Sashe 77
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
@Rufaida UmarMami ta ga abin na Abba dagaske ne, a gefe ga Humaira dake shirye-shiryen tafiya Nijar sai ɗoki take yi saboda tsabar jimawar da ta yi ba ta je ba. Abba kuwa kamar yanda ya ce ne, Baba Amina ya kira suka yi magana ya ba ta ragamar siyayyar kayan kicin wanda a farko ta nuna sam ita ba za'a yi haka ba idan an yi ba'a yiwa Mami adalci ba. Sai da Abban ya ɓata rai ya zayyane mata yanda suka yi, da kanta ta samu Mamin da zancen amma Mami ta buɗe mata wuta da zummar babu abin da ya shafe ta da auren Humaira da Fadeel. Jiki a mace da kuma ɗumbin mamaki Baba Amina ta dawo a dole ta karɓi wannan ragamar ta kuma taushi Abban akan ya yi mata uzuri tunda hakan ba ta taɓa faruwa tsakaninta da yaran riƙonnata ba.
Humaira kuwa sosai Mami ta dauke mata wuta, gaisuwarta ciki ciki take amsawa, hakanan ko tsinke ta bar sa Humaira dauke mata balle ta sanya ta aiki. Raihana da Ummita lamarin duka ya dame su. Humaira ma tana jin zafin hakan, duk ta bi ta rame amma ba ta jin za ta iya yiwa Mami alfarmar rabuwa da Fadeel alhalin ba ta da kwakkwarar dalili ba. Idan har a yau ta yi yanda Mamin ke so tana da tabbacin alhakin Fadeel sai ya kama ta. Ba kuma za ta taɓa samun rayuwar jin dadi da walwala ba a duniyarta.
AÂ yau ma tana zaune tana gyara kayanta cikin jaka tana yi tana sauraron Raihana da Ummita dake faman zantawa akan lefen da za'a kawo washegari wanda ita kuwa ana kawowa da kwana É—aya za ta wuce Nijar. Ba ta ce musu uffan ba, sai bayan fitar Raihana ne Ummita ta dube ta.
"Ya kamata ki je ki sami Mami kuyi magana Humaira. Haka za ki tafi tana fushi da ke?"
Ta ajiye set din kayan da take shirin sakawa a akwati a saman cinyarta bayan ta zauna gefen gadon jiki a sanyaye.
"Toh ya zan yi Ummita? Kina gani fa Mami ko gaisuwata ba ta amsawa."
Ummita ta girgiza kai.
"Hakanan za ki mayar da komai ba komai ba ki je ki kara ba ta hakuri ki lallaɓa ta. Mun yi mata uzuri saboda sanin da muka yi cewar kowane DAN ADAM ajizi ne. Mu kara yi mata mu gani."
Sauke nannauyan ajiyar zuciya ta yi.
*"Shikenan, bari na je na gani ko za ta saurare ni."
ÆŠan murmushi Ummita ta sakar mata na karfafa gwuiwa. Wannan ya sanya ta mikewa ta nufi dakin Mami. Ta shiga da sallama a bakinta amma babu amsa, don ta tabbatar ko ba ta dakin ne ya sanya ta É—aga labule ta shiga. Mamin hankali kwance tana zaune gefen gado sai faman danna wayar hannunta take. Abin bai ba Humaira mamaki ba, ko ba komai zuwa yanzu dama ya ci ace ta saba da hakan. Don haka ta daure ta karasa ta durkusa a gefe, Mami kuwa tun shigowarta ba ta ko kalleta ba sai ma fuskarta da ta tamke tamkar hadari ya haÉ—o.
"Mami ina sane da cewa har yanzu kina fushi da ni, na zo ne domin na ƙara ba ki haƙuri akand laifin da ban san na aikata ba."
Wani kallo ta É—ago ta watsa mata wanda ya sa Humaira sunkuyar da kai gami da yin shiru.
