Sashe 19
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Ummita da iyakar burgewa yar uwar ta burgeta sai ta shiga murmushi kawai da mamakin kaifin hankali da tunaninta, ta sani ko ita ba lallai ta iya shiru a irin wannan gaɓar ba. Amma ta gwammace kowa ya yi mata kallon rashin kyautatawa akan dai ta bayyana gaskiyar abin da Raihana ta aikata. Sai kuma karar wayar Ummitan ya katse tunaninta. Da sauri har su na rige-rigen ɗauka ita da Humairar, sai dai a karshe wayar ta faɗa hannun Humaira tana dariya, ga nata wayar ta na ta haske shaidar faɗowar saƙo amma ko a jikinta.
"Ki yiwa girman Allah kada ki É—aga." Gwalo ta yi mata suka hau zagaye a kicin din.
"Sai kin rantse cewar za ki fadamin ko wane ne mai kiran."
Da sauri ta amsa.
"Eh wallahi zan fadamaki, yanzu dai ban wayar."
Ba musu ta ba ta tana dariya, ta ja kujera ƴar tsugunno ta zauna tana duba nata wayar da saƙon ya faɗo tun ɗazun.
_*Kar ki yi tunanin akwai abin da zai sa Fadeel ja baya ko tsoro. Ki tambayi wadanda suka san waye shi, yana da naci akan abun da zuciya da gangar jikinsa suka yi na'am da shi. Ba shi da saurin karaya, ba kuma ya jin zai soma daga kan ɗiya mace. Ina kuma farin ciki shaida maki ke ce halittar farko a mata da na ji zuciyata ta yi na'am da kasancewarta rabin jiki kuma abokiyar rayuwata. Nasara tana tare da wanda ya miƙa lamarinsa ga Allah. Have a nice day.*_
Ta karanta har da karkata kai kusan sau uku, sai ta ji ma abin kamar irin a fina-finan da ake haskowa a tashar Hausa da su Tasleem ke kunnawa. Ranta na wani irin huci da zafi, a gefe guda kuma duk da wannan radadin wai sai ta ji tana so ta san ma'anar kalmomin karshen da ya rubuta mai kama da farasanci da turanci.
"Lafiya ki ka ba waya hankalinki?"
Muryar Ummita ya katse mata tunani, ta isa wajenta ta miƙa mata waya. Har a sannan hausarta ba ta dawo daidai irin ta Kanawa ba.
"Ɗan fassaramin ƙarashen saƙon nan, me yake nufi?"
Ummita ta karanta tun daga farko, tun kuma somawarta take zabga murmushi don ba ƙaramin burgeta ya yi ba.
"Fatan alheri ya yi maki a wannan rana. Kai Humaira wannan mutumin akwai iya tsara kalami, ina ji a jikina kin samu mijin aure."
Guntun tsaki Humaira ta ja gami da warce wayarta tana Æ´ar harararta.
"Ai ke ce mijin, ni raba ni da wannan shirmen soyayyar kin ji ko. Ba ni da lokacinsu."
"Anya Humaira kalau kike kuwa? Ko dai sai an haÉ—a da addu'a?"
Yamutse fuska ta yi kawai ta kwashi tafarnuwar ta dauraye ta watsa a turmi ta hau daka. Ganin haka itama Ummita ta share batun.
A gefen Futuha kuwa, gaba daya ta yo kan Raihana.
"Ke! Wane Ibb din ki ke nufi ne?"
Raihana ta yi jim, ba ta son ta ce Ibb Malaminta allura ta tono garma don haka sai ta kife ta da fadin.
"Ba fa wanda kike zato ba ne, wannan wani Ibb ne Ibrahim sunansa suka hadu da ita a hanyar islamiyya."
Nannauyan ajiyar zuciya Futuha ta yi kafin ta juya ta koma gadonta tana jan tsaki.
"Toh barkanta, amma da ace Ibb da nake mutuwar so da kauna ne wallahi sai na koyamata hankali. Ke kuma wani sabon salon gulma da munafunci tun da ta wanke maki fuska da mari kike wani shakkarta har da taya ta hira. Ke kika sani."
Raihana dai ba ta tanka ba ta mime ta bar mata ɗakin. Amma ta sa a ranta babu wani abu da zai sa ta kara biye musu wurin nunawa baiwar Allah da ba ta ji ba kuma ba ta gani ba ƙiyayya kawai saboda don zuciya irin nasu.
***
Gidansu cike taf da jama'a sakamakon daurin auren Fu'ad da aka yi a ranar, haka ya dinga kutsawa ransa duk a ɓace har ya shige bangarensu, kai tsaye dakinsa ya nufa, tun daga falo ya cire hularsa ya yi jifa da ita, hakanan babbar rigarsa blue itama ya ajiye saman kujera kafin ya zauna ya shiga kokarin cire covershoe din da ke a ƙafarsa da kuma safa. A duniya Fadeel ya tsani hayaniyar jama'a, wannan ta sa kansa har wani sarawa yake yi. Ya ja guntun tsaki gami da kwantar da kai jikin kujerar ya lumshe idanu. Zafi biyu ya haɗe mishi, ga na rashin samun haɗin kan yarinyar da yake jin ta a ƙoƙon rai, ga kuma wata irin yunwa da yake ji domin ko karin kumallo bai yi ba suka fice masallaci wurin daurin aure. Kowa kuma a dangin sai ya yo kansa da tsokana a wajen, su na fadin saura kai babban yaya. Wadanda ba su da labarin dawowarsa kuwa, sai a ranar suka gan shi. A hankali ya bude lumsassun idanunsa ya murza yatsunsa suka yi ƙara, har wani zogi suke yi mishi saboda gaisuwar da ya dinga yi da jama'a. Lokaci guda kuma ya miƙe ya nufi bandaki, hannun ya wanke tas da hand sanitizer sannan ya fito rike da karamin tawul yana gogewa. Ya yi daidai da shigowar Ibb tare da wani dan uwansu Imran.
