← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 43 OF 101

Sashe 43

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

***
Kwanakinta a gidan Futuha babu abin da take yi sai ɗirkar aiki, akwai ƴar dattijuwar dake zuwan yini tana tafiya. Takan kama ayyukan gyaran ƙasa, ita kuwa Humaira ta gyara saman tas, duk wata dauɗa da Futuha ta bari tun zuwanta babu gyara kaca-kaca sai da ta dawo yana kyalli. Ga girkuna masu dadi da ta ke yi musu safe da yamma, Futuhar da ba ta ɗan sakarwa Humaira fuska, tsabar jin daɗin yadda ta ke mata bauta sai ga shi ta soma saki, babban ƙudurinta kuma bai wuce idan sun dawo daga tafiyar da zasu yi ba ta yi dabarar da Humairar za ta dawo ƙarƙashinta gaba ɗaya.
Ana gobe su Futuha za su tafi ne, Humaira ta fito ta zagaye can bayan ɗakunan inda anan ne aka yi wasu shuke-shuke masu ban sha'awa, a lokacin babu koda a ɓangaren Futuhar, Baba Furera ta wuce gida, Futuha kuwa an tafi gyaran gashi da jan ƙunshi. Hakan yasa kaɗaici ya yi mata yawa, ga dai wuta nan daga safe har dare amma ta gaji da kallon balle kuma danna wayar. Wannan ne dalilin zagayawarta baya tana kallon shukokin masu burgewa da ɗaukar ido. Tana nan tsaye tana murmushi tana shafar su gami da shinshinar ƙamshin da ke jikinsu, ta kai duba ga sararin samaniya yadda hadari ya yiwa garin ƙawanya, a hankali ta lumshe idanu saboda jin daɗin yanayin. Sai dai kuma lokaci guda kamar wacce aka mintsila ta bude idanuwanta tarr jin kukan jariri da ke tashi sosai. Ta kai duba ga inda sautin ke fita har ƙirjinta na bugu da sauri-sauri. Sashin dai da aka ce na uwargida ne, daga nan ta dinga jin kukan na tashi. Cikin sauri da gudu-gudu ta bar bayan ta dawo bangaren Futuha, daidai nan suka yi kiciɓus da mai ba shuka ruwa. Ta dube shi, ganin yadda take faman haki ya sanya shi tambayar ko lafiya. Da yatsa ta yi mishi nuni da hanyar ɓangaren Uwargidan da ake kira Hajiya Saratu.

"Me aka yi a wurin?"

Ta haÉ—iyi miyau.

"Da mutane a ciki ne?"

Sai tambayar ta ba shi mamaki.

"Hala ke baƙuwa ce? Ai ɓangaren Hajiya ne, tana nan. Ko wata biyu ba ta yi da haihuwa ba."

Sai hankalin Humaira ya É—an kwanta amma kuma sai ta hau wani sabon mamaki da al'ajabin. Don haka ta kuma dubansa ta ce.

"Dama ta dawo daga tafiyar da ta yi ne?"

Ya yi Æ´ar dariya.

"Ko kusa, babu inda ta je tana nan. Ai da yake ba ta fiye fita ta wannan ƙofar ba, akwai ƙofa ta baya, ta fi fita ta can idan ta tashi zuwa unguwa. Kuma gaskiya dai ni zan iya cewa tun ma da ta haihu ba na tunanin na ji ance ta fita. Koda dai ba ganewa ake yi ba tunda Hajiya motar haya take shiga."

Ya ƙarashe da wani irin jimami, har ya buɗe baki zai ƙara magana sai kuma ya girgiza kai kawai ya fice. Humaira ta bishi da idanu tana mai cike da al'ajabi. Idan maganganunsa gaskiya ne? Toh me Alhaji Yakubu yake nufi da ɓoyewa? Ita dai ta ji Futuha ta ce Uwargidansa ba ta nan su na Dubai da yaranta. Toh idan hakane su ne a gidan, meyasa ko da wasa ba a ganin gilmawar yaranta tunda dai ai yaro ba zai yarda da rayuwar ƙulle ba?

