← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 48 OF 101

Sashe 48

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

***
Ruwan sanyi ƙarara aka sheƙa musu a fuska wannan ne ya yi sanadiyyar da firgigit suka farka daga baccin wahalar da ya kwashe su. Idan ka kalle su, ba za ka ce su ne wadannan ƴanmatan Abban ba masu iya ado da kwalliya uwa uba kuma tsafta. Sun rame sun yi baƙi a kwanaki huɗu kaɗai da suka yi a wajen, ga fatar jikinsu da ya yi ruɗu-ruɗu saboda cizon sauro da ma cinnaku. Ummita fama take yi da mugun zazzaɓi, ita kuwa Humaira a kwanakin amai kawai take kwararawa ga gudawa, gaba ɗaya sun zama wasu ƙazamai na ƙarfi da yaji. Suka kai duba ga wanda ya yi musu wannan aika-aikar, wannan dai azzalumin ne mai suna BadBoy. Ya ƙaraso ya ja Ummita kasancewar babu kuzari a jikinta kawai ta tafi luu, ya dakatar da ita ta hanyar tura ta da hannu ta faɗi tim a saman busassan aman da Humaira ta yi. Ya fisgo hannunta ta koma ta zauna kafin ya sa baƙin kyalle ya tamke mata idanu. Humaira da ta kasa koda ɗaga yatsa sakamakon galabaitar da ta yi na amai da gudawa ya koma kanta, ya toshe hanci jin ƙarni da warin dake tashi a jikinta, mari ya kifa mata.

"Don ubanki ke wace iriyar ƙazama ce da ba za ki shiga banɗaki ba. An faɗamaki nan gidan gyatuminki ne da za ki yi mana kashi a wuri? Za ku wa ki raina kanki."

Ya fisgota itama ya ƙullemata idanun. Daidai nan Wizzy ya ɗan leƙo da kai yana mai zuƙar sigari.

"Wai ya ne? Ka tattaro su mu bar nan."

Daga haka ya titsa ƙeyarsu Wizzy na kundumawa Humaira ashar ganin yadda ta yi kace-kace sai tashin hamami take yi. Ya rantse ba za su shiga motarsu a haka da ita ba. Wannan ya sa anan suka ɗauki ledar kayan Raihana dake hannunsu a falon gidan suka damƙamusu a hannu.

"Ku sauya kayan kar ku kuskura ku gwada wani motsi idan ba haka ba sai na ciremaku kai da wuƙarnan." Daga gargadin da ya fito a bakin Wizzy, sai Badboy ya tura Humaira banɗakin da ke falon wanda ya fi na ɗakin da suke ciki kyau shi har da ruwa a ƙaton bokiti. Idanunta ya kunce mata sannan ya fice ya tura ƙofar. Humaira dakyar ta ɗaga rigar da suka bata, doguwar rigar Raihana ce na atamfa sai ɗankwali. Kuka ya kufcemata da wani irin kewarta. Ba ita ta iya saiya kayan ba sai da Badboy ya bugamata ƙofa da ƙarfi ya na zaginta akan ta yi sauri, wannan dalilin ya sa cikin rawar jiki ta shiga rage kayan dake jikinta, ta ɗan watsawa kanta ruwa a gaggauce har da ɗora alwala sannan ta sa kayan ta fito. Itama Ummita hakan ta yi duk kuwa da cewa ga zazzaɓi a jikinta, amma tana buƙatar tsaftar jikinta ko yaya ko don sallah. Itama dai kayan Raihanar ce riga da siket ƴan kanti.

Wizzy ya kallesu su biyun yana mai haɗiyar yawu maƙwat. Shakka babu sun kai a kira su ƴanmatan da za a nuna, ban da ma baƙar wahalar da suka ci ai ya sani sun haɗu ne ƙarshe musamman Humaira da ya kasa ɗauke idanu a kanta. Saƙe-saƙen dake ransa, hakan ne a na Badboy wannan ta sanya shi duban Wizzy.

"Ga nama amma babu damar ci."

Wizzy ya busar da hayaƙi gami da yin wani shu'umin murmushi.

