Sashe 51
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Awa bai fi ɗaya tsakani ba, sai ga wayar Abba zuwa ga Mami, a gaggauce ya sanar da ita kuɓutar su Ummita ya kara shaida mata cewar su na asibiti. Hankali a mugun tashe suka fice tare da Ƙasim da Raihana wacce lokaci guda wani mugun zazzaɓi ya rufe ta musamman jin cewar su na asibiti. Suka yi kiciɓus da Kawun Humaira da matarsa Hajjo wadanda isowarsu kenan garin. Ba su tsaya yi musu dogon bayani ba, Kawu ya bi su yayinda ya ce Hajjo ta tsaya ta jira dawowarsu a gida.
***
 BAYAN AWANNI...
Mummunan labarin da ya iske su Abba na keta alfarmar da aka yi ga Ummita ya sanya shi sumewa bai ko iya jin ƙarshen ba balle ya san ko har Humairar ma an taɓa. Nan aka kwashe shi shima don ba shi taimakon gaggawa. Raihana kuka kamar ranta zai fita yayinda Mami ke taya ta. Kawu da Fadeel kuwa tashin hankalin da suke ciki ba zai misaltu ba. A gabansu aka fiddo su bayan an yiwa Ummita ɗinki na mugun raunin da aka ji mata aka sauya musu ɗakunan zuwa na hutu, daki mai gado biyu. Fadeel ya ƙurawa Humaira idanu kamar kirjinsa zai fashe haka yake ji, nan take idanunsa suka kaɗa jawur. Gaba ɗaya ta lalace ta yi rama tamkar wata halittar ce ba ita ba sai ko hancinta da ya ƙara fitowa. Har aka shige da su bai iya kauda kansa ba. Shi ya yi ƙarfin halin biyan dukkan abin da aka kashe har da na kama ɗaki.
 Cikin ƙanƙanin lokaci labarin kuftowar su Humaira ya cika gari, mutane da waɗanda suke dangi da ma yan uwa na gari suka dinga tururuwar zuwa yi wa su Abba barka, babu wanda aka bari shiga wajensu, hakanan labarin abin da ya afku gare su bai fita ba. Yan jarida kuwa suka dinga yaɗa rahoto, hakanan social media ta dauka. Futuha mutanen Dubai ta ƙara yin bidiyo mai nuni da damuwa da kuma farin ciki tana shaida wa jama'a cewa an ga ƙannenta. Nan aka hau taya ta murna sosai.
Mutanen Bichi da labari ya iske su su ma baa bar su a baya ba. Anti Maijidda ta yi kuka kamar ranta zai fita jin labarin keta haddin da aka yi ga Ummita, matsayinta na babbar yaya ga uwarta ya sa Abba sanar da ita a sirrance.
 Sahabi kuwa baki har kunne, sun zo shi da abokansa yayinda mahaifinsa takanas ya zo ya taya Abba murna da addu'ar Allah ya kiyaye gaba.
 Kwanakin su Humaira biyu suka dawo hayyacinsu. Ummita ce ta soma farfaɗowa, ranar Allah ya taƙaita Anti Maijidda na zaune tare da Baba Amina sun yi jugum su na dan hira jefi-jefi hannuwansu riƙe da casbaha. Wani gigitaccen ƙara Ummita ta saki da ya yi masifar tayar da hankulansu.
"Wayyo Allahna! Kar ka kashe ni! Ka rabu da ni! Na haÉ—a ka da Allah ka rabu da ni!! Wayyo Allahna!!!"
Cikin kuka da tashin hankali suka yi kanta su na riƙewa, aka bankaɗo ƙofar aka shigo, su Abba ne da ihun Ummita ya iske su. Raihana a guje ta nufi wurin Nurses dake tahowa, kafin ta kai ga magana suka ce sun ji. An tafi kiran likitan. Su na shiga sai ga Likita, aka fitar da kowa a ɗakin.
Gaba É—aya matan kuka sosai babu kamar Raihana da take jin kamar ta shiÉ—e. A yadda take jin zuciyarta za ta iya fille kan wanda ya aikata wa yan uwarta wannan tozarcin.
Koda likitan ya ƙarasa gareta flask din ruwan zafin dake ajiye a gefenta kawai ta ɗauka ta jefa masa. Ba don Allah ya sa shi kaucewa ba da babu abin da zai hana a same shi.
Tana cikin wannan gigitar Humaira ta farka a matukar firgice, ta kira sunan Ummita da karfi sannan a guje ta diro ta zo ta rungumeta tana kallon jama'ar ɗakin kamar wasu sabbin halittun da ba ta taɓa gani ba.
"Su waye ku? Me za ku yi mana?! Ku fice ku bar nan! Wallahi ku ka yi ƙoƙarin zuwa kusa da mu zan ji maku ciwo."
Sai kuma ta juya a mugun firgice tana tattaɓa jikin Ummita dake kuka kamar ranta zai fita.
"Ummita! Yi shiru, Abba zai zo. Naji suna cewa yana hanya. Yi shiru, sai mun kashe su."
"Kin.."
Likitan ya ƙaraso zai soma magana Humaira ta juya da azama tana nunashi da yatsa. A sannan su Abba gaba daya sun shigo sun kasa daurewa.
"Kar ka taɓamin ƴar uwa! Zan kashe ka!!"
"Humaira, Ummita."
Humaira na ganin Abba ba ta ko damu da sauran jama'ar Abba ta karasa a guje ta rungume Abba tana kuka mai tsuma zuciya.
"Abba za su kashe mu! Abba ka cece mu! Ka É—auke mu mu bar nan!"
