Sashe 17
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
"Ko? Kai kuma kana neman ka dakile faruwar hakan."
"Ah wane ni? Ba ni na sanya maka."
Ya karɓi wayar Fadeel da tuni ya buɗe, lambar Humaira ya sa a ciki sai kuma anan ya dafe goshi.
"Oh no, ka ga ko sunanta ba mu sani ba. Da me zan maka saving?"
Jin haka ya lumshe idanunsa yana hasko kyakkyawar fuskar Humaira wacce kumatunta har wani sheƙi suke saboda fushi, ya kuma lura ko ya ya ta buɗe bakinta sai wushiyarta ta bayyana. A hankali ya ce.
"Mrs Fadeel."
"What?" Ibb da kunnuwansa kamar ba su ji ba ya tambaya. BuÉ—e idanunsa ya yi ya dube shi dakyau.
"Yes, haka za ka yi saving lambar."
"Aa, riƙe ka yi da hannunka. Ka gani koda wani abun ya je ya zo, ba za ka kalle ni da shi ba."
"Babu abin da zai je ya zo face alheri. Da yardar Allah ba ta da miji sai Fadeel."
Ya ba wa Ibb amsa sa'ilin da ya sa hannu ya karɓi wayar. Aikuwa da hakan ya yi saving sunan. Ibb dai mamaki ma yake, to kodai ɗan lokacin da ya kwashe ba ya tattare da su ya sauya ne daga yadda ya san shi? Mutum da zancen aure ma ba ya so a yi mishi, daidai da hira idan ta budurwa ce aka ɗauko cikin abokai yanzun gayyar za ta watse a wurinsa don tsam yake tashi ya bar musu wurin yana mitar ba shi da lokacin shirme.
"Sai goben?"
Maganar Fadeel ta katse mishi tunanin, ya sauke ajiyar zuciya.
"Allah ya kaimu. Amma ina mai ba ka shawarar kada ka zurfafa, duk abin da aka zurfafa ana shan wuya a cikinsa. Balle kuma irin wannan faÉ—awar da ka yi lokaci guda."
Madadin ya amsa sai ya yi murmushi ya soma tafiya kawai, sanin da Ibb ya yi shikenan sallamar tasu ya sa shima ya nufi motarsa cike da fatan shi din ma Allah ya kawo mishi mace ta gari ya huta da gorin ƙannensa sun yi aure sun bar shi da Mahaifiyarsa ke yawon mishi.
***
 A can gida kuwa, Mami tun da ta ji wai Humaira ta fita ba da saninta ba gaba daya ta ji ta kasa sukuni. Har ta kasa ɓoye ɓacin ranta ta hau faɗa a falon.
"Wannan wani sabon salo ne da har Humaira za ta sa ƙafa ta fice a gidannan ba tare da neman iznina ba? Me take so na faɗawa Abbanku idan ya tambaye ta?"
Tasleem da Futuha suka kalli juna suka taɓe baki, yayinda Ummita da aka kira tuhumar ko ta san inda take, ta ke gefen kujera a zaune.
"Toh wai Mami, ba Humairar na da waya ba? A kira mana." FaÉ—in Mubarak wanda ke shigowa falon daga masallaci, tun kafin fitarsa Mamin ke faÉ—an fitar har dai ya dawo ba ta chanja zani ba. Ganinsa ne ya sanya su Tasleem nutsuwa. Mamin kuwa dubansa ta yi kafin ta kauda kai ta ja guntun tsaki na takaici.
"Kira na nawa kuma? Wayarta idan ba a kashe take ba to na fi tunanin babu network."
Ya kai duba ga Ummita.
"Ke ba ta faÉ—amaki komai ba?"
Kafin Ummita ta amsa, Futuha ta yi caraf.
"Nima dai ita nake zargi don babu ta yadda za ta fita ace ba ta sanar mata ba. Bakinsu daya wallahi Yaya."
Kallon da ya watsa mata ya sa ba ta ƙara cewa uffan ba, Mami ta ja tsaki karo na ba adadi ta nufi ɗakinta. Ganin haka Ummita ta miƙe ta yi nasu dakin da zummar gabatar da sallar La'asar, ita kanta tunanin da take yi bai wuce na inda Humaira ta je ba tare da neman iznin Mamin ba kamar koyaushe. Tsoronta kar Abba ya dawo ya tambaye ta ace ta fita alhalin ba ta da makaranta yau.
Aikuwa dai sai wuraren biyar da mintoci suka shigo gidan, ko ci kanki ba wanda ya cewa wani a cikinsu. Su Yassar dake zaune cikin abokansu a kofar gidan su ka bi su da kallo.
"Ga uwar girman kan gidannan ta dawo." FaÉ—in wani abokin Yassar yana nuni da Humaira. Tun ranar da ya yi gangancin kulata da sunan so ta ci mishi mutunci yake jin tsanarta. Yassar tsaki ya ja.
"Kai ka so ai dama ka ga kalar nata girman kan, amma ga mata a gari kamar ƙasa ka rasa ta kulawa sai wannan ƴar ƙauyen nijar din?"
Sauran suka yi dariya. Shi kuwa Yassar miƙewa ya yi ya bi bayansu ganin kamar Raihana na sharce hawaye, jikinsa har mazari yake don muddin ya kasance Humaira ce sila to ya rantse sai ya rama mata koda kuwa gaban Abba ne ba Mubarak ba.
***
A falon gidan suka iske su Futuha zaune, sallamar Humaira ta dakatar da Ummita daga shiga kicin, ta dawo cikin falon da sauri don ta ganewa idonta ko ita É—in ce. Futuha da Yasmeen kuwa ido suka bi Raihama da shi ganin yadda fuskarta ta yi ja ga shatin yatsu kwance saman fuskarta.
