Sashe 55
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
"Ina kaunarki Maryam, Allah ya yi maki albarka ya bar mu tare. Kin cikemin gurbin mace hudu a duniya. Babu abin da zan ce maki sai fatan alheri. Yanda kika ce haka za'a yi, gobe ki shirya zan baku kudi, ku fara da siyayyar, koda zuwa jibi ne kuma sai ki kai É—iyartaki wurin mai maganin. Ina fatan hakan ya yi maki?"
Har lokacin tana murmushi ta gyaÉ—a mishi kai.
"Ya yi ranka ya daÉ—e. Fatanmu Allah ya maidowa yaranmu farin cikinsu."
Cikin jin dadi Abba ya amsa da amin amin.
***
Washegari kuwa hakan aka yi, tamkar ba Mamin da Tasleem ɗiyarta ke kwance gadon asibiti ba, tamkar kuma ba wacce ɗiyarta mace ta farko ba (Futuha) ta kawo mata ƙorafin tashin hankalin da take ciki. Daga fuskarta za ka fahimci kamar a duniya ba ta da wata aba wai ita matsala ko kuma damuwa. Ta saki ranta suka zagaye shoprite da su Humaira da Raihana. Ummita sosai kuwa ta sake ɗin kamar yanda Mamin take buƙata, su kansu sun ji dadin yadda yanayinta ya sauya. A ɓangaren Ummitan kuwa, ta tabbatar domin ta saki jiki ne aka yi duk wannan shiri hakan ya sa ba ta watsawa Mamin ƙasa a ido ba, ta daure ta yakice damuwarta ta saki jiki. A ɓangare guda shima Sahabi na nashi iyakar kokarin ganin ya faranta ran abar kaunartasa. Wannan ma ya yi tasiri kwarai a zuciyarta amma har lokacin wannan baƙar ranar ta ƙi ɓacewa a tunaninta da mafarkanta. Su ne har gidan Hajiya Lubna, sun ɗan jima tare da yaranta a ƙasa inda Mami ta haye saman kafin daga bisani ta sauko su wuce.
"Mami ba zamu leƙa Anti Tasleem ba?" Cewar Raihana. Mamin ta yi shiru. Ganin haka sai Ummita ta sa baki.
"Mami don Allah muje a duba ta."
Humaira kuwa uffan ba ta ce ba, asalima kallon shuke-shuken dake farfajiyar gidan Hajiya Lubna kawai take.
"Shikenan, muje. Yarinyar ce ta ban takaici, kina da ciki don sakarci ki tsaya wani faÉ—a akan kishin banza da wofi."
Su dai babu abin da suka ce. Humaira ta buɗe bayan mota ƙarama ƙirar KIA da Abba ya tsiya ta shiga. Mami ta ɗan bita da kallo sai kuma ta murmusa ba ta ce uffan ba. Ta dubi Hajiya Lubna.
"Shikenan Hajjaju, sai mun yi waya."
Ƴar dariya Hajiya Lubna ta yi.
"Toh Hajiya Mamin yara. A gaida Tasleem din ki ce mata ta sha kuruminta zan zo."
"Ai shikenan. Za ta ji."
Daga haka suka yi sallama.
***
Malamin ya yi shiru yana duban ƙasa, can kuma ya ɗago ya kalli Murja ya girgiza kai.
"Abin da kike so ba zai taɓa kasancewa ba."
Wani malolon baƙin ciki ya turnuƙe zuciyarta. Daƙyar ta haɗiyi miyau mai ɗaci ta ce.
"A yanzu kake nufi ko har a gaba? Kenan Humaira ba za ta kasu ba?"
Malamin ya yi Æ´ar dariya.
"Wane mutum! Inji mutuwar. Ai Hajiya Murja babu wanda ba zai mutu ba. Kuma ni da na isa na duba mutuwar wani ai da nawa zan fara dubawa. Abin nufi kina son ta mutu kada ta auri Fadeel din ko? Toh hakan ba zai taɓa yiwuwa ba."