Amsoshi ne da ba ta da amsar su kawai sai ta ja ƙafafunta da suka yi wani irin sanyi ya bar wurin.

***Humaira ta kama bakinta koda wasa ba ta sanar da Futuha komai ba, ba ta ga dalilin sanar da ita abin da bai kamata ta ji daga bakinta ba wannan ya sa ta bar abin a cikinta. Washegari da misalin ƙarfe biyun rana sai ga su Raihana a gidan sun zo rakiya Airport, daga nan direba zai mayar da su gida gaba ɗaya.
  Jirgin dare ne wannan ya sa sai bayan magriba suka hau shirin tafiya, Humaira ta tattara kaf kayanta, dama ta gaji da gidan babban burinta shi ne kawai ta koma cikin ƴan uwanta. Sakewar da Futuha ta yi da ita bai sa ta iya sakin jikinta ba don ba ta saba da shi ba, ta fi ganewa rayuwarsu ta baya yadda suke hantararta a abu ƙalilan amma sam zuciyarta ba ta amince da wannan sauyin ba.

Ƙarfe goma jirginsu ya tashi, su kuma aka kai su gida. Humaira ranar kamar an tsoma ta a aljanna, farin ciki biyu ya haɗe mata, na farko bai wuce dawowarta gida ba daga zaman uƙuba da bautar da ta ke yi a gidan Futuha, na biyu kuwa jin daddaɗan labari daga bakin Raihana cewar iyayen Sahabi nan da kwanaki biyu za su zo tambayar auren Ummita. Ranar dai bacci ɓarawo ne ya sace su don raba dare suka yi ana hira.

***
  Anna ta dubi Mami ranta a tsananin ɓace ta ce.

"Ke kam da a asibiti na haihu zan iya rantsuwa sauyamin ke a ka yi wannan ba jinina ba ce. Ni dai kaf zuri'armu babu macen da za ta aikata wanan abi da kike aikatawa na rashin sanin ciwon kai da kuma rashin zuciya. Wannan rawar ƙafa da murna da kike yi ko kuɗin auren Raihana aka kawo sai haka."

Tana kai wa nan ta ja tsaki, Mami ta yi ɗan murmushi. Kawo kuɗin gaisuwar iyaye da sanya rana da aka yi na Ummita a yau ne ya sosa zuciyar Anna take wannan zantukan. Ita idan irin hakan ma abu na farin ciki ya afku ga Humaira ko Ummita har ba ta kaunar ya zo kunnen Anna saboda irin waɗannan bakaken kalaman da ba ta haƙura ta bar wa cikinta sainta furzar. Kamar ko yaushe a kwanakin nan, wannan karon ma Mamin shiru ta yi ba ta ce uffan ba. Itama Annar don kanta ta gaji ta bar zancen. Ta sanyo wani batun bayan ta kora ruwa a cikinta.

"Af, yar uwarki tana nan tafe ƙarshen watan nan."

Cike da mamaki Mamin ta dubi Anna ta ce.

"Jannat kuma? Me zai kawo ta nan kusa alhalin yara ba hutu suka yi ba?"

"Toh kina baƙin ciki da zuwan nata ne?"

Jin haka da sauri Mami ta ce.

"Ko É—aya, Allah ya huci zuciyarki. Allah ya kawo ta lafiya."

Anna ta amsa da amin, ganin tana neman ɗora maganar ɗazu sai kawai Mami ta miƙe tana mai ba ta uzurin zuwa wurin mijinta. Yamutse fuska kawai Anna ta yi ba tare da ta ce komai ba.

***
Alhaji ne zaune saman darduma a barandarsa yana latsa waya, isowar Fadeel ne ya sanya shi ajiye wayar ya mayar da hankali garesa. Bayan amsa gaisuwarsa ya gangara kan batun da yake son yi.