"Ke, Raihat, me nake gani haka? Uban waye ya mareki?!" Tasleem ta faÉ—i da buÉ—aÉ—É—iyar murya tana kallon Humaira. Humaira da ita dinma kiris take jira ta dube ta dakyau.
"Ni ce nan, ko za ki rama mata ne?"
Aikuwa jin haka gaba daya Tasleem da Futuha suka yo kanta, ta kuwa shiga tarewa, duk wacce ta bugeta sai ta sa hannu ta rama da iyakar ƙarfinta, duk da cewar su biyu ne a kanta, ta yi iyakar kokarinta amma itama ta ji jiki. Ummita ta hau kwala ihun kiran Mami, ga Yassar a gefe da ya ƙi ya tsawatar don dama ya jima da haushin Humaira a ƙoƙon ransa. Raihana na ihun su kyaleta akan ba ita ce ta mare ta ba amma inaa dama sun jima su na dakon rana mai kamar ta yau din hakan ya sa da gayya suka yi biris da ita. Yayinda a ɓangarenta shakkar tonuwar asirinta take musamman da ya kasance Yaya Mubarak na gari, ta sani koda ace Abba bai taɓa lafiyarta ba, shi kam ban da lafiya ma, hatta da wayar da take tunƙaho da ita sai ya raba ta da shi.
Kusan a tare Abba da Mami suka shigo falon. Wata tsawa Abba ya daka da ta sa gaba daya suka saki juna, Humaira gefen kumatunta na fidda jini sakamakon yakushi da ta sha da dogayen faratan Futuha. Su kuwa daga mai riƙe baya, sai mai riƙe gefen fuska da naushin Humaira ya kumbura har ya tasa. Mami zuciyarta ta yi wani iri, ta kasa magana ta yi shiru tana kokarin hadiye abin da ke cinta. Abba ya karaso falon ya dube su gaba daya. Humaira tuni ta durkusa, ganin haka su ma suka durƙusa.
"Mene ne hakan? Wane sabon shashanci ne haka? Ke Humaira wadannan ba su girmeki ba? Ku kuma manyan wofi ba kanwarku ce ba? Duk me ya kawo rigimar ne?"
Humaira ba ta ce uffan ba, Yassar ya yi saurin sa baki.
"Abba ba fa wani abu ba ne, Humaira ce ta mari Raihana har fuskarta ya yi shatin yatsu, shi ne don Tasleem ta yi magana kawai sai ta taso mata da faÉ—a wai ta mara ko akwai shegen da zai rama mata. Kalmar shege ya fusata su suka yi kanta da duka." Murmushi mai ciwo Humaira ta yi lokaci guda hawayen da take dannewa suka zubo samam fuskarta, zubar hawayen a inda Futuha ta mata rauni ya sa ta jin zafi amma ba ta ko damu da sharewa ba don wata azabar ta fi wata, ita daya ta san me take ji a zuciyarta. Ummita ma hawayen take na ganin yadda gaba daya Yassar ya juya magana. Ita kuwa Mami, karasowa ta yi ta É—aga fuskar Raihana tana kallo. Tabbas mari ne, fuskar ta yi ja, ga yatsu kwance ta ko'ina a gefen fuskar.
"Mari?! Mamana dagaske ne kin mari Æ´ar uwarki? Me ta yi maki da zafi har haka da kika É—au hukunci da kanki?"
Raihana nan fa ta shiga zare-zaren ido, Humaira ta kalleta na É—an dakiku, har abada ba za ta tona mata asiri gaban iyayensu ba. Mami ta kai matsayin da ko laifin É—iyarta ta gani za ta iya rufa mata asiri don haka dakyar ta haÉ—o abin fadi.
"Ka yi hakuri Abba. In sha Allah ba zan kara ba."
Nan kuma Abba ya kara fusata.
"Oh, dagasken kenan kin mare ta ko?! Wannan ai hauka ne! Kamar babu manya a gidan? Ke waye ya mare ki?"
Nan ya shiga bude mata wuta, sai da ya gama sannan ya maida hankali ga su Futuha wadanda duniyarsu ta yi dadi, ko babu komai wacce suke yiwa kallon ta fi su a wurin Abban yau ya rufe ido ya wanketa tas kamar zai kai duka. Hakan yasa ba su ji zafin nasu faÉ—an sosai ba. Sai da Mami ta sa baki sannan ya bar wurin. Humaira na ta kallon fuskar Mamin don ta hasaso yanayinta amma ba ta fahimci komai ba sai dai jikinta ya yi sanyi ganin ko kallonta Mamin ba ta yi ba. Hakan na nufin ba ta ji dadin hukuncin da ta yiwa Raihanan ba?
***
"Ban da abinki Humaira, duk son da Mami za ta nuna mana ai ba zai kai son ƴaƴan da ta haifa da kanta ba. Ni ba abin sa ya fi ban haushi irin yadda ba a damu da tambayar inda ku ka je ba. A jikina nake ji ba hakanan kawai za ki mari Raihana ba, akwai abin da kike ɓoyewa. Amma wace rana zai maki? Zai siya maki daraja ne a gun Raihana da yan uwanta kike zato? Babu ɗaya fa, halinsu ne ba na jin za su taɓa sauyawa."
Ummita ke zubo mata zance sa'ilin da suke kicin su na gudanar da girkin dare, awanni kusan biyu bayan afkuwar komai, Humaira wacce tuni ta yi wanka ta sauya shiga cikin riga da siket ƴan kanti ta yi murmushi daidai sadda ta motsa tukunyar miya ta rufe gami da rage wuta. Juyowa ta yi tana kallon Ummita da ta mayar da hankali tana juye farar shinkafar da ta dafa a cikin ƙaton warmer.