Ji tayi wani abu mai nauyi ya tsaya a ƙahon zuciyarta. Malamin ya zubamata idanu, ya lura ba ta saduda ba don haka ya sauya zancen.
"Amma fa idan kina so za'a iya nakasata rayuwarta. Zamu iya nakasta ta gaba É—ayanta. Amma da sharaÉ—i, matukar aikin bai ci ba, zai dawo kanki. Kin amince?"
Ba tare da dogon tunani ba ta amsa.
"Eh na amince."
"Murja, ko za ki yi shawara?"
Ranta ya ɓaci sosai.
"Wancan karon haka ka ce min, wannan karon ma kana nema ka tauye ni da faÉ—in haka ko? Toh yanzu ba shawarar da zan yi, ga kudi nan ka yi duk abin da ya kamata."
Ta bude jaka ta ciro bandir na dubu ta dire mishi.
Ya yi murmushi.
"Shikenan, ni nawa aiki. Sauran ke za ki yi da kanki. Dole kina bukatar zuwa inda ita yarinyar take. Ki je ki dawo nan da kwanaki uku."
Murja ta ji kwanakin tamkar watanni a wurinta. Tana jin zuciyarta za ta iya bugawa na yanda Fadeel ke rawar ƙafa akan Humaira, kullum ya zauna da Hannatu a falon Anti to fa hirarta ne kawai.
"Babu wani aiki da za ka yimin akan Fadeel?"
"Aiki kai, ga wannan layar ki tabbatar kin saka a ƙarƙashin katifarsa, muddin ya kwana ya tashi ki ɗauke ki binne. Wannan kwallin kuma ki zizira ki tabbatar kun yi ido hudu."
Ta yi murmushi, duk da cewa ta yi abubuwa da dama ba ta yi nasara a kan Fadeel ba amma hakan ba zai sa ta karaya ba. Ta karɓa ta sa a jaka ta mishi sallama ta tafi zuciyarta sol.
*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*
*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*
09034973645
Misalin bakwai da mintoci ne, Fadeel ne zaune a falon Alhaji tare da Hannatu da Alhajin. Wannan damar Murja ta yi amfani da shi wajen kokarin ganin ta ƙaddamar da shirinta, sai da ta fakaici idanun su Khadija da Abdulmaleek wadanda suke kallo ta nufi ɓangaren Fadeel. Sai dai ta yi mugun mamakin jinsa a garƙame da muƙulli. Ta ciji leɓɓa don takaici kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu haka ta ke ji, sai kuma ta tuno duk abinsa da safe yana barin mukullin ɗakin ya fice don a yi mishi gyara. Wannan ya sa ta yi murmushin mugunta ta juya tana mai kara cin alwashi.
***
Futuha na zaune tana faman cika da batsewa kamar ta fashe, Alhaji Yakubu ya shigo fuskarnan a murtuke ya zauna yana dubanta gami da jefamata ledar dake hannunsa.
"Idan har kina son mu cigaba da rayuwar farin ciki da ke, to ki gaggauta shan magungunan nan, an tabbatarmin zasu yi sanadin zubewar cikin dake jikinki. Idan kuwa har ki ka ƙi, kika dage sai kin haihu da ni, toh shakka babu baƙar rayuwar da za ki fuskanta sai kin sha mamakinsa. Sannan rashin bin umarnina zai yi sanadin da zan yi aure."
"Wallahi ba zan sha ba! Idan kuma aure ne ka yi idan ka isa! Kuma wallahi ka ji na rantse maka matukar ka ce za ka wulakantani ba zan zauna ba sai dai ka sakeni!"
Ya yi wata muguwar kyakyacewa da dariya. Ya nunata da yatsa.
"Ke Futuha, ba ki da hankali ashe? An fadamaki ni Yakubu zan saki mace? Ai babu wannan ranar a duniyata. Zaman aure da ni ya zamar maki dole. Koda bakya so kuwa sai kin zauna da ni. Na dai fadamaki, muddin rayuwarnan mai dadi da na ɗanɗana maki kina so ya ɗore, to sai kin bi umarnina. Idan kuwa kin ƙi zan auro..."
