Sashe 45
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Jiki a sanyaye kamar ta cewa Humaira su sauya wani ɗan sahun sai ta ji harshen nata ya mata nauyi ga kuma Humaira wacce har ta sanya kai a ciki wannan ya sa itama ta shiga. Sun soma tafiya hankalin Humaira a kwance idan ka cire Ummita da ta yi wani irin la'asar, sun yi gaba kaɗan wani namijin ya tsayar da su ya shiga yana rangaɗa sallama. Sallamar da ya yi ne ya sa Ummita ɗan samun nutsuwa, ko ba komai ai ba za ka yi tunanin cuta daga wanda ya nemar maku amincin Allah ba ku ka amsa. Gudu sosai ɗan sahun yake, Humaira na ta ɗan yiwa Ummita hira jifa-jifa, ita kuwa ta kasa nutsuwa sam, hankalinta rabi na ga kallon hanya da kuma gilashin ɗan sahun wanda ke kallonsu jifa-jifa suna hada idanu da shi. Ba ta san ya aka yi ba, ita dai ta kamar na kusa da ita ya fiddo wani hankicif, kafin ta yi aune ya hura mata a fuska, Humaira ma ta juyowa kafin ta kai ga wani yunƙurin ya shaƙa mata, ji kake yaraff, sun lafke bacci mai tsawo ya ɗauke su.
****LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*
*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*
09034973645
Ummita ce ta soma farkawa, a hankali ta shiga murza idanunta da suke yi mata dishi-dishi kafin ta buɗe su tarr cikin ɗan tsurkukin ɗakin da babu komai ciki. Daga wata ruɓaɓɓiyar fanka wacce kallo ɗaya za ka tabbatar da ba ta aiki, sai ko shimfiɗaɗɗiyar katifa wadda da ita da babu duk ɗaya tsabar yamutsewar da ta yi ta rabe biyu. Duk dai a ƙokarinta na son tunano abin daya faru ta ci gaba da bin bangon ɗakin da kallo wanda duk ya yi jirwayen ruwa ga yaana da gizo-gizo da suka cika lungu da kusurwarsa. Sai ko wata ƙofa wacce daga ƙasanta gaba ɗaya ta rarake har kama iya hango ruwan jirwayen banɗakin da ya kwanta har ya rine. Ban da tashin zarni da wari babu abin da ke fitowa daga cikinsa. Ta kuma miƙe tsaye a razane, ta tuna komai, su na hanyar zuwa gidan Tasleem ne su kai wa Raihana kayanta sai ko saƙon Tasleem din na girkin da aka yi mata. Toh nan ina ne? Ya aka yi suka ƙare anan? Fuskokin matasan nan uku ciki har ɗan sahun suka zo mata tarr tarr, da sauri ta nufi windon dake ɗakin, a buɗe yake sai dai an zagayeshinda wasu irin ƙarafana masu nauyi, ciyayi ne cike a wurin har ba ka iya hango bangon dake waje. Ta juya ga Humaira da har lokacin hodar ba ta sake ta ba ta shiga jijjiga ta tana kukan tashin hankali, ga jikinta da ke rawa ta ko'ina.
A ɓangaren Humaira kuwa, ji ta yi kamar a can wani nisan wuri Ummita ke kiranta, a hankali ta buɗe idanunta tana kallonta dishi-dishi. Sannu-sannu kuma har ta dawo hayyacinta ta fahimci dagaske ne dai Ummitar ke kwala mata kira. Ta miƙe zaune tana ambaton innalillahi. Irin yanayin da Ummita ta shiga, shi ta tsinci kanta a ciki. Da rawar murya ta ce.
 "Na...nn..nan ina ne?"
Ummita dake hawayen itama girgiza mata kai ta yi hankali a tashe.
