Sashe 25
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
"Mami, wannan fa ya fi Hamza kudi da haÉ—uwa, na tabbata abin da ya ruÉ—e ta kenan."
Mamin ba ta ce komai ba face Allah ya kyauta.
***
Yana zaune a cikin motar hankalinsa rankatakaf akan ƙaton ƙyauren gidan da Tasleem ta yi mishi kwatance, ji yake tamkar ya yi tsuntsuwa ya shiga ya yi ido huɗu da abar ƙaunarsa, ganin ya kwashi mintuna babu alamar Tasleem sai ya ji gaba ɗaya ya karaya. Kodai ba gidan ba ne? Waya ya fiddo da niyyar ƙara kiranta sai ya hange ta ta fito daga gidan. Da farko sam bai gane ta ganin tamkar wannan ɗin shirin fita unguwa ta yi, ga dukkan alamu ma ba gidan ba ne. Amma a hankali tana matsowa ya gane ita ce don haka ya sauke tinted glass din motar wanda ya katange ta daga ganinsa sai waige ta ke.
Tasleem kuwa yana saukewa ta ji numfashinta na barazanae ɗaukewa ba don tsoro ba sai domin tsananin burgeta da ya yi, ga kuma wani irin kyau da ya yi mata. Shadda ce a jikinsa coffee colour, ya ɗora hula a kansa, wannan karon babu gilashi a idanunsa don haka kyawun fuskar ya ƙara bayyana muraran. Ta kasa furta koda harafi har sai da don kansa ya fito daga motar ya rufe. Murmushi mai tsada ya sakar mata.
"Ashe kin iya kwatance."
Ta yi farr da idanu haÉ—i da sakarmasa nata kalar murmushin itama. Cike da yanga da kwarkwasa ta ce.
"Kai kuma kana da basira tunda har ka iya ganewa. Barka da zuwa, bismillah mu shiga daga ciki."
Ba musu ya karɓi tayinta, bayan sun gaisa da maigadi dake zaune a benci, tana gaba yana biye da ita yana ƙarewa gidan kallo. Hatta da gidan sai da ya ji kaunarsa a zuciya, ya kuma rantse albarkacin masoyiyar tasa ce. Falon suka shiga ya zauna bayan ta mishi bismillah, sai ƙamshi kuwa ke tashi a ciki don dama tunda ya yi mata kiran farko ta ba mai wankin Abba dari biyu akan ya taimaka ya kara share mata a sa turaren wuta.
"Ina zuwa." Ganin ta furta haka tana niyyar ficewa sai bai ce mata uffan ba, ba ya son ya yi garaje da tambayarta Humairar, tunda har ta ce tana zuwa to ya sani ba zai wuce ita za ta rako ba.
Ya lumshe idanunsa kafin ya buɗe ya sauke saman hoton Abban dake maƙale jikin bangon. Ko wani bai faɗamasa ba, wannan mahaifin Humaira ne, kamannin ya ɓaci kwarai. Sai ya ji kaunar Abban ya lulluɓeshi, ƙauna dai kwatankwacin irin kaunarsa da Alhajinsa. Sallamar Tasleem din karo na biyu ya katse dukkan tunaninsa. Ganinta ɗauke da tray na kayan sanyi nan da nan ya ɗan ɗaure fuska, shi fa duk ba wannan ne a gabansa ba. Tana ajiyewa ya ga tana kokarin zama ya karya bille ya ce.
 "Where is she?"
Ta dube shi cikin rashin fahimta, ta yi ƙarfin hali ta ce.
"Who?"
Ya dauke kai daga kallonta, ya soma hasaso wani abun, ya gane ita É—in manufarta daban, tunaninta ya tafi wani wajen. Mafarkinta daban.
"Wacce na zo domin ta, Humaira."
Kirjin Tasleem ya hau bugu, har ji ta yi ganinta ya É—an dusashe. Miyan bakinta haka ta neme shi ta rasa, dakyar ta tattaro jarumta ta ce.
