← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 4 OF 101

Sashe 4

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Suka ƙarasa ga Mamin, ta zauna a gefe a ƙasa. Duk yadda Mamin ta so ta hau kujerar ta ƙi, haka dole ta rabu da ita. Ummita ta kawomata abincin amma gaba ɗaya ta kasa sakewa balle ta ci, ƙarshe dole dai ɗakin suka yi da abincin bisa umarnin Mami. Nan din ma dai kaɗan ta ci ta ce ta ƙoshi. Hankalinta kuma ya koma ga Kawu da Abba, ba ta gaji da ganin Abba ba, ba ta kuma gaji da jin muryarsa ba. So take ta samu damar da za su yi doguwar hira da shi, tasan dai ba yau ba domin dare ya yi.

Suna nan da Ummita tana ƙara ba ta labari akan zuri'arsu har lokacin sallar isha'i ya yi, koda suka idar kai tsaye falon Abba suka nufa sakamakon kiran da ya yi musu. Nan suka tarar shima Kawu har ya ci abinci ya yi wanka, hirarsu kawai suke yi da Abba wanda shima ya sha doguwar jallabiya ruwan madara. Har Humaira ta zauna kallonta yake da murmushi saman fuskarsa kafin ya maida duba ga Kawu ya girgiza kai.

"Allahu Mai Halitta." Kawun shima murmusawar ya yi, ita kam sai ta yi kasa da kai. Zamansu ba jimawa sai ga Mami ta shigo ta lulluɓe jikinta da ƙaton mayafi. Sai da ta zauna ne ta dubi Kawu.

"Umar, kwana da  yawa. Idan babu Fatima  a gidan shikenan kuma sai zumunci ya yanke? Dama kun raba ni da ɗiyata, toh dama ƙarshen alewa ƙasa, ka ga yau dai ungulu ta komo gidanta na tsamiya."

Kawu ya yi Æ´ar dariya.

"Hajiya Maryam kenan, idan dai kin yarda kin amince da komai lokaci ne, ba za ki ga laifinmu ba. Sai dai kamar yadda kika ce, na yi kuskure kuma na ji kunya da ban tashi zuwa ba sai bayan babu Adda Fatima, Allah ya gafartamusu. Ina kuma neman afuwa."

Gaba daya suka amsa da amin.  Abba ya yi gyaran murya ya dubi Mami.

"Ina yaran nan suka shiga ne wai?"

"Su na can wurin Anna, na rasa me suke yi alhalin na sanar da su. Bar..."

Ba ta ƙarasa ba sai ga su sun faɗo ɗakin kamar daga sama, babu ɗaya cikinsu da ya yi tunanin yin sallama. Yaron ɗazu ne da ya je kiranmu ya shigo a guje ya rungume kafaɗun Abba, wani da ya fi shi tasawa yana biye da shi a gujen. Sai kuwa su Tasleem da samarin nan uku.

"Kai Muhsin, me ya yi maka ne?"

Wanda aka kira Muhsin ya turo baki ya nunawa Abba bindigar ruwa da aka raba gida biyu.

"Ba shi ne ya karyamin bindiga ba. Allah kuwa sai ya biya ni."

Abba ya ja hannun karamin mai suna Waleed ya maido shi gabansa.

"Haba Autan Mami, ya haka? Ba shi hakuri toh."

Da dariya irin na yarinta ya furta kalmar sorry. Abba ya maida idanunsa ga su Tasleem waÉ—anda suka yi É—are-É—are saman kujera ba su ko gaisar da Kawu ba. Fuska ya É—an É—aure.

"Ba ku iya gaisuwa ba ne?"