"Babban dalilin kiranka bai wuce kan maganar aure ba. Lokaci ya yi da za ka tsaida hankalinka wuri guda ka nemawa kanka abokiyar rayuwa. Kana gani dai ga ɗan uwanka nan har an soma batun zuwa gaisuwa da roƙon iri. Toh an kai lokacin da zubamaka idanun da aka yi ya kamata ace ya zo ƙarshe, ga baffanninka nan a ganinsu har da laifina a ƙin matsa maka da zancen. Har cewa suka yi idan babu dama ka je can gida ka zaɓa cikin ƙannenka wacce ku ka daidaita sai a yi magana. Rashin ba su goyon baya akan haka ba yana nufin na amince da zaman naka hakanan ba Fadeel. Shekaruna gaba suke ƙara yi ba wai baya ba, lokacin ƙure mana yake ƙara yi. Alhamdulillah ka fara gini, koda ace bai yi nisa ba, ina da tabbacin nan da shekara dai ka haɗa komai. Kai yanzu ɗan uwanka ba abin koyi ne gareka ba? Ka gwammace kana ji kana gani ya yi aure ya bar ka nan zaune? Har zuwa yanzu babu wacce ka tsayar?"

Fadeel ya ƙara sunkuyar da kansa, ya sani dama tun da har zancen auren Ibb ya tashi, toh fa Daddy da Alhaji ba za su ɗaga masa ƙafa ba. Yana kuma da tabbacin yadda Alhai ya yi mishi magana, to fa shi ma Daddy zai ɗora da nasa bayan kwanaki.

"Ba ka ji ne?"

Ya ɗago ya ɗan ja numfashi, babu amfanin ɓoye-ɓoye, babu kuma alfanun faɗin gaskiyar da za ta jaza masa rabuwar da bai shirya ba da Humaira. Yana tsoron ya kasance idan ya zayyana komai yadda yake tafiya a yanzu, ran Alhajinsa ya ɓaci ya nemi ya fita a hanyar Humaira, wannan ne dalilin da ya sanya shi yiwa zancen kwaskwarima.

"Ka yi hakuri Alhaji, ba wai babu wacce na tsayar ba ne. Akwai, sai dai yarinyar nan da watanni bakwai zuwa takwas za ta kammala makarantar da take zuwa, ta kuma roƙe ni na ba ta dama har su kammala. Wannan shi ne dalilin da ya hana ni gabatar da ita a wajenku. Ina neman ƙarin lokaci zuwa sannan, idan Allah ya yarda ba zan ba ku kunya ba."

Alhaji ya É—an yi jim, ba haka ya so ji ba, ya so ace kawai Fadeel din ya ba da damar a nemi auren a haÉ—a da na É—an uwansa (Ibb) amma hakan ma ya ji daÉ—i tunda dai akwai wacce yake so. Don haka sai ya É—an saki fuska.

"Shikenan, su iyayenta sun sani cewa kana neman auren É—iyarsu?"

Ya ji gabansa ya faɗi, anan kam ba ya jin zai iya ɓoyewa don haka ya girgiza kai ya furta kalmar a'a.

Murmushin manya Alhaji ya yi.

"Fadeel kenan, to kai ban da ma abinka, yanzu idan aka tashi mahaifin yarinyar ya aurar da ita ga wani sai ka ce ya yi maka rashin adalci ko?Idan ba kai ba, ina aka taɓa wannan wautar? Kana son yarinya amma ka kasa gabatar da kanka wajen iyayenta? A zatonka sun san da zamanka ne kawai saboda kana zuwa hira wurin ɗiyarsu? Me zai hana mu ka bamu damar tura wa gidannasu a san da zancenka?"

Ya ɗan sosa ƙeya kaɗan, inama hakan abu ne mai sauki, inama kuma idan an aikata ba zai ga bore daga Humaira ba wadda yana da tabbacin a yanda take gudunsa za ta iya cewa ta fasa auren ma baki ɗaya, ai ba don haka ba da gudu zai yi na'am da shawarar Alhaji. Sai dai kuma ya sani, ba abu ne mai sauƙi ba.
Chapter 43 · 0% Book details