"Humaira kuma? Dama wajenta ka zo."
Sai a sannan ya dube ta tsakar ido.
"Yes, wurinta na zo. Ko sadda muka haÉ—u dama haka nace wujenki zan zo?"
Tasleem da har ta soma hawaye ta kasa magana, eh bai furta cewa wajenta zai zo ba, amma wane rainin hankali ne ya sa bai nemi kwatance daga Humaira ba sai a wurinta? Ta kuwa daure fuska tamau, ta rantse daga ita har Humairar sai dai su yi biyu babu. Kowa ya rasa don hana ta ce.
"Toh Humaira ban santa ba, asalima a wurin biki muka haÉ—u. Na yi zaton gidanmu kake nufin na kwatanta mana. Don haka babu Humaira a gidannan."
"Ko?" Ya furta idanunsa a saman hoton Abba, itama ta kalli hoton. Ranta ya ɓaci ainun, ta san kamannin Humaira muraran da ya gani a fuskar Abba ya sanya shi furta hakan. Ta mike tsaye ta koma gefen Fadeel ta zauna. Zuwa yanzu ransa ya kai maƙura wajen ɓaci amma yana tausar zuciyarsa da tunanin bai dace ba, ta ci alfarmar abin sonsa. Ko babu komai tace masa mahaifinsu guda. Ita kuwa da muryar kuka ta soma magana.
"Wallahi ina sonka. Tun ganin farko da nayi maka zuciyata ta kamu da begenka. Me za ka yi da Humaira? Da me ta fi ni? Na rantse babu abin da za ta nunamin."
Ya runtse idanu, ransa ɓaci yake ya na kokarin danneshi, amma jin ana kushe abar sonsa ya bude idanunsa da suka yi jawur tarr a cikin nata. Sai da ta ji rishin kukan ya tsaya na ɗan lokaci tsabar fargabar kar ya shaƙo ta.
"Ki san kalaman da za ki faÉ—i a kanta. Idan kuma kina son kanki da mutunci, ki yakice ni a ranki. Ki sani kuma ki kara, Humaira ta fiyemin ire-irenki dubu. Kyau da sura ba su ne a gabana ba. Da ace su ne, na bar da yawansu a inda na fito, ba na sonki, ba kuma na son kowa sai ita É—in. Idan za ki iya ki shiga ki yimin sallama da ita, idan ba ki iyawa ni zan sa a kira ta."
Da gudu Tasleem ta mike ta yi hanyar fita tana kuka sosai. Fadeel ya mike tsam ya fito farfajiyar gidan inda ya ci karo da Muhsin na wasa da keke. Ƙarasawa ya yi wurinsa ya ɗan durkusa daidai tsawon yaron yana murmushi kamar ba yanzun aka ɓata ransa ba.
"Boy, ya sunanka?"
"Muhsin."
Ya jinjina kai, da alama duka sunayen yan gidan su Humaira masu dadi ne, shi kam dadi yake mishi, ya ji ance Futuha, Tasleem yanzu kuma ga Muhsin.
Ganin yaron na shirin janye keken ya sanya shi saurin riƙe keken.
"ÆŠan shiga ciki ka ce Humaira ta zo, Fadeel ya iso."
Jin haka Muhsin ya amsa da toh, ya juya kan kekensa bayan Fadeel ya saki ya wuce ciki.
***
A can kuwa, Mami da Futuha na zaune sai gani suka yi Tasleem ta fado falon a guje, tana zuwa ta zube cinyar Mamin tana kuka.
"Ke lafiya? Meyafaru?" Cewar Mami cikin É—aga murya gaba daya ta ruÉ—e. Wannan ya yi sanadin fitowar su Humaira daga É—aki sai a sannan Tasleem ta É—ago ta dubi Mami.
"Wai ba ki yake so ba, wajen Humaira ya zo."