Jin furucin Abban ya sa suja gaida Kawu ciki-ciki, ba tare da jin komai ba  ya amsa har da nema musu albarkar Allah. Babu wanda ya amsa da amin a cikinsu. Mami ta kalle su ta yi musu alamar su sauko ƙasa su zauna, ba a son ransu ba dole suka zaune a ƙasan kafet kamar dai yadda Humaira da Ummita suka yi. Sai dai Abba ya buɗe taron nasu da addu'a sannan ya gabatar da Humaira a wajensa. Ya kuma gargaɗe su da kar su kuskura ya ji wani zance na daban koda nuna bambanci ne. A karshe ya sa kowannensu ya gabatarwa da Humaira sunansa. Su tara ne cif, Mubarak ne babban ɗan Abban, shi kuwa yana ƙasar Ghana yana karatu, sai Dawud, Yassar, Ƙasim, Futuha, Tasleem, Raihana, Muhsin da autansu Usman da ya ci sunan baban Mami suke kiransa Waleed.

"Humaira toh, yanzu dai ba wanda ba ki sani a Æ´an uwanki ba ko? Sai babban yayanku shi kam sai ranar da ya samu hutu idan ya dawo sai ku gaisa. Ko kuma ma ina iya haÉ—a ku a waya wataran."

Jin abinda ya fadi ya sa ta murmushi, ta gyaÉ—a kai tare da furta toh. Daga haka Abba ya sallame su baki É—aya suka tashi.

A wannan daren dai ba ta samu damar hira da Abbanta ba, ta koma ɗakin da ba ta kauna dalilin yadda suka kaya da masu ɗakin. Mami ta sa aka yi mata shimfiɗar katifa a ƙasa kafin nata gadon da sif ya iso, acewarta. Hakanan ta kwanta, mutanen ba su ƙara tanka mata ba musamman ma Futuha da ta sha ƙasa har lokacin ƙugunta na ciwo. Sun dai sha jinin jikinsu, sun kuma fahimci Humairar ba kanwar lasa ce ba itama.

***
Washegari tun da asuba ta ga ƴanmatan ba su koma bacci ba, ita daman baccin safe ba ya daga cikin ɗabi'unta, a can ƙauyensu daga sun tashi to sannan za'a hau ɗora ruwan wanka da kuma abin kari, wannan dalilin yasa ta kwanta kawai tana kalle-kalle da saƙe-saƙen zuci. Tana kallo suka yi wanka har Ummita, kowannensu ya hau shiri. Ummita da Raihana cikin shigar uniform na makaranta, ita kuwa Tasleem shigar fararen kaya ta yi na ma'aikatan asibiti riga da wando da ɗan ƙaramin hijab. Sun mata kyau kwarai, gogar kuwa, wato Futuha, kayan gida ne jikinta, riga doguwa ta atamfa da ya ɗame ta ɗam ya fiddo da surarta.

"Wai ke Futuha ni ban gane ba, ina mamakin yadda kike rawar ƙafa da jiki duk sadda aka ce kuna da English, ko uban me yasa oho." Faɗin Tasleem kenan sa'ilin da take ɗora agogo a tsintsiyar hannunta. Kafin Futuha ta yi magana, Raihana dake fesa turare a jikin uniform dinta wanda iri ɗaya ne da na Ummita, kalar fari da ruwan makuna dinkin riga da wando sai ɗan hijab da ya rufe kirji kaɗan, dariya ta yi ta amsa wa Tasleem.

"Wai ke ba ki da labarin IBB Gusau? Tab, ai kusan kaf matan department dinsu sonsa suke ban ciremaki matan aure ba, toh itama har da ita a ciki, ba ki ganin kwalliyar ta daban ce."

Futuha ta jefowa Raihana murfin man shafawa, Raihana ta kauce tana dariya.

"Af, akwai ƙarya cikin maganata ne? Ke fa naji kuna hirar da wannan ƙawartaki me wuya kamar mariƙin lema, ni me ma sunanta? Yauwa Khalisat, kina wani koɗa shi kina cewa nan duniya shi kike so."

A fusace Futuha ta nufo ta, Raihana ta sunkuci jakar makarantarta da waya a gefen gado ta fice daga dakin da sauri tana dariya. Itama Tasleem dariyar ta yi.

Ummita kam dama ta fice daga dakin tun da ta zura uniform, dakin su Muhsin ta wuce don yi musu shirin makaranta.