"Kin zo ne don ki nunamin ke din ba ki da mutunci kuma butulu ce?"
Jin haka sai abin ya daure mata kai.
"Mami har ga Allah ban san taƙamaiman laifin da nayi ba."
"Dakyau! Ai idan ba ki yimin wannan butulcin ba, ba ki cika É—iyar Fatima ba."
Maganar ta daki zuciyar Humaira da har sai da ta ƙara buɗe idanunta wurin kallonta sosai. Mami me yawan yabon halayen Mahaifiyarta, yau kuma ita ce saboda son zuciya irin nata ta ke kushe ta?
"Kiyi hakuri Mami, kiyi hakuri idan har da abin da na maki mai zafi amma domin Allah kada laifina ya ture kyawawan yabon da Mahaifiyata ta samu a wurinki. Babu abin da take buƙata a wurinmu face fatan alheri."
Muguwar harara ta watsa mata, kamar ta ce fatan alherin uwarki sai kuma ta danne zuciyarta dakyar.
"_Kar ki yi saurin rushe komai don ba alheri ne gareki ba._ _Nace maki mu bi komai sannu har mu cimma gaci._ _Aure dai ki kwantar da hankalinki ba zai faru ba kamar yadda Babandi ya tabbatar mana._"
Maganganun Hajiya Lubna ke yawo a ƙoƙon ranta, don haka sai ta yiwa Humaira nuni da ƙofa.
"Ficemin a ɗaki tun ban kwaɗa maki mari ba. Ke har kin kai ki faɗamin abin da ya dace da ma wanda bai kamata ba? Ko kin ga ni Maryam na shiga shirgin aurenki da wancan lalataccen? Toh kamar yanda ban shiga ba ki je can ku ƙarata ke da shi, ai kowa ya san abin da za ku aura daga ke har shi."
Ɗan shiru Humaira ta yi tana nanata kalaman ƙarshe na Mamin a zuciyarta idanunta kuwa ƙurr a kanta, to me take nufi? Gaba daya ta kasa fahimtar manufarta da kuma inda ta dosa. Sai da Mamin ta yi mata wata tsawa kan ta fice mata a ɗaki sannan ta miƙe gwuiwa a matukar sanyaye ta fita tana fidda hawayen bakin ciki. Tunanin ba Ummita kadai ce a ɗakin ba saboda lokacin yi mata wanka ya yi sai kawai ta shige kicin ta zauna tana kuka sosai. Tana kara gasƙata cewa dai wasu sabbin halayyar Mamin da ba ta sani bane suke bayyana a muraran. Lallai ta fara shaƙar ƙamshin gaskiya a kalaman Anti Maijidda, za kuma ta so tasan ko menene ta sani akan Mamin har ta kasa aminta da zuciya ɗaya take zaune da Ummita da ma ita kanta. Sai da ta kammala kukanta ta share hawaye ta koma sashinsa bayan ta wanke fuska amma ina, duk da haka Ummita da Raihana dake zaune riƙe da Ahmad a hannu wanda ya sha wanka suka fahimci akwai ta yi kuka sakamakon sauyin da fuskarta ta yi.
"Lafiya Humaira? Me aka yi? Kin bar waya tun É—azu angonnaki ke faman kira."
Ta yi murmushin yaƙe kafin ta amsawa Raihana.
"Babu komai, ina wayar?"
Ta miƙa mata tana mai ƙara jefamata tambaya don ita sam ba ta yarda ba, a ƙarshe ta ce.
"Mami ce ko? Don nasan ba kya shiga sashin Anna balle nayi tunanin ko..af ko kin haÉ—u da Anti Jannat ne? Ba ta jima da fita a dakinnan ba ko kun haÉ—u?"
"Ke dai Raihana ko ma wacece kuma ko mene ne tunda dai ya faru ba shikenan ba?"
Ta É—an yatsine fuska.
