su kai ga shiga ciki ba suna mata dariya, tana kallonsu suka ɗauke kai. Gwuiwa a sake ta kama hanya ta bi bayan su Tasleem, ranta ya yi tsananin ɓaci.  Ita kam ta soma gajiya da wulakancin Ibb, amma za ta yi hakuri tunda Anti Jannat ta haɗa ta da wata ƙawarta dake garin za ta yi mata rakiya gurin wani Malami a yi musu aiki a kansa. Amma zuciyarta na kokwanton aikin don ta ji wadanda sun buga sun kasa a kanshi.

Humaira kuwa na tsaye gefe Tasleem na tambayarta inda ta san su Ibb ta yi banza da ita kamar ba ta ji ba. Hankalinta na ga Fadeel dake magana da ɗaya cikin masu tsaron wurin. Ba ta san ya aka yi ba sai juyowa ya yi wannan karon gilashin da ya rufe ƙwayar idanunsa ya cire, lumsassun kyawawan idanun suka bayyana, suka kusan susuta Tasleem har ba ta san ta ce "Masha Allah." a fili ba sai da Humaira ta ɗan dube ta. Shi kuwa cikin ido ya kalli Humaira ya mata alama da ta zo. Sai da ta karasa dab da  shi kafin ya samu damar magana.

"A sha biki lafiya. A gaida Mami."

Ta ji dadi sosai ganin da ta yi an ba ta damar shiga. Ta kuwa buɗe masa haƙoranta har wushiryarta na bayyana a fili.

"Nagode sosai."

Ga Fadeel shima murmushin ya bita da shi, ji yake kamar ya jawo ta jikinsa ya rungume. Da ace shari'a ta halarta masa ita ma, sai ya sumbaci kuncinta wadanda har gani ya yi kamar su na sheƙi idan ta murmusa. Bai taɓa ganin murmushinta ba sai a yau, sai ya ji inama za su dauwama ta na jifansa da shi.

"Always welcome."

Ita dai ta yi gaba don bai san ba ta jin turanci bane, ta dai tsinci welcome din. Zuwan Mubarak ta ji yanda su Tasleem ke faman welcome welcome har ta nemi fassararsa a wajen Ummita. Babu wani iyaka kuwa aka bari ta shige, tana ɓacewa ganinsa ya maida gilashinsa. Ganin Tasleem tsaye tana kallonsa ya dauke kai, har zai wuce sai kuma dabara ta faɗo masa. Ya dubeta.

"Gidanku É—aya?"

Ta yi wani farr da idanunta.

"Eh, babanmu É—aya da ita."

Ya É—an jinjina kai.

"Idan ba damuwa, ko zan iya samun full address na gidan naku?"

Ba musu jiki na rawa ta hau yi mishi kwatance, ta kara da fadin.

"Ko na ba ka phone number dina kaga ko da ace ba ka gane ba sai na yi maka bayani ta waya idan ka tashi zuwa."

Kamar ya ce aa, sai ya tuna ba lallai ya samu cikakken bayani daga Humaira ba dalilin haka kawai ya amince. Wayarsa ya ciro ya miƙa mata. Tasleem ji ta yi kamar ta daka tsalle ta yi rawa da juyi, hannunta har rawa yake yi. Ya dubi yanda take danna wayar cikin rawar jiki ya ɗan taɓe baki. Ya fahimci inda ta dosa kwarai amma ya basar. Babu gurbin wata ɗiya mace a rayuwarsa, madallah da Humaira da ta ciri tuta har ta yi nasarar sace zuciyarsa.

Ya karɓi wayar kafin ma ya tambayi sunan da zai yi saving da shi ta riga shi.

"Sunana Tasleem. Kar ka manta ka yi flashing É—ina kaga koda ka kira zan gane kai ne saboda ban fiye É—aga unknown number ba."

Bai sake kallonta ba kuma bai tanka ba ya fice yana zura wayarsa cikin aljihu. Ta bishi da kallo kamar ta haɗiye shi. Futuha ita kuwa tuni ta shige ciki saboda kunyar yanda Ibb ya yi watsi da ita. Ta kuma rantse koda ace son Humaira yake, sai ta yi yanda ta yi ta raba su har abada. Tana ji a jikinta ba lallai ta sami Ibb ba, toh kuwa Humaira ta yi kaɗan ta samu abinda ita din ta rasa shi. A ɓangaren Tasleem kuwa gani take yi kawai ta tsinci dami a akala, ta samu mijin aurenta. A farko har ta amincewa Hamza D da zuwa gaishe da Abba, amma yanzu kam za ta dakatar da shi tunda ga Fadeel nan.

Wannan kenan.

***
Tun daga wannan ranar Futuha ke tsananin sanya idanu akan Humaira. Daidai da wayarta idan ta yi ƙara sai ta yi saurin kallonta ta ga wane ne. Rannan ta titse Raihana sai da ta titse wai wato Ibb ke kiran Humaira amma ta nuna mata sam ba shi ba ne, tsabar ta koyi munafunci.

Raihana rai a ɓace ta amsa.

"Wai ke meyasa kin fiye son kanki ne? Toh koda ace soyayyar ce tsakaninsu ai ke kin fi sauran masu haukar sonsa cin riba tunda ko ba komai ƙanwarki yake aure."

Wannan magana ta fusata zuciyarta nan kuwa ta hau kilar Raihana kamar an aiko ta. Lokacin Humaira na can gidan koyon girkinta. Ita kuwa Tasleem ba ta dawo daga asibiti ba don yanzu su na asibiti an tura su daga makaranta. A falon daga su Muhsin sai Ummita. Hankali tashe Ummita ta ruga kicin ta kira Mami. Ganin abin da ke faruwa yasa Mami dakawa Futuha tsawa. Sai a sannan ta miƙe daga ruwan cikin Raihana, gaba daya fuskarta ta yi tabo. Kuka kawai take da ihun fadin Allah ya isa, raini kam ta daɗe da raina su.

"Wane irin hauka ne wannan? Kashe ta kike son yi?!"

Cewar Mami tana duban Futuha dake faman huci. Sai kawai ta fashe da kuka.

"Wallahi Mami ba don kamannin yarinyar nan da mu ba sai ince ba ƙanwata ba ce! Wai saurayina ne Humaira ke so har da karɓar lambar wayarsa suna waya. Raihana ta san komai tsakaninmu, kema Mami kin san shi, wai shi  ne take fatan da ace ya auri Humaira. A gaban idanuna."
Chapter 23 · 0% Book details