Humaira lumshe idanunta ta yi tana ji suna faman hira tsakanin Tasleem da Futuha inda Futuha ke kara jaddada dagasken dai tana son Ibb Gusau.

"Ke malamin fa ƙarshe ne wallahi, ya haɗu ba zan nuna masa komai ba. Nidai fatana Allah yasa ya karɓi tayina ya aure ni. Wallahi zan jure dukkan wulakanci muddin zai yarda ya so ni. Yau in sha Allahu sai na nemo lambar wayarsa."

"Lallai, kina ruwa kusa da breaker." Cewar Tasleem.

Fuska dauke da damuwa Futuha ta amsa.

"Ai na yi nisa ma cikin ruwan Tasleem, ki dai yi fatan kar Allah ya jarabceki irin yadda ya jarabtan."

Tasleem cike da mamaki ta ce.

"To tsaya, don iskanci kwanakin nan da wa kike waya kike kashe murya kina furta kalaman so?"

Yamutsa fuska Futuha ta yi.

"Mujahid ne, wallahi akan dole nake kula shi, shi ke fa taya ni da attendance da ma test. Kinga kuwa dole ce ta haifar da shiga lamarinsa. ÆŠan taya ni na ci jarrabawa ne."

Suka sheƙe da dariya. Ba jimawa suka fice zuwa falo.

Ita Tasleem nursing take karanta duk ta fi su kwakwalwa da basira, tana da kokari sosai shiyasa wasu lokutan take samun alfarma daga Abba koda zai yi hukunci ba ya tsaurara mata, yayinda ita kuwa Futuha ke karantar Mass Com, ba laifi tana da kokari sai dai matsalar tun zuwan wani matashin malaminsu makarantar ta susuce ta zama shiritacciya. Wannan yasa lokaci guda ta kwaso C.O a zango na biyu a aji na biyu a makaranta, hakan ba ƙaramin ɓata ran Abba ya yi ba. Shi mutum ne da ya tsani asarar kwandalarsa a abinda ba zai kawo mishi ribar komai ba sai asara, hakanan mutum ne mai son abin hannunsa sosai, dakyar Mami ta shawo kansa ya aminta da tura Mubarak karatu, ya kuma ce daga kansa ya rufe, sauran kowanennsu sai dai ya yi a jami'o'in Kasarnan.

Dawud na ajin karshe a jami'a inda yake karantar Accounting, Yassar wanda tare suke tafiya da Dawud din adalilin maimaicin aji da Dawud ya yi a sakandire, shi kam Bussiness ya ke karanta, su biyun tare suke da Futuha a jami'ar Bayero. Sai Ƙasim dake karantar fannin Kasuwancin shima dai inda yake aji na uku a jami'ar Maitama Sule Kano.

Wannan kenan.

Humaira jin É—akin ya yi shiru ta buÉ—e idanunta, ajiyar zuciya ta saki tana mai jinjina wannan rayuwa ta Futuha, shakka babu ta É—orawa kanta wahala, koda dai faÉ—an da ba ruwanka, daÉ—in kallo gareshi. Mikewa ta yi ta nufi banÉ—akin bayan ta É—auki zanin wankanta da brush. Sai da ta wanke jikinta tsaf kafin ta fito ta soma shiri cikin doguwar rigarta Æ´ar kanti ruwan madara, tana daga cikin suturun da Kawunta ke siyamata. A dai fannin sutura daidai gwargwado itama tana da su, sai dai ace ba wasu masu tsada ba ne, ba kuma masu kyawun gaske ba ne idan an haÉ—a da na su Tasleem da ta gansu a jikinsu a kwana É—ayan nan. Tana cikin kwashe shimfiÉ—arta sai ga Ummita ta shigo da sauri, ganinta ta saki fuska sosai.

"Au Humaira ashe kin tashi, kinga mu ma makaranta za mu wuce. Mami tace idan kin kammala ga abin kari can an rufemaki a kicin, idan ma ba ki gani ba ki tambayi Ladidi mai aikin Mami tana falon tana gyara."
Chapter 4 · 0% Book details