← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 29 OF 101

Sashe 29

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 6 min read

"Don me za ku dinga yi mata batun saurayin da ba ta so?! Ina gargadinku daga rana irin ta yau koda wasa kada wanda ya kara kuskuren ko ambaton sunansa balle ya yi mata zancensa. Fadeel ko? Daga yau sunan nan ya fice a bakinku." Suka ce toh, su ma abin ya tsorata su, sun kuma kara gaskata zancensu, Humaira na da aljanu musamman da suka ji Mami ta mike tana fadin wai ta samu bacci idan ta tashi komai zai wuce a ranta. Tabbas zarginsu ya tabbata gaskiya, aikuwa ga mamaki Humaira sumul ta tashi tamkar babu abin da ya faru. Yanda ba ta yi zancen ba hakanan su ma ba su kara tada shi ba. Ba ma kamar Raihana mai shegen tsoron aljanu, Ummita sai dariya take mata ciki-ciki ganin ko zama kusa da Humairar ta ɗan rage yi a ranar. A gefe guda kuma ta yi alƙawarin muddin ta je Bichi za ta yiwa mijin yar uwar mahaifiyarta magana akan lamarin Humaira, yana ba da hayaki da maganin jinnu, in sha Allahu za ta karɓo mata.

***

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

Ibb ya mike tsaye yana safa da marwa kafin ya naushi bango a zuciye ya juya ya nuna Fadeel da yatsa.

"Wai kai wace irin soyayya ce wannan da ba ta da mafaÉ—i? Wace irin soyayya ce mai neman kai ka ga halaka?"

Murja wacce ke shirin kwankwasa ƙofar ɗakin don ta miƙa musu fruitsalad da ta haɗa ta tsaya cak jin abin da ke fitowa daga bakin Ibb, kirjinta har wani lugude ya ke yi.

Fadeel kuwa jin an danganta soyayyarsa da sunan halaka ya É—an É—ago idanu dakyar ya dubi Ibb sanadiyyar ciwon kai da ya wuni da shi ga azumi a baki. Ibb ya kara jaddada masa furucinsa.

"Yes halaka mana, mutumin da ya amince da zaman jiran gawon shanu alhalin yana da damarmaki da yawa da ma ƴanmata masu ilimi da aji da ke rububin ya amince ya aure su ai kuwa ya jefa kansa a halaka tunda wacce ya ke zaman jiran kora da hali ta yi mishi. Fadeel wake up, ka runtse idanunka da kyau ka fahimci yarinyar nan kora da hali ta ke maka, ba soyayya ba ce. Ba ta sonka, a wautarta lokacin da ta ɗibarmaka zai sa ka ƙosa har ka gaji ka sauya sheƙa amma ba ta san yanda ka mace a kanta ba, ka shirya aikata komai! Toh ni abin ya ishe ni, zan je na sanar da Alhaji komai a je a nema maka aurenta."

Fadeel dai ya yi shiru kawai yana cigaba da kurɓar ruwan shayi don  ba su jima da shan ruwa ba. Jin maganar tunkarar Alhaji ya sanya shi ɗago kai ya daure fuska.

"Ban saka ba Malam, kar ka sake ka aikata wannan gangancin. Ba za ka taɓa fahimtar ya nake jin Humaira ba, ni dai na yarda ita ɗin mahaɗi ce ga rayuwata. Kai duk fa son da za ku yimin ba zai kai yanda ni nake son kaina ba, tun farkon ganina da ita nake addu'ar neman zaɓin Allah amma daidai da sakan guda ban ji ta sauya a raina ba. Ni dai na sani, ina mata so ba iyaka wanda nake da tabbacin ko ba ta sona, nawa son ya yi ƙarfi da isar da zai wadace mu gudanar da kyakkyawar rayuwar aure, na koyar da ita yanda za ta fara sona. Ballantana kuma ina ji a jikina tana kaunata."

Tsaki Ibb ya ja ya koma ya zauna, tabbas ya ji daɗin dawowar ɗan uwansa wajensu, amma ya yi danasanin haɗuwar da suka yi da Humaira. A can ƙasan ransa tausayinsa ne lulluɓe, son maso wani akwai wahala. Don haka sai kawai ya ja bakinsa bai kara cewa uffan ba ya tsiyayi ruwa mai sanyi a kofi ya soma kurɓa.

