← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 34 OF 101

Sashe 34

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Kin bani kunya da mamaki Mamana, ban yi zaton hali na rashin kunya da É—a'a daga gareki ba. Me ya hau kanki har haka? Meke yawo a kwakwalwarki kika aikata abin da yau ace mahaifiyarki na raye za ta yi bakin ciki?"

Humaira ta ji ƙarfin kukanta ya ƙaru, kewar mahaifiyarta mai yawa ta ji, ta sani ta aikata ba daidai ba amma ba ta jin Mahaifiyarta za ta kasa fahimtarta koda kuwa ace ta nunamata kuskurenta. Ta danne abin da ke taso mata dakyar ta iya magana.

"Nayi laifi Abba, ka yi hakuri ka yafemin."

Ya kuramata idanu duk sai ta ba shi tausayi kuma, sai dai hakan ba zai sa ya fasa nunamata kuskurenta ba.

"Shikenan, amma ki tabbatar kin samu uwarki kin ba ta hakuri. Matar da take ƙimanta ki, ai yau ko wani mugun bautar mahaifiyarta da ƴar uwarta ke nunamaki ai sa ci albarkacinta ballantana ma babu ɗaya. Amma ki rasa da me za ki sakamata sai da cin mutuncin yan uwanta? Wannan ba daidai ba ne Humaira, Maryama ta wuce nan a wajenki idan kina da tunani. Burinta duk a kanki ya ƙare, kar ki so ki ji yadda koyaushe ba ta da magana sai naki, kullum cikin yabonki take da burin ki zama hamshaƙiyar ƴar kasuwa mai siyar da abinci irin wanda ko Otel sai haka. Ba ina faɗamaki ba ne don wani abu  a face sai na son ki fahimci irin girman da ta ba ki. Daidai da batun bikin yarannan idan aka ɗauko, sai ta ce ita dai burinta ta ga auren ƴan ukunta (Ummita, Raihana da Humaira), su ne ƴaƴanta. Toh kiyi takatsantsan, ki kuma kara martaba wannan girma da soyayyar da take nunamaki. Na san ke ɗin mai jin magana ce kuma ba na shakku akan tarbiyyar Dada, sai dai ina roƙonki kar ki sake na ƙara jin makamancin wannan daga gareki. Kin ji ko?"

A sannan kukanta ya tsaya, sai Mami dake yawo a kanta wadda Abban ya kara sa ta ji kaunarta ta cika zuciyarta ga wani irin nauyi da kunya da ta ji. Shakka babu ta kai maƙurar da har ta kasa danne a zuciyarta ta aikata abinda zai sosa ran Mamin da ma Raihana da Ƙasim wanda a yanzun suke ɗan gaisawa sama-sama.

"Na ji Abba, ina neman gafararka, zan samu Mami na ba ta hakuri. Na kuna yi alkawarin ba zan kara ba"

Murmushi Abban ya yi.

"Masha Allahu, ko ke fa. Maza tashi ki je wajen Mamin taki."

Itama ɗan murmushin ta yi kafin ta miƙe ta bar falon. Kai tsaye ɗakin Mami ta nufa, sallama ta yi aka amsa sannan ta faɗa. Mami dake zaune gefen gado ta yi shiru ta ɗago ta dube ta sai kuma ta sunkuyar da kai. Gaban Humaira ya faɗi, tabbas Mami kuka ta yi, idanunta sun tasa sun kumbura. Sai ta ji nata hawaye sun dawo sabbi, ta durkusa gami da ɗan dafa gefen gadon. Dakyar ta iya tattaro jarumta ta ce.

"Ma..Mami nayi kuskure, nayi babban laifi. Ki yafemin, ki yi hakuri. Maganganun ne suka yimin nauyi, zuciya ta kwasheni na aikata haka."

Sai ta kasa kara wani abin a kai, ta yi shiru. Mami ta kalleta ta ɗan yi wani murmushi mai kama da yaƙe.