"Akwai ranar ƙin dillanci. Yanzu dai mu yi haƙuri mu ci miliyoyin kuɗaɗen nan idan ya so ko mene ne sai a yi."

Badboy ya jinjina kai, ya ƙulle idanun su Humaira wadanda duk iyakar kalle-kallensu sun kasa gane inda suke. Wizzy ne ya soma fita ya ɗan duba wuri sannan ya ba Babba dake gaban mota umarnin tayarwa daga haka ya sa Badboy fitowa da su Humaira suka tura su cikin motar mai baƙaƙen gilasai suka bar wurin da gudun gaske.

***
Fadeel wanda likitoci suka duƙufa a kansa dakyar cikin taimakon Allah suka samu ya dawo hayyacinsa. Sai dai har lokacin zazzaɓinsa bai sauka ba wannan ta sa suka yi mishi allurai suka ɗora masa ruwan drip ganin gaba ɗaya jikinsa babu kwari saboda aman da ya yi mai yawa bayan farkawarsa.
Ganin ya kasa nutsuwa sai kokarin miƙewa yake yi yana cewa zai je neman Humaira hankulan Alhaji da Ibb wanda tuni ya iso suka tashi, Likita dole ya yi mishi allurar da zai sanya shi bacci.
Bayan fitarsa Alhaji ya dubi Ibb.

"Wai meke faruwa ne? Me ya samu Humairar?"

Ibb ya sanar da Alhajin labarin ɓatan su Humaira. Shi kansa ya jinjina lamarin. Shi tun daga sadda Fadeel ya ce mishi zai yi jiran Humairar ya fahimci irin zurfin da ya yi a kaunarta.

"Toh ban da abin Fadeel, ai ba sanyawa zuciyarsa damuwa ya haifar mishi da ciwo ne mafita ba, mafitar ita ce a yi addu'a sannan a ƙara magana da hukuma don ganin an ƙarfafa bincike."

Ibb ya jinjina kai.

"Hakane."

Suna nan zaune Daddy ya iso tare da Maman Ibb. Anan suke jin silar ciwon, shi ma dai irin hangen Alhajin ya yi. Daga nan ya ce Ibb ya yi mishi rakiya zuwa gidan su Humairar. Shi ma Alhajin ya bi su yayinda Mama da Anti Amarya wacce ta iso lokaci guda da Fu'ad suka zauna anan asibitin.

***
Abba bai yi mamakin ji daga Ƙasim cewa ya yi baƙi ba domin tun faruwar lamarin yake ta samun baƙi daga kan ƴan uwa har abokan hulɗa. Ɗazun ba jimawa ƴan uwan Maman Ummita na Bichi suka iso su ma.
Falonnasa na saukar baƙi ya shiga. Daddy da Alhaji suka miƙe aka yi musabaha da Abba sannan duk aka zauna shima Ibb ya gaida shi. Daga nan kuma Daddy ya gabatar da kansu matsayin iyayen Fadeel yaron wajensu dake neman auren Humaira. Abba ya ji zancen banbarakwai, Alhaji kuma sanin da ya yi cewa Fadeel bai bi maganarsa ba na gabatar da kai ga Abban yasa shi fahimtar komai. Nan ya yiwa Abban bayani cewa ai yaron nasu bai kai ga zuwa wurinsa ba. Abba ya ɗan saki fuska, watakila dai shiyasa Humairar aka ce ba ta kula kowa, kenan tana da wanda ta ke so. Nan kuma aka shiga jajanta batun ɓatan su Humairar, Abba ya ƙara ba su labari daidai sadda Raihana ta zo kawo ruwa kamar yadda Ƙasim ya shaida mata saƙon Abban. Ta shigo da zumɓulelan hijabi idanunta duk a kumbure, gaishe su ta yi. Abba ya bita da kallon tausayawa, sai a kwanakin nan ne ta soma magana amma tun bayan faruwar lamarin ta zama ƴar kallo. Suka amsa gaisuwarta, jin Ibb ya kira sunanta gami da jajanta mata ne ya sanya Abba kuma yarda dagaske dai akwai sanayya tsakanin Humaira da wanda suka kira da Fadeel.