Sai kuma ya yi shiru yana jinjina kai duk a kokarinsa na shanye sirrin dake ransa. Tun su na Dubai ya yi wani irin sabo da ɗinkewa da Sa'a Ƴar Snow, kullum yana shafinta yana jifanta da likes da kuma chatting da suke yi a ɓoye. Tsantsar kalaman iskanci da ma hotunan tsiraicin da take turomasa ya yi mugun hargitsa shi, ba ya fatan ya kusanci zina amma ya sha alwashin aurenta. Ta kuma amince sannan ta ba shi lokaci ya gama cin angoncinsa kamar yanda ta buƙata. Ya fi kowa sanin ƴar tsamar dake tsakaninta da Futuha, ya tabbatar idan zancen ya fasu to fa ba za su kwashe da dadi ba hakan ya sanya shi zaɓar yin shiru.
"Ka auro wa?! Ka faÉ—amata ko ma wacece don ubanta ta yi kaÉ—an ta shigo gidannan!"
Ya mike ya watsamata harara.
"Saboda ke kika haife ni kenan? Titse ni za ki yi na faÉ—amaki ko? Toh sai ki yi da wani."
Yana kaiwa nan ya kama hanyar fita, aikuwa ta yi tsalle ta dire gabansa idanunta har sun kaɗa tsabar kishi da ɓacin rai, cakumar wuyan rigarsa ta yi tun ma ba ta kai ga furta ƙala ba ya cire hannu sai ji kake tas a saman fuskarta.
"Ke! Ashe iskancin naki ya kai haka? Ni kike cakumarwa wuya?! Wannan ya zama na ƙarshe idan kika ƙara mugun gangancin nan sai na nunamaki ba ki da wayo! Banza marar tarbiyya ƴar rawar Tiktok kawai! Mtsw."
Yana kai wa nan ya fice yana gyara zaman babbar rigarsa, dama dawowarsa kenan daga wurin Ƴar Snow, don dai kalamai da rungume rungume wadannan ya sha su kamar ba gobe, ita ta yi mishi rakiyar siyan magani kafin ya maida ta gida da siyayya mai yawa sannan ya dawo gidan.
Futuha ta yi kuka mai isarta tamkar ranta zai fita sai dai ta ƙudurta a zuciyarta Alhaji Yakubu bai isa ya wulakanta ta ba. Sai ta ɗauki mummunan mataki a kansa kamar yanda Mami ta ba ta shawarar ta kwaci kanta da gidanta, to kuwa za ta ƙwata ta ƙarfin tsiya. Gama tunaninta kawai ta ciri waya ta kira wata tsohuwar aminiyarta Aneesa Jafar. Matar aure ce amma tantiriyar ƴar duniya ce domin ko a rayuwarsu ta makaranta tana cikin masu neman soyayyar Sir Ibb duk kuwa da auren dake kanta. Ita din shaida ce a yanda take juya mijinta a gida hakan yasa ta yanke shawarar tuntuɓarta. Tun sadda ta yi aure ba ta ƙara nemanta ba saboda a ganinta ajinta ya fi nata, sai a yanzun da buƙatarta ta taso.
Kasancewae Aneesa ta iya barikanci, ko kusa ba ta nunamata komai ba suka gaisa hannu bibbiyu. Sai kuma Futuha ta warware mata damuwarta. Dariya Aneesa ta yi kafin ta amsa.
"Ai wannan ba matsala ba ce yar uwa, amma ki yi yanda yace. Ke banda abinki mene ciki don kin zubar da cikin wanda ya nuna ba ya son haÉ—a zuri'ar da ke? Kuma wallahi kika yarda kika haihu da shi to ina mai tabbatar maki nan da nan za ki lalace ki zama wata daban. Ki daurewa ranki ki zubar da cikin idan ya so ki kawo kudi mu san hanyar da zamu bi ki mallake shi, yanda ko tsinke bai isa ya tsallake ba matukar ba ki yi mishi izini ba."
Cikin sanyin jiki da kuma É—an nutsuwar da Futuha ta samu ta ce.