← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 82 OF 101

Sashe 82

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Ya yi daidai da shigowar Abba gidan, yana tsaye da jami'an tsaro na SS da suka zo tafiya da Jannat su na magana ta fahimta, Abban na cikin muguwar kaɗuwa na jin wannan sabon al'amarin, suka tsinci ihu da kururuwar Mamin. Gaba ɗaya suka nufi ciki da gudu-gudu har Abban don ganewa idanunsu abin da ya faru kasancewar ɗakin samarin dab da waje yake.*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

Yassar ne ya yi kan wayar da Ƙasim ya yi cilla da ita ya dauka, shi kuwa Ƙasim da gudu ya tafi don ɓuya a bandaki jikinsa na mugun kaɗawa tsabar firgici cikin sauri Mami ta karasa ta rike shi gami da watsamasa mari hagu da dama.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Kassim mene haka nake gani?"

Yassar ke ambato hannunsa da yake rike da wayar har rawa yake yi, Dawud ya karasa ya karɓa ai kamar wanda aka jonawa wutar lantarki sai ya yi jifa wayar. Ya yi daida da fadowar su Abba ɗakin. Mami idanunta sun rufe ruf ta cakumi vest din dake jikin Ƙassim tana girgiza shi tana kuka take fadin.

"Don ubanka sai ka faÉ—amin inda ka koyi kallon banzan nan?! Kana neman jinsi ne? A gidan uban wa ka ke yi?!!"

Maganar ta saukarwa Abba kamar wata kibiya a ƙahon zuciya.

"Ke Maryam, me kike magana a kai ne?"

Sai a sannan ta san ma da Abba a É—akin, ta dube shi cikin rufewar isanu har ma ba ta tuna tare ya ke da wani balle ta tuna tashin hankalin da take ciki na rashin cikar muradinta ta soma magana.

"Ka cuce ni Yusuf! Tsaurin daka yiwa yarannan na hana su abin kashewa shi ya janyo Kassim kalla-kallacen bidiyoyin luwaɗi. Ni dama na jima ina zarginsa da matasan yaran gidan Alhaji Tsalha! Ance yaran ba su ji kuma abin da suke aikatawa kenan amma nayi magana ya ƙaryata ni, kuma ka hana shi mu'amala da su ya
."

"Ke! Ya isa hakanan!"

Abba ya tsawatar ganin kamar ba a hayyacinta ma take zantukan ba ga Ridwan da ya tsaya cike da jinjina wannan lamari. Sai kuma ya É—an kalli Ridwan din sannan cikin karfin hali ya ce.

"Ki bar zancen zan san ta yanda zan ɓullo masa, yanzu dai ki shiga ki kira Jannat ina son ganinta."

Mami ta ji wani malolon bakin ciki, wato yana nufin dai ba zai matse bakin ƙassim din ba ta ƙarfi a ji ko me kenan da har ra'ayinsa ya tafi ga kallon zina? Sai kawai ta sa kai ta bar ɗakin, Abba ya bi ta da kallon kin ban mamaki kafin ya mayar da hankali ga Ridwan wanda cikin nutsuwa yake yiwa Ƙassim tambayoyi kai ka ce don shi ya zo. Nan Kassim cikin zubar hawaye ya soma magana bayan ya yi rantsuwar bai taɓa aikatawa ba ya ƙara da fadin.
"Sosai suke kashemin kudade don son na saki jiki da su na bi sahunsu, ni kuma na nunamusu ba zan aikata hakan ba shi ne ni kuma bisa zugar su Usha na soma kallon bidiyoyin don na ga abin da suke aikatawa. Abba don Allah ka yafemin, wallahi tallahi ban taɓa aikata kowace kalar zina ba balle kuma ta jinsi."