"Ina Yaya Fadeel?" Ta furta tana duban Ibb don tun wayarsu take ta neman layinsa yana ƙara ba a ɗagawa. Ya sanar mata da yana asibiti, tausayinsa ya kamata, ta yi fatan Allah ya ba shi lafiya suka amsa da amin daga haka ta mike ta koma ciki.

Daddy a take ya yi kiran Commisioner na ƴan sanda wanda ya kasance abokinsa ya shaida mishi batun ɓatan su Humaira, nan ya ce ya san da maganar. Ya ƙara roƙonsa akan a tsaurara bincike ko Allah zai sa a dace. Daga haka suka yi sallama, suka yiwa Abba bankwana da zummar za su dawo, shima Abban ya tabbatar musu zuwa anjima zai shiga duba Fadeel.

***
Raihana ta ci karo da Mami a falo, Mami ta ce.

"Su waye baƙin?"

ÆŠan murmushin dole Raihana ta yi.

"Iyayen Yaya Fadeel ne wanda ke son auren Humaira suka zo jajantawa Abba. Shima yana asibiti ba lafiya."

Daga haka ta yi gaba ta bar Mamin a tsaye shiru. Sai kuma can ta ankara ta kai duba ga mutanen dake falon, ƴan uwan mahaifiyar Ummita ne da suka iso daga Bichi sai kuwa yan uwan Abba zaune ana ta jajantawa waɗanda wasunsu a cikin magana suke watsawa Mami habaici da baƙar magana. A ganinsu wannan ba tsautsayi bane, akwai lauje cikin naɗi. Juyawa ta yi ta shige ɗakinta da sauri ta rufe da muƙulli.

***
A wannan daren sai ga waya daga kidnappers din Humaira kai tsaye Abba suka kira. Ya É—aga ba tare da sanin ko su waye ba, lokacin su na tare da makwaftansa da wasu cikin yan uwansa maza ana zaune.

"Da Alhaji Yusuf muke magana?"

Abba ya amsa da sauri.

"Eh, ni ne."

"SharaÉ—i na farko, idan a cikin mutane ka ke ka tashi ka bar wajen. Ko da alama kar ka nuna wani abu da zai sa a fahimci wani abu a saman fuskarka. Ka tashi maza ka koma É—aki muddin kana son yaranka su tsira da rai da lafiyarsu."

Jin haka Abba ya miƙe gabansa na dukan tara-tara, wannan kiran yake addu'ar ji don ya shirya salwantar da duk abin da ya mallaka matuƙar su Humaira za su dawo gida cikin aminci. Hanyar ɗaki ya nufa ba tare da ya da kowa komai ba suka bishi da idanu kawai. Muryarsa har tana rawa ya ce.

"N..a.na..matsa. Ni kadai ne a É—aki."

Wata shu'umar dariya aka saki da ƙarfi sannan aka ce.

"Dakyau! Ka buɗe kunnenka ka saurare mu dakyau! Kana da nan da awanni arba'in da takwas ka kawo kuɗin fansar yaranka miliyan biyar muddin kana son su ƙara shaƙar numfashi a duniya. Idan kuwa ka yi gangancin furtawa ƴan sanda wannan zancen toh shakka babu sunan msu matattu. Kar ka manta muna sane da komai dake gudana a nan. Idan kunne ya ji toh jiki ya tsira."

Abba da tuni hawaye sun wanke mishi fuska yana shirin magana ya ji sun daka tsawa.

"Don ubanku nace ku yi magana da Babanku! Ku tabbatar masa kuna hannunmu!"

Sai kuma ji ya yi muryar Ummita ta zabga uban ihu, sai Humaira mai kiran sunan Abba da iyakar muryarta. Da alama dai wani baƙar muguntar aka yi musu.

Abba ya miƙe tsaye yana fadin.

"Ummita! Humaira! Ku yi hakuri don Allah kar ku cutarmin da ƴaƴa, in sha Allah zan ƙoƙarta cika umarninku."

Jin haka sai aka sheƙe da wata iriyar dariya daga ɗaya ɓangaren sannan aka ce.
Chapter 48 · 0% Book details