Sashe 42
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Yana zaune ya kafe manyan frames guda biyu da aka yi mishi na hoton Humaira da idanu yana kallo. Ta yi kyau matuka, daya tana tsaye ne a farfajiyar Manal Event Centre ranar bikin su Futuha, dayan kuwa wanda ta dauka da sallah ne ba ta san ma an yi hoton ba ta rike kafaɗar Ummita tana dariya mai bayyana wushiryarta. Ta yi kyau ainun, masifar son da yake yiwa hotunan ne ya sanya aka wanko da zummar zai adana duk radda suka yi aure ya kafe su a ɗakin baccinsa. Uzurin bandaki ya kama shi, ya mike ya shige ƙuryar dakin don kama ruwa. Daidai lokacin Murja ta hau kwankwasa ƙofar dakin, tana ji kamar ta tura kanta ciki ko ba izninsa. A yau ta kai maƙura a so da kauna da begen ganinsa.Ganin Fadeel ba shi da niyyar buɗewa sai kawai ta murɗa ta tura kanta falon. Babu kowa, ta ɗaga ƙafa da niyyar bin bayansa zuwa ɗakin, sai wata zuciyar ta kwaɓe ta. Ba ta son ɓata rawarta da tsalle, har ta juya za ta bar falon idanunta ya sauka saman hotunan dake ajiye. Jikinta har rawa yake yi ta karasa ta ɗauka. Ji ta yi kirjinta ya yi wani irin bugu da karfi, numfashinta kuwa dakyar ta iya jawo shi ta furzar. Ita ce! Humaira mai Deelsha's Delicacies, ita ce dai masoyiyar da Fadeel ke so. Kafin ka ce me idanuwan Murja sun soma zubar da hawaye. Maƙoƙon baƙin ciki da tsantsar kishi suka tokare kirji da maƙoshinta. Ta tuna ko ɗazun sai da suka gaisa ta waya da ita, ashe ba ta sani ba da rival dinta take mu'amala? Ji ta yi kwakwalwarta na rayamata kawai ta tarwatsa hoton a ƙasa idan ya so komai ta fanjama fanjam! Aikuwa ta ɗaga a zuciye da wannan niyyar amma ba zato ta ji tsawar Fadeel a kanta. Ya ƙaraso ya fisge hoton a hannunta, murya a ɗage ya ce.
"Me ya kawoki É—akina?! Uban waye ya baki iznin kutsowa ba tare da sanina ba?"
Kamar ta ce mishi Ubanka ne amma ta danne, kishi dai bala'i ne. Ta kasa samun nutsuwa, ta kai hannu ta dafe kai har lokacin kuka take, ko kaÉ—an tsawar Fadeel bai razanar da ita ba. Wannan kaÉ—an ne akan yadda take jin raÉ—aÉ—in azabar kishin Humaira a zuciyarta. Dakyar ta iya tattaro kuzarin da ya yi mata saura ta soma magana.
"Dama akan wannan yarinyar ka ke wulaƙanta soyayyata? Yaya Fadeel ina sonka ka sani amma ka ke nuna kamar ba ka san da zamana ba. Meyasa? Da me ta fi ni? Me za ta nunamin? Wallahi Yaya Fadeel muddin ka aureni zan maka fiye da abin da kake tunanin samu daga wannan yarinyar."
Ransa ya ɓaci ainun.
"Ke a naki tunanin koda ace auren zan yi don kyau ko suea kin kai na aureki?! Toh ke ba komai ba don ba ki da suffar da zan gani har naji kwaɗayin aurenki. Daga yau ina maki gargaɗi ki fita harkata, na rantse maki duk sadda na ƙara ganin ƙafafunki a nan sai na ɓaɓɓallaki. Get out!!"
Ta razana sosai, ga baƙaƙen maganganun da ya fesamata ga kuma tsawa, ta kalleshi tana jin ranta na suya sannan ta kara kai duba ga hoton Humaira kafin ta juya a guje ta fice daga ɗakin. Fadeel ya yi tsaki ya zaune yana jin zuciyarsa na zugi. Da ace yana da ikon fitar da yarinyar daga gidannan da tuni ya aiwatar.
***
 Tasleem ta buɗe ƙofar kyauren, suka shigo. Humaira ta bi ta da kallo, ba laifi itama ta yi kyau ta kara haske. Ta rungume Futuha suna murnar ganin juna, ba ta ko kalli Humaira ba suka shiga ciki zuwa ɗaki suka bar Humaira a falo zaman jira.
 "Shegiya, haka gidanki ya yi kyau?"
Cewar Futuha, Tasleem ta ji zancen kamar zagi hakan ya sa ta ja tsaki.
"Ba dai baƙa kike faɗamin ba ko? Bayan naki gidan an ce ya kere nawa nesa ba kusa ba."
Ta yi dariya.
"Abar wannan zancen, ya ne? Kin ji labarin tafiyarmu ko? Kai Tasleem burina zai cika zan shiga jirgi nayi selfie, na kuma ga wurare da dama irin yadda su Ƴar Snow suke gani su na hoto suna mana yanga."
Baki buÉ—e Tasleem ke kallonta cike da É—umbin mamaki.
"Futuha, anya kina cikin hayyacinki kuwa? Ƴar Snow dai da ta yi maki baƙin ƙazafi ita kike farin cikin za ki zarta? Wallahi ina rabaki da shiga harkar ƴan Tiktok, lallai idan kika sa kanki cikinsu sai kin yi kukan da na sani fiye da na baya."