Daga can bakin ƙofa kuwa, Murja tuni tsayuwar ta gagareta, don haka ta ja ƙafafunta da suka yi mata nauyi ta bar wajen cikin sauri ba tare da ta miƙa musu abin da ta kawo ba. Dama na gulma ne ta kirkiri aikinsa don kanta kawai domin ta burge Fadeel, daga abin da ta ji yanzu ta fahimci babu abin da za ta yi ta burge shi tunda ya makance har haka a san wata banza wacce take da yaƙinin ba lallai ta fi ta kyawun zubin jiki ba. Kafin ta karasa falon Anti Amarya idanunta sun yi jage-jage da ruwan hawaye, ta gifta yaran ta shige ɗakin da kusan yanzun ya zama mallakinta bayan ta ajiye kwanon fruitsalad a falo gami da ba su umarnin shanyewa idan su na so. Kuka sosai ta fashe da shi, babu kalamin da yake mata baƙi kamar na jin da ta yi Fadeel na ambaton wata ɗiya mace da sunan so har yana ikrarin wai yana mata son da ya ishe su rayuwar aure koda ita ba ta sonsa. Ta nanata sunan a ƙasan zuciya, wato Humaira. Sai ta yi ƙwafa gami da tsaida kukanta, a fili ta ce.

"Fadeel muddin ina numfashi sai na mallake ka a rayuwa koda ace hakan na nufin na ɓatar da Humaira a doron ƙasa."

Wannan shi ne alƙawarin da ta ɗaukarwa kanta.

***
A daren da aka yi shelar ganin wata kowa ya tashi da farin ciki da walwala. Humaira tuni sun sha kitso da ƙunshi abinsu, a wannan daren wuni ta yi a kicin tare da Ummita su na aiki ita kuwa Raihana tana can falo tana taimakawa Tasleem jera stones a atamfarta da tela bai samu damar yi ba. Shirin waina, sinasir da miyar taushe ake yi, tun safe suke aiki inda Humaira ta yi snacks har kala hudu, samosa, springrolls sai meatpie da cincin. Ko kusa ba ta huta ba, wata iriyar gajiya ce tattare da ita dukkan gaɓɓanta ciwo suke, kusan ita kadai da Ladidi ne karfin aikin don Ummita ba ta zauna ba, tana kula da yaran Anti Jannat, ko mintuna biyar ba ta yi a kicin din take kiranta ta sanya ta aiki. Dahuwar indomie, haɗa cornflakes, wankin kashi da sauransu.
Ita kuwa Futuha ta tare can sashin Anna wajen Anti Jannat suna hira kamar ba gobe. Mami sai dai ta leƙo ta bita da sannu ta kuma ga yanayin tafiyar aikin sannan ta koma. A wannan daren ba ita ta bar kicin ba sai wuraren karfe ɗaya da mintoci. Da asuba dakyar ta tashi ta yi sallah ta faɗa kicin aikin suyan waina. Kasancewar Ladidi a gidan ta kwana bisa umarnin Mami ya sa ta kama mata. Sai dai duk da gajiyar dake tattare da ita, ranta fari sol, kowa ya san irin murna da farin ciki da bayi ke tsintar kansu ciki idan aka ce yau sallah. Wannan murnar ne ya ɗan ƙara mata kuzari, kafin dai zuwa karfe takwas sun yi sun kammala. A gaggauce ta sanya zuba komai kamar yanda Mami ta umarce ta, ta dauki na Abba za ta kai sai ga Ummita wacce ta tsaya shirya yaran Anti Jannat ta shigo tana mata sannu. Ta karɓa ta ƙarasa da shi. Ya yi daidai da fitowar Mami wacce ta ci adonta cikin doguwar rigar atamfa dinkin three-quarter da zani, peach colour ya sha adon stones. Ta yi kyau sosai abinka da farar fata. Humaira ta gaishe ta, fuska a sake Mamin ta amsa tana mata sannu da aiki.

"Kin yi kyau sosai Mami."

Ta yi Æ´ar dariya.

"Nagode. Muje na ga aikin naki sai ki je ki shirya."

Ta amsa da toh, suka koma kicin ta bubbuÉ—a tana jinjina kai. Cike da farin ciki ta dube ta.

"Girki ya yi kyau Humaira, na kuma sani a baki ma zai fi haka. Sannu da aiki. Ladidi kun sha aiki, Allah ya bada lada."
Chapter 29 · 0% Book details