Kuka sosai ya sanya a ƙarshe dukkan gaɓoɓin jikinsa babu inda ba ya kakkarwa. Abba dai ya kasa magana saboda tsananin kunyar Ridwan da kuma baƙin cikin gurɓacewar zuri'arsa da ya rasa ta inda aka haihu a ragaya. Ya dai san cewa jarrabawarsa kenan. Ridwan ne ya dinga yiwa Ƙassim nasihohi masu ratsa jiki. Kassim sai da a karan kansa ya yi nadama ya kuma yi alƙawarin fita a hanyar su Usha da yan uwansa. Da wannan Abba ya ce Ridwan su ƙarasa ciki aiwatar da abin da ya kawoshi.

***
Jannat ko a kanta ba ta taɓa zaton wani abu ne ba don Abba ya yi kiranta, saboda Mami ranta a ɓace yake ne da batun Ƙassim da kuma rashin nasarar da ta yi sai ta ma kasa tsayawa yi mata wani bayani dogo, tana isar da saƙon ta fice ɗakinta don tunanin mafita.

***
Ta karaso falon, Abba dai kallonta kawai yake. Ga ta dai mutum har mutum a fuska, matar da yake yiwa kallon kanwarsa Amina, koda alama babu wani abu wai wasan ƙanwar mata tsakaninsu face girmamawa da nuna damuwa ga dukkan wani abu daya shafi al'amarin iyalinsa. Bai manta ba, faruwar lamarin na ɓacin sunan su Ummita takanas ta kira shi a waya tun daga Misra ta jajanta masa har da yin Allah ya isa ga duk wanda ya aikata laifin.

Ita kuwa Jannat ta bi mutanen da kallo sannan ta mayar kan Abba, gaba daya sai kuma ta ɗan sha jinin jikinta. Da murmushin yaƙe ta gaida Abba. Madadin ya amsa sai ya ce.

"Ga baƙinki nan."

Ta gaishe su, ta kara da fadin.

"Toh, sannunku. Sai dai ban gane fuskokin ba."

Ridwan ya murmusa yana mai fiddo Id card dinsa na aiki ya nunamata.

"Sunana Ridwan Bello Jafar, ma'aikacin SS ne. Mun zo tafiya da ke bisa kama ki da laifin ɓata suna."

Ai sai ta ji kamar ta saki fitsari a wando, iyakar dakiya ta dake wajen ɓoyo razanarta. Ta dubi Abba wanda idanunsa ke tsaye ƙurr a cikin nata sannan ta dubi Ridwan da yanayin basarwa ta ce.

"Ɓata suna kuma? Me kake nufi? Sunan wa na ɓata? Sannan waye ya baku iznin kama ni?"

Ya nunamata shaidar izinin kafin ya amsa.

"Ga shaidar iznin tafiya da ke Madam, ɓatancin sunan da nake nufi ba kowanne ba ne sai wanda kika yi ga Ummita da kuma Humaira. Muna da evidences da muke da tabbacin komai da kika aikata, sauran bayanin idan mun je can za ki ji. Ki bamu hadin kai kawai ki bi mu mu tafi."

Shikenan! Ta faru ta ƙare wai an yiwa mai dami ɗaya sata. Zufa ya shiga yankowa Jannat ta ko'ina a fuskarta, ta hau girgiza kai cikin tsananin ruɗewa da tashin hankali bisa kokarin ta ga ta kare kanta amma banda kalmar ƙarya ne babu abin da bakinta ke iya furtawa. Ga Abba da ya yi mata ƙuri da idanu yana dubanta, har lokacin jikinsa a mugun mace yake. Wannan wane irin zuri'a ne ya yi aure a ciki? Daga Maryam har Jannat sun jefa shi cikin ɗumbin mamaki da kuma tsoron halayyar DAN ADAM. Ban da kalmar Innalillahi...babu abin da yake ambato a can kasan ransa.