Jin haka Futuha ta ji zuciyarta dan yi sanyi, ko ba komai Tasleem ba za ta ƙara hura mata hancin ta yi wanda ya fi Ibb ba kuma ta gane ba Ibb ne masoyin Humairar ba. Amma a gefe kuma kishi da tsanar Humaira ne ya kara mamaye ta, mene ne da ita wanda har namiji irin Fadeel zai gani ya maƙale mata, su da suke buzaye ma ta kasa shawo kan Ibb ya kaunace ta sai wata can bafulatanar ruga?
Mami kuwa gaba daya fuskarta ta sauya, kafin ta yi magana dai ga Muhsin a guje da kekensa ya shigo falon, yana cin karo da Humaira ya ce.
"Adda Humaira, ki je inji wani a waje."
"Ka je ka ce ba za ta fito ba! Kada ya kara gigin zuwa gidannan!"
Gaba daya suka dubi fuskar kowannensu dauke da mamaki idan ka cire Humaira da kalaman ya yi mata dadi ainun, haba ta gaji da naci irin na Fadeel, shi bai san ba ta son komai da ya danganci saurayi ba. Meyasa ya ƙi fahimta? Ai gwara Mamin ta kora mata shi. A bangaren Raihana da Ummita kuwa tunaninsu daban da nata. Akan me Mami za ta ce Fadeel ya tafi? Wato don ba ya sin Tasleem shikenan kowa ma ya rasa? Tasleem da Futuha kuwa dadi ne ya mamaye su, wato dai uwa uwa ce, ta damu da yaranta. A farko sun yi zaton kwata-kwata Mamin ba ta kaunarsu ta fi kaunar ƴan riƙonta musamman ma Humaira. Amma a hukuncin da ta yi abin ya musu dadi, Tasleem ta ji gwara ma kowa ya rasa.
Muhsin kuwa tuni ya fice don cika umarnin Maminsa. Humaira dai ta juya zuwa daki don ci gaba da abin da ya rage na ninkin da take yi, ganin haka Ummita ta bi bayanta, Raihana kuwa da sauri ta bi bayan Muhsin. Futuha na kwala mata kira ta yi mata banza.
***
A can farfajiyar gidan kuwa, Muhsin ne ya karaso har kusa da Fadeel, yana shirin faɗin saƙon Mami da sauri Raihana ta kwala mishi kira.
"Kai Muhsin." Suka juya har Fadeel suka dube ta, ta karaso da sauri ta ce.
"Jeka zan faɗamasa." Ya kuwa tura kekensa ya ci gaba da zagaye a gidan yana waƙe-waƙensa da ake musu a boko. Ta gaida shi ya amsa, zuwa yanzu ya karaya da ganin Humaira.
"Suna na Raihana ƙanwa ce ga Humaira, don Allah ka yi hakuri ba za ka samu ganinta ba a yau sai dai ko watarana idan an ɗan kwana biyu."
Murmushin da bai kai zuci ba ya yi, ta tabbata shi kadai ke kiɗa da rawar sa, wacce ya ke yaƙin don ita ba ta san yana yi ba, ko kuma ya ce ta sani amma ra'ayinsu ya sha bamban.
"Kar ki damu, ba komai. Idan kin shiga ki ce ina gaishe ta, na kuma cika alƙawarin da na daukarwa kaina na zuwa gidansu. Amma hakan ba ya nufin ko a mafarki zan iya fita a rayuwarta. Ina sonta."
Daga nan ya juya ya fice. Raihana ta zuba masa idanu har ya fita daga gate din gidan, tausayi sosai ya ba ta, Humaira dai tana neman cutar da kanta. Samun masoyin gaske irin Fadeel abu ne mai matuƙar wahala. Ta ji haushin Humaira a zuciyarta kamar ta je ta rufe ta da duka. Gwuiwa a sake haka ta juya ta koma ciki.