"Allah ya kyauta dai." Ummita ta amsa da amin. Sai da Raihana ta bar wurin ne ta kwashe duka yadda suka yi da Mamin ta sanar mata. Ummita yarinya mai kaifin basira da kwakwalwa tsaf ta fahimci manufar zantukan Mami amma sai ta ɓoye ga Humaira duk kuwa tana tunanin watakila itama ta fahimta kawai dai ba ta son fassara zancen yanda zai yi mata ƙuna a zuciya ne.
***
Washegari kuwa ya kama ranar da za'a kawo lefen Humaira, tun safe Baba Amina ta iso sai shiri take yi don ma dai an ce maza ne za su kawo. Mami kuwa sai cin magani take yi ta ƙi kula koda gaisuwar Baba Amina balle ta sa ran samun maganar arziki. Raihana ya je makaranta don sun soma zane jarrabawa, su Muhsin ma duka ba sa nan. Mami ce zaune a galo sai Baba Amina a gefe ita da Jannat wacce duka ranta a ɓace yake sakamakon wayar da ta kammala da mijinta da ya rufe ta da faɗan lallai ta dawo kda ta ƙara koda kwana ɗaya don tare zasu yo ƙaura zuwa Nijeriya baki daya amma firr ta ƙi saboda bikin Humaira da ya tsaya mata a rai, burinta ta ga tsiyar da za a kawomata ga aikin da bokanta ya bayar take son aiwatarwa akan Humairar wanda zai sa ko bayan aurenta da Fadeel ta kasa samun kwanciyar hankali a gidansa, an tabbatar mata auren babu fashi hakan ya sa ta ɓullo da wata hanya daban na musguna mata duka don ta faranta ran Tasleem dake haukar son Fadeel amma ba ta samu aurensa ba. Kayan Humaira kawai za ta dauko saiti ɗaya ta kawo masa ya yi aikin da idan har ta sake ta yi amfani da kayan za ta tsani zaman gida kullum tana hanyar gantali koda kuwa ba za ta aikata wani shirme na banza ba. Tana da tabbacin muddin aikin ya ci toh fa Fadeel da ma yan uwansa za su tsane ta kuma ya rabu da ita.
Suna nan zaune Mami da Jannat sun cika sun yi fam saboda Baba Amina dake kiran wayar sauran yan uwan Abban da ba su ƙaraso gidan ba akan su yi da jiki an kusa. A haka wayar Mami ta dauki ƙara, dubawar da za ta yi ba kowa ba ne sai Wizzy, ta dan saci kallon Jannat dake gefenta, ganin hankalinta na ga waya tana dannawa ya sanya da sauri ta mike ta shige ɗaki ta rufe kafin ta sa wayar a kunne. Cikin kwantar da murya kamar ba Mami ba take magana.
"Haba Wizzy, meyasa kake son yimin azarɓaɓi a lamura ne? Ban fadamaka ka kwantar da hankalinka a soma sabgar biki ba idan ya so sai na sato maka shi na kawomaka?"
A kausashe ya ce.
"Ke Hajiya kina fa kawomin rainin hankali iri-iri, sai wani hankadomin hotunan yaro kike yi kina sanya soyayyarsa samun matsuguni a zuciyata toh kuma don me za ki wani ja min lokaci don za'a yi bikin Æ´ar dabar da ta kusa kashe ni?"
Ta dan goge zufar goshin da ya karyo mata tana mai sauke ajiyar zuciya.
"Ka dai yi hakuri, ni ai Maryam ba na daukarwa mutum alƙawarin da na san cewa ba zan iya cika shi ba. Ka kara hakuri zuwa lokacin komai zai tafi yadda kake so."
"Shikenan! Kin ci darajar jikanki da na nunamaki ko ni É—in waye. Zan ba ki daga nan har sati uku."
"Babu damuwa. Amma don Allah ka bar kokarin kira koda ta whatsapp din ne, ka dinga hakurin na yi maka magana."