Sallamarsu ya amsa ya koma mazauninsa har da kwanciya wannan karon. Kafin Ibb ya yi magana ya riga shi.
"Wai so ku ke na mutu? Yunwa fa nake ji."
Harararsa ya yi.
"Kai dai an yi É—an iska, muna can Alhaji ya sa mu nemoka ku gaisa da abokansa ashe kai nan ka yo? To sai ka tashi ka shirya muje idan ya so kafin mu dawo na yiwa Anti Amarya magana a kawo mana abinci."
Fadeel ya lumshe idanu.
"Kasan Allah ba zan iya fita ko'ina ba, ni fa ji nake idan ma na kara sa ƙafa na fita cikin wannan ranar hanjin cikina za su fito waje."
Imran ya kwashe da dariya, shi kuwa Ibb kamar ya shaƙo amininnasa haka yake ji. Yana niyyar magana kuma sai ga kiran Alhaji karo na uku. Ya ɗaga ya mishi bayani, dama bai tsammaci faɗan Alhajin ba, cewa ya yi babu komai maza ya yi waya a kawomusu abinci. Da wannan suka yi sallama shi kuma a nan take ya yi kiran Anti Amarya ya sanar da ita.
A bangaren Anti Amarya wacce ta ci ado cikin arnen leshi ruwan toka da ya sha adon stones, ga ƙunshi ta yi sai baza ƙamshi take, jin wayar Ibb ya sa da rawar jiki ta amsa ta ba ɗaya daga cikin hadiman gidan Larai umarnin haɗawa Fadeel da abokansa abinci za ta turo a kai musu. Ta shiga falonta inda yan uwanta hudu ke zaune su na shan hira. Uku a cikinsu matan aure ne, ɗaya yayarta sai sauran gaba daya ƙannenta. Ƙanwarta Murja dake kwance tana danna waya ta kai wa duka a ƙafa. Ba shiri ta mike zaune.
"Ke tashi maza ga dama ta samu, jeki wurin Larai na sa ta haÉ—a abincin su Fadeel ki kai musu, kika sani ko Allah zai sa a dace ko cikin abokansa wani ma ya ce yana so?"
Jin haka babbar yayarta Saddika ta amshe.
"Ke wallahi hakane kam, tashi Murja, Allah ya É—ora ki akan su."
Murja ta haɗe girar sama da ƙasa.
"Nikam wallahi Fadeel nake so. Shi dai za ku taya ni addu'a ya ce yana sona."
"Kin ji wawiya, ke kanki kinsan kaf abokansa ma babu na yar wa musamman Ibb. Ai dai kinga irin jama'arsa da suka kawo masa ziyara muna nan dake a gidannan tun zuwansa ko?"
Murja wacce ta zo hutun makaranta gidan Æ´ar uwarta ta, ta mike tana gyara zaman É—aurin dankwalinta.
"Nidai kam shi nake so, ai duk kyawunsu ba su kai shi ba. Malam ga aji na musamman. Kiga fa ko sadda su Sholy suka zo gidannan ko kallo basu ishe shi balle su ga haƙoransa. Nima din ba.."
"Ki yi zaman hira har sai ya gaji ya turo wani ya karɓar musu abincin. Shashasha marar wayo kawai. Ana kai ki kina ƙin zuwa. Ke kika sani. Zauna har ki yi biyu babu."
Jin haka da sauri ta fice daga falon tana dariyar maganar Zuwaira, mai bi wa Anti Amarya.
A kwando ta ga Larai ta haɗa komai har da cokula da farantai, ta kinkima ta yi gaba inda ta tsallake yan uwan Alhaji da suka zo daga ƙauye ko kallo ba su ishe ta ba ballantana ta yi tunanin gaishe su. Su kam suna hau gulmarta da harshen fulatanci. A ƙasan ranta ta ja Allah ya isa.
Tana zuwa ƙofar ta kwankwasa, Ibb ya ba da umarnin a shigo. Lokacin dukkansu har Imran sun cire babbar riga ana shan iskar fanka ana hira, sun zama su biyar a ɗakin sakamakon shigowar abokan Ibb biyu, Saifullahi da Idris. Da sallama a bakinta ta shiga, kasancewar Fadeel ne a saitin ƙofa ya bi ta da kallo ɗaya ya kauda kai ya maida saman kwandon dake hannunta. Dama abin da yake jira kenan, ita kuwa kusan zaucewa ta kusa yi sakamakon kwayar idanun Fadeel da suka haɗu da nata, gaba daya ta ji ta ƙara narkewa a tekun sonsa. A ranta tana ayyana ba gudu ba ja baya shi din dai ranta ke so. Babu wani abokinsa da ta ga ya burge ta, gwara ma Ibb don a baya tana mishi kallon hadadden saurayi duk sadda suka hadu ya zo gaida Alhaji, ita kuma ta zo gidan, yanzu kuwa ta fahimci Fadeel ya kere shi.
"Ba sai kin zuba ba, bar shi za mu yi serving da juna." Fadin Ibb fuska a sake ganin ta sauke kwandon ta hau fito da kayayyakin tana shirin buÉ—e warmer.
Ta kalle shi kadan tana dan murmushi.
"Lah ba komai, bari na zubamaku, wannan ai aikinmu ne mata."