"Ban sani ba Humaira, ban san ina muke ba. Mun faɗa hannun mugaye azzalumai, jikina tunda muka fito yake ba ni cewa babu alheri a tafiyarnan amma ƙaddara ta riga fata. Na so na ce maki kar mu shiga dan sahun nan ban yarda da su ba amma.."
Sauran kalaman Ummita suka maƙale a fatar bakinta sakamakon bankaɗo ƙofar da aka yi da ƙarfi aka sanyo kai cikin ɗakin. Mutum biyu ne cikin samarin, da matuƙin napep ɗin da kuma wanda ya zauna kusa da Ummita a hanyarsu. Hannun ɗaya riƙe da leda. Yayinda mai napep din ke shan taba hankalinsa kwance yana fesar da hayaƙi suna murmushi, matuƙin ɗan sahun ya ce.
  "Kun sha bacci, sannunku da tashi."
"Ku dubi Allah da annabinsa s.a.w ku yi hakuri ku kyalemu mu tafi. Iyayenmu ba su da kudin da za su bayar domin fansarmu. Ku yi hakuri mun tuba, wallahi komai da ke cikin jakkunanmu ku É—auka halak malak mun bar maku."
Ummita ke wannan zancen cikin rawar baki da murya. Ga kukanta da ta kasa tsaidawa, itama Humaira kukan take yi ta ma kasa cewa komai. Matashin da ya soma magana tun farko, ya kai duba ga na tsayen wanda ya fi shi sirantaka da tsawo, tun murmushin farko da ya yi bai ƙara koda buɗe haƙora ba, shi kuwa na durƙushen ya bi Ummita da kallo sannan ya yi ƴar dariya. Madadin ya yi magana sai ya zuƙi sigari ya busamata a fuskar, ta kauda kai tana tari, Humaira ma ta toshe hancinta. Hannu ya miƙawa na tsayen, ledar ya miƙo mishi ya karɓa ya buɗe ta. Shinkafa da wake ne sai manja da yaji, ya tura musu ledar ya ƙara fesar da hayaƙin sigari kana ya ce.
 Â
  "Ga food ku eat. Kin gane bana son musu, if you follow za rules here, you will ji dadi sosai. If you break oza, za ku yi dana sanin haihuwar da uwarku ta yi."
Anan ne Humaira ta samu ƙarfin gwuiwar taso mishi cikin ɗaga murya ta ce.
"Sai dai taka uwar ta yi nadamar haihuwarka idan tana raye! Ba dai namu iyayen ba!"
Tana fadin haka a zafafe ya ɗaga hannu ya sauke yatsunsa saman fuskarta ji kake tas! Ya fizgota ya take ƙafarta kafin ya ɗosana mata karan sigari inda hayaƙi ke fita a saman fatar wuyanta, ta saki ƙara iyakar ƙarfinta na azaba, Ummita ta shiga ƙokarin kwace ta tana haɗa shi da Allah da Annabi kan ya yi haƙuri. Don kansa ya sake ta, wurin kuwa nan da nan ya yi jazur ya ja ruwa.
"Ke har kin isa na zageki ki rama don ubanki?! Banza ƴar iska kawai! Kika ƙara yimin irin wannan kuskuren da shishshigin sai kin raina wayonki."
Ya ƙara ƙudundumo ashar ya watsa mata, har ya sa kai zai fice ya dawo da baya ya sanya ƙafa ya murje abincin ledarnan har ya baje a ƙazantaccen tayils din wurin. Ya dubi wanda suke tare ya soma magana da muryar ƴan daba.
 "Kai Bad boy, koda wasa kar a ba su abinci da ruwa har sai don kaina na baku iznin haka. Ƴan wahala kawai."
Daga haka ya sa kai ya fice, wanda aka kira da Bad boy ya watsamusu mugun kallo sannan ya bi bayansa gami da maida ƙofar ya rufe gam da muƙulli. Su na tafiya Ummita cikin kuka ta ɗago Humaira tana duba wajen da aka sanya mata wutar sigari. Humaira hawaye kawai ta ke yi idanunta a runtse ga raɗadin da ya addabe ta.