Ummita dake tsaye riƙe da ɗan ƙaramin kofi mai murfi da ta haɗowa Raihana shayi ta tsaya cak cikin razani da jin abin dake fitowa daga bakin wanda ya kira kansa ma'aikacin SS kuma mai suna Ridwan. Ban da Allah ya taimaka tana dab da bangon shiga kicin ɗin babu abin da zai hana a yanda jiri ya kwashe ta ta zube a nan. Sai da ta ga Ridwan ya miƙe tsaye cikin ba wa Jannat umarnin ta ba su haɗin kai su tafi da kuma ihun da Jannat din ta fasa akan Abba ya taimake ta sharri ne aka yi mata ya sanya ta jin wani mugun ƙarfin zuciya ya taho mata. Ummita mai haƙuri da kawaici, mai yawan murmushi da tausar wanda aka ɓatawa, nan da nan ta rikiɗe ta juye ta koma wata kalar Ummitan mai ban mamaki a inda ta yi fatali da kofin hannunta wanda ƙararsa ya dauki hankalinsu suka dube ta, ba ta damu da radadin zafin da ya tsirga saman fatar ƙafarta ba ta tsallake ta yo gaba jikinta har wani mugun rawa yake yi na ɓacin rai. Babu abin da take tunawa sai muggan kalaman da aka yi amfani da su wajen ɓata musu kyakkyawar tarbiyyar da Abba ya gina su akai shekara da shekaru. Ta tuna sanadin dukkan haka ne ya sa gaba daya aka janye aurenta da Sahabi da a yanzu ya koma ainahin garin iyayensa wato Zamfara da matarsa.

Kallon Abba ta yi ya kauda kansa daga dubanta zuciyarsa cike da tsantsar tausayawa sannan ta maida kai ga Ridwan.

"Domin Allah abin da kake fadi akan wannan (ta nuna Jannat) gaskiya ne?"

Ridwan ya gane ta kwarai, ita ce Ummita don ba ta sauya ba, ya dai ga ta ma fi yarinta a fili sosai fiye da yadda aka yawo da hotunanta. Kawa sai ya ji ta burgeshi ta kuma ba shi tausayi kwarai. Madadin ya amsa da baki sai kawai ya ɗan gyaɗamata kai. Ta juya ga Jannat daidai lokacin da su Yassar suka shigo har Mami da Anna da ma Raihana wacce dama can a gigice take sakamakon ƙarar da Jannat din ta yi ba na wasa ba ne.

"Anti Jannat, ke da kanki? Ke ce kika ɓata mana suna? Me muka yi maki? Wace kalar bautar ce bamu yi ba da har kika zaɓi yi mana mummunan ƙazafin da duniya za ta bar ganinmu da ƙima?"

"Ummita kin yarda zan aikata wannan?"

Ta fadi tana kokarin riƙo kafadun Ummitan, kamar wacce za a jonawa wutar lantarki cikin mugun sauri ta ja baya. Za ta ƙara gangancin matsawa domin ta taɓa ta aikuwa ga mamakin kowa Ummita ɗaga yatsunta biyar ta yi ta sauke saman fuskar Jannat hagi da dama. Za ta ƙara ne da sauri Abba ya riƙeta, kuka sosai take yi kamar ranta zai fita.

"Ya isa, ya isa, kiyi hakuri hukuma za ta yi maganinta da ma dukkan wani azzalumi."

Ya ƙarashe yana duban Mami wacce ta yi mutuwar tsaye jin abin da ƙanwarta ta shuka ya fito muraran. Ta kuma dan sha jinin jikinta bisa kallon da Abban ya watsa mata sai ta yi saurin wayancewa da matsowa ta dubi Jannat.

"Kin bani mamaki, ban yi zaton za ki aikata hakan ba. Me suka tare maki a rayuwarki?"

Jannat dake kuka sosai ta ji kamar Mamin ta sokamata mashi a ƙahon zuciya, ba kuma domin akwai su Ridwan a wurin ba za ta shaƙe wuyan Ummita ne ta aika ta lahira saboda marin da ta yi mata. Ba don jirginta da ya kasance na dare ba da tuni a safiyar yau ɗin ta tashi zuwa Misra inda za su tattaro su dawo Nijeriya gaba daya.
Chapter 82 · 0% Book details