Irin riƙon da ta yiwa Abban ba na wasa ba ne har maɓallan wuyar rigarsa sai da suka fita.
Cikin hawaye ya ce.
"Mamana babu abinda za su yi maku, likitoci ne. Kun kuɓuta daga hannun azzalumai. Ki kalla dakyau, ga Maminki ga yar uwarki Raihana. Kin gane Kawunki?"
Ta tsaya cak kamar wata sokuwa tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, Ummita kuwa da nos ta lallaɓa ta yi mata allura tuni bacci ya kwasheta. Kawai sai ta soma ruwan wasu sabbin hawayen ta ma kasa cewa uffan. Zuciyarta ta gasƙata eh sun kuɓuta daga hannun azzaluman, amma kuma ta ji tana tantama tana gani ko mafarki ne. Wannan ya sa Raihana tahowa da sauri ta rungumeta ta kara sautin kukanta.
A hankali ta ɗaga hannunta ta ɗaga fuskar Raihana ta na kallo kamar wata baƙuwar halitta ce gabanta, sai kuma da rawar murya ta ce.
"Raihana ce?"
Raihana saboda ƙarfin kukan ma ta kasa magana sai kawai ta ɗagamata kai. Humaira ta rungumeta sosai suna kukan tare.
"Amm, don Allah a ragu a É—akinnan. Alhaji ina son magana da kai."
Fadin Likita, ganin haka duk aka fice banda Raihana wacce Humaira ta riƙe hannunta gam tamkar ita kaɗai ta gani.
***
Likita ya dubi Abba cikin nutsuwa ya soma magana.
"Lamarin ita Ummita na buƙatar rarrashi da ja a jiki. Kaso casa'in na ire-irenta da hakan ke afkuwa a kansu sukan samu matsala ta rudani, firgici da kuma rashin yarda ga kowa. Wasu kuma yakan taɓa musu kwakwalwa. Zamu yi mata gwajin kwakwalwa don a tabbatar da komai na ta lafiya kalau yake."
Abba ya share fuskarsa.
"Toh Likita, nidai babban burina lafiyarsu. Allah ya sa komai lafiya."
"Ameen." Ya amsa cikin tausayawa yana mai lallaɓar Abba.
***
Cikin iko na Ubangiji an yiwa Ummita gwajin kwakwalwa kuma an tabbatar da komai lafiya. Wannan ya kwantar da hankulansu. Humaira dai ba ta dogon magana tun farkawarta, kowa ta gani sai dai ta ambaci sunansa, idan an rungumeta an sa kuka itama ta soma. Da daddare ba bacci sai razana, ga Ummita haka. Wannan yasa aka raba musu É—aki. Fadeel na zuwa, kuma abin mamaki Humaira na ganinsa ta kira sunansa, abin sosai ya ji dadinsa ya kuma tsaya a ransa.
Sai da suka kwashe sati biyu a asibiti kafin su tattara su dawo gida. Babu laifi sosai zuwa lokacin sun samu nutsuwa ba kamar farko ba. Sai dai daga Ummitan har Humaira duk sadda tunanin cin zarafin da aka yi musu da kuma keta haddin da aka yiwa Ummitan sai su yi ta kuka. Har zuwa lokacin babu wanda ya san da mummunan labarin sai ko Anti Maijidda da Mami wadanda Abban ya faÉ—awa.
Anti Maijidda nan fa ta dage akan lallai sai a ba ta Ummita su tafi Bichi, Abba ya ƙi amincewa. A dole ta haƙura ta tafi tana ƙunar rai da jin tsanar Mami har cikin ƙoƙon ranta.
Jannat ko a fuska sai ka rantse nan jimamin duniya take yi akan lamarin don ba ta nuna komai wanda zai sa wanda bai sani ba ya fahimci takun saƙarta da su. Hakanan Anna wacce ta daurewa zuciyarta ta taka har ɗakinsu ta duba lafiyarsu bayan ta je asibitin a baya har sau uku. Wannan ya wanke ta daga zargin mutane da rashin nuna kauna ga su Humaira a baya.
****LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*
*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*
09034973645
Sai da su Humaira suka samu sati hudu cif kafin su ɗan maido da jikinsu, da kuma walwala kaɗan. Sukan zauna cikin jama'a, a taɓa hira da su idan ka cire Ummita da har lokacin ta tuno aika-aikar da aka yi mata sai kawai ta fashe da kuka wanda hakan ke tayarwa Humaira hankali itama ta sa nata kukan sai su haɗu su yi ta yi. Kawun Humaira ya so su koma can Nijar da ita amma nan ma Abba ya nuna sam bai amince ba dole haka ya tattara matarsa suka koma gida.
 Su na zaune a ɗaki, Ummita riƙe da Alƙur'ani tana karantawa zuciyarta na yin sanyi yayinda Humaira ke kwance saman katifa ta yi shiru gami da zubamata idanu kusan ma hankalinta ba a kanta yake ba, ta lula wata duniya ta daban na tunani. Raihana ta shigo ta iske su haka, dawowarta kenan daga makarantar boko wanda har lokacin Ummita ta ƙi amincewa ta koma ganin haka babu wanda ya takura mata shi ma mai makarantarsu da ya zo har gida ya jajanta ya ce a kyale ta zuwa wani lokacin.
"Wash! Wallahi na gaji! Ke kuma kina da baƙo a falon Abba."
Ta faɗi da murmushi tana duban Humaira duk a ƙokarinta na son ta ga komai ya dawo daidai a mu'amalarsu. Humaira ta ɗan dube ta gami da ɗan haɗe gira kaɗan.
"Wa kenan?"
"Fadeel."