"Kiyi hakuri Humaira, don Allah ki kai zuciyarki nesa har mu samu kuɓuta daga hannun waɗannan azzaluman."
"Toh." Shi ne amsar da Humaira ta iya bayarwa kawai, daga haka ba ta ƙara ko harafi ba saboda azaba. Ummita ta yi mata tofi a wurin sannan suka yi zaman shiru sai ambaton Allah da suke faman yi.
***
 Mami suna tare a kicin ita da Ladidi, abinci suke ta hadar-hadar shiryawa na dare tana ta mitar zaman da su Humaira suka je suka yi a gidan Tasleem alhalin ta ce musu kar su jima.
"Gashinan yanzu har an fara kiraye-kirayen sallar Magriba, itama gwanar duk da na gargadeta kar ta bari su yi zaman hira da mutuniyar tasu (Raihana) amma ta yi kunnen uwar shegu."
Ladidi ta yi Æ´ar dariya tana goge kwanukan da ta wanke don yin kwasar tuwo.
"Ai fa kam, ƴanmatannan naki uku idan suka haɗu a wuri sai haƙuri. Ji suke yi kamar ba su taɓa zaman hira ba a duniya sai a lokacin."
Mami ta buɗe baki za ta yi magana sai ga Walid ya shigo da gudu riƙe da wayarta, a bayansa kuwa Muhsin ne.
"Mami Mami! Anti Tasleem tana kira."
Wayar a lokacin har ta katse, Muhsin yana kawo ƙarar Walid wai game yake ta yi har ana kira yana katsewa. Mami ta ɗan yi musu tsawa akan suf fice a kicin ɗin su ba ta wuri. Ta na kokarin dannawa Tasleem din kira sai ga kiran Raihana ya shigo, ta ɗaga ta kara a kunne.
"Raihana, yanzu nake shirin kiranku, maza maza ki cewa yarannan su dawo. Ku idan ku ka samu hira ba ku san dare ba ya yi ku haƙura ko?"
"Mami su wa kike magana? Ai kiran ma da Sis ta yi maki kenan ta ce kodai ta cire rai ne ta sanya Yaya Hamza ya yi mata odar wani abun? Nidai tun É—azun ma na kikkira wayoyin su Ummita a kashe."
Mami ta fiddo idanu gami da dafe kirjinta, cikin rawar murya ta ce.
"Me kike shirin cewa? Kina nufin wai su Humaira ba su zo gidan ba? Kinsan tun ƙarfe nawa suka bar nan?"
Raihana itama muryarta cikin tsananin ruÉ—ewa da tashin hankali ta amsa.
"Wallahi Mami ba su zo ba."
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Na shiga uku ni Maryam."
Hakan da ta faɗi ya sa Ladidi maido hankalinta gareta, itama gaba ɗaya jikinta ya ɗauki rawa. Mami ta kasa cewa Raihana komai sai kawai ta katse kiran cikin tsananin tashin hankali ta fito falon inda Ƙasim ke kwance saman kujera yana latsa waya.
 "Ƙasim! Tashi ka bi sahun su Humaira! Na shiga uku, tun da rana suka fita a gidannan har yanzu ba su dawo ba."
Gaba ɗaya a ruɗe take maganar, ta kasa nutsuwa balle ta yi mishi bayani yadda zai fahimta. Ba ta jira cewarsa ba ta yi gaba ta nufi ɓangaren Abba amma ina, ta iske ya fice zuwa masallaci. Ta dawo falon inda ta tarar Ƙasim tsaye Ladidi na mishi bayanin abin da ya faru. Shi ma nan take ya ji hankalinsa ya tashi.
 "Amma Mami kodai sun biya gidan ƙawayensu ne?"
Mami wadda gaba É—aya cikinta ya É—uri ruwa ga tsananin tashin hankalin da ya bayyana saman fuskarta ta amsa mishi.