Futuha tun da Tasleem ta soma magana take faman doka murmushi, ta ba wa ranta cewa kawai baƙin ciki ne ke cin Tasleem saboda a duniya ta fi ta burin hawa jirgi da fita ƙasar waje sai kuma ya kasance ita ce ta samu wannan damar, ta ba kanta lallai Tasleem dai da biyu take wannan sabuwar nasihar.
"Ƴar uwa kenan, ki bar wanda ya samu duniya ya ci abinsa da tsinke, ai komai da kike gani lokaci ne. Wasu ma damar da suka jima su na burinta kenan amma ba su samu ba. Mu kuwa tun da Allah ya kashe ya ba mu kinga kenan sai mu dama kununmu yadda muka ga dama."
Tasleem ta yi dariyar yaƙe.
"Ai shikenan, Allah dai ya kaiku lafiya. Nidai please and please ki yo min tsarabar dogayen riguna."
Futuha ta yi farr da idanu tana dariyar itama.
"Kar ki samu damuwa Æ´ar uwa, ai ke tawa ce."
A falon kuwa, Humaira na nan zaune tana karewa gidan kallo aka yi sallama aka shigo. Ta É—aga kai, wata budurwa ce da ba ta wuce sa'arta ba ta shigo kai tsaye ta nemi wuri ta zauna suka gaisa fuska a sake.
"Anti Tasleem na nan?"
Humaira ta amsa da eh.
"Ok, bari na jira fitowarta a nan. Kema ƙanwarta ce ko?  Na tuna fuskarku da biki, ku uku cikin shiga iri ɗaya aka ce sisters dinta ne."
Humaira ta É—an yi murmushi.
"Eh, ƙanwarta ce."
"Ok, amma ba Uwa É—aya ba? Naga su kamar buzaye ne."
Humaira dai ta É—an yi jim, ta rasa wannan maganganun da ake mata na babu gaira babu dalili. Sai a nan kuma ba ta amsa ba. Budurwar ganin haka ta sauya darasin.
"Allah ba ƙaramin so Yaya ke yiwa Anti Tasleem ba. Akwai wata cousin sister din mu da ke masifar sonsa amma ko kaɗan ya ce shi ba ya yinta, kuma fa ..."
Sauran zancen ya maƙale a fatar bakinta sakamakon fitowar Yayannata daga ɗaki. Humaira ta gaida shi, ya gane fuskarta sarai don takan fito kawo masa abin motsa baki lokacin da yake zuwa zance wajen Tasleem. Ya amsa gaisuwar fuska a sake, daidai lokacin kuma su Tasleem suka shigo falon. Nan aka hau sabuwar gaisuwa da Futuha anan take sanar da shi batun tafiyarsu Dubai da mijinta. Ya yi mata murna kwarai. Daga bisani suka yi sallama har bakin mota suka raka su, sai bayan sun tafi ne suka koma ciki. Har lokacin Hamza bai sakarwa Tasleem ba sakamakon haushinta da yake ji na irin kalaman da ta yaɓa masa. Ita kuwa budurwar ƙanwar tasa mai suna Fauziyya ba wani jimawa ta yi ba, daman shigowar don ta ganewa ƴar uwarta Ramlat irin zaman da ke gudana a gidan Hamza wanda har gobe yana nan daram a ranta. Akwai kuma da yawa cikin yan uwansa masu taya ta kishin Tasleem. Ciki kuwa har da Fauziyya.
***
Daki guda na saukar baƙi Futuha ta ba Humaira, nan ta zauna. Madaidaicin gado ne a ɗakin sai kafet a shimfide da bandaki a ciki. Ya yi ƴar ƙura kaɗan ba ta damu a haka ta kakkaɓe bayan ta idar da sallah ta yi kwanciyarta tana danna waya. Tana nan kusan awanni biyu wuraren ƙarfe tara na dare ta ji shigowar mota. Ba jimawa kuma wayarta ta ɗau ƙara, Futuha ce. Ta ɗaga da sallama, ba ta ko amsa ba ta ba ta umarnin ta zo falo ta gaida Maigidan. Kashe kiran ta yi ta mike tana jan guntun tsaki. Mace ko sanin darajar sallama ba ta yi ba, an yi amma madadin ta amsa sai ta yi share. Hijabi ta sanya ta fito, su na nan falon dake saman, yana zaune ita kuwa tana saman cinyarsa tana zuba ruwan shagwaɓa. Sallamar da ta yi har aka amsa bai sa sun sauya a yanayin da suke ba, Humaira sai ta sunkuyar da kanta domin ba ƙaramin kunya suka ba ta ba. Wannan wace iriyar fitsara ce? Koda dai dama ta riga da ta san wace ce Futuha, matar dake tsayuwa gaban waya ta tiƙi rawa ta ɗora a midiya, ai kuwa ba za ta ji kunyar idanun kowa ba idan tana tare da mijinta. Haka Humaira ta ayyana a ranta.
"Kika wani tsaya daga ƙofa, Malama ki ƙaraso ki gaida shi."
Muryar kamar ba ta Futuha ba don gaba ɗaya ta wani ƙanƙantar da ita irin yadda ta saba idan tana waya da samari a baya. Humaira ta karasa shigowa ba tare da ta kallesu ba ta gaida Alhaji Yakubu, ya amsa murya a sake. Daga haka ta miƙe za ta yi ciki, Futuha ta dakatar da ita ta hanyar nuna mata wata leda akan ta ɗauka ta ci. Ta dauka ba musu ta fice daki. Ita dai mamaki kawai take yi na irin wannan wayewar zamanin.
Tana shiga ta buÉ—e, shawarma ce a naÉ—e a paper sai ko gashin kaza rabi, ta cinye tas don dama yunwar take ji ta wanke hannu da baki ta dawo ta nemi makwanci.