"Tabbas kin aikata babban laifi Humaira, kar ki damu, abinda ya faru ya riga da ya afku. Ni na sani, matsalar ni za ta shafa yanzu. Uwa ce ya zama wajibi ga duk mai neman dacewa da rahmar Allah ya bi ta sau da ƙafa, ba zan iya sauya tsanarki a zuciyarta ba kamar yanda ba zan iya jure ƙiyayyar da ake nunawa jinin Fatima ba don a duniya da ace za'a samu abokiyar zama ta gari irin mahaifiyarki, shakka babu da an zauna lafiya. Ƴar uwata kuwa, ni da ita mu biyu kaɗai Allah ya mallakawa Anna, zan iya cewa ƙauna da soyayyar da Anna ke yiwa Jannat ya ninka nawa son a wurinta. Da ace tana da damar zama tare da ita, da tuni yanzu ba ta tare da ni sai ita. Hakuri nake yi ina takatsantsan da abin da zai haɗani faɗa da Jannat sabida na sani ɓacin ran Anna kawai zan fuskanta. A wasu lokutan har nakan yi tunanin Anna ba ta sona kwata-kwata, sai dai son da naga tana yiwa jikokinta ya shafe zargina. A hankali kuma na ke gudun zuciyarta, amma faruwar wannan lamarin, Anna ta yimin maganganu masu zafi wanda ba sani bakinta halaka ce gareni. Har cewa ta yi ba zan gama da duniya lafiya ba. Wannan shi ne dalilin kukana. Na san kema mutum ce mai zuciya a kirji, yau da gobe ana maka abu wataran dama dole a kai ka maƙura. Ina da yaƙinin hakan ce ta kasance yau, amma ina mai baki hakuri a madadinsu."

Humaira wacce ta gama narkewa sosai a tausayin Mami, ta yi saurin girgiza kai ta riƙo hannuwanta, cikin muryar kuka ta ce.

"Mami ki daina faÉ—in haka. In sha Allahu bakin Anna ba zai kama ki ba saboda mu ma shaida ne akan iyakar biyayyar da kike mata, ni nayi laifi Mami, ni ce mai bada hakuri ba ke ba. Na kuma yi maki alkawarin jure dukkan wani abu daga Anna da Anti Jannat albarkacinki. In sha Allahu hakan ba za ta sake afkuwa ba. Ki yafemin, ina jin kunyarki."

Murmushi Mamin ta yi.

"Kar ki damu, ya wuce. Share hawayenki, kukan ya isa. Allah ya sa mu dace."

Humaira ta share fuska bisa umarnin Mamin tana mai amsawa da amin. Itama Mamin ta sauya darasin da yin batun odar da aka ba Humairar. Ita sai a sannan ma ta tuna da wata oda, nan fa ta kara yiwa Mami bayanin matar da ta kirata.

"Toh kinga kuwa zama bai ganki ba, anjima ki zo muyi lissafin komai, idan ya so sai mu ga nawa ya kama sai a sanar da ita ko?"

Zuciyar Humaira tas ta gyaɗa kai tana murmushi. Daga nan ta miƙe ta fita, Mami ta bita da kallo har ta fice.

  Raihana ta fahimci Humaira sai dai ta ɗan nuna rashin jin dadin marin Anti Jannat a fili, ta dai ɗan basar da Humaira na lokaci sai kuma aka shirya suka ɗinke. Su Futuha kuwa ta rasa  me ya hana su yi mata maganar sai dai kallon banza kawai da suke watsa mata a duk sadda aka yi katari suka haɗa ido. Ummita dama ba ta da matsala, wata iriyar yarinya ce mai sanyi da hakuri, ta nunawa Humaira kawai bata kyauta ba da har ta bari zuciya ta kwashe ta suka kasa cin albarkacin Mami. Koda ta fadi haka da toh kawai ta bita, ita kanta ta sani Ummita ta juri abubuwa da yawa wanda ko rabinsa ba za ta jure ba. Ta taso tun bata san mene ne ma'anar hankali ba, ta rayu cikin duka da zagin Jannat, ga Anna a gefe wacce a baya Ummitan ke bala'in tsoro kamar mutuwa. A wurin Mamin kaɗai take samun sa'ida, su Yassar ba su wani damu da zamanta ba tunda tun kafin ta gama mallakar hankalin kanta take basu girma. Komai suka ce ta yi ba ta ƙi, koda kuwa ya fi ƙarfinta haka za ka jagula. Ummita ta ci wahala ta kuma yi hakuri ta jajirce, wannan ne ya sa har gobe ƴan uwan Mamanta na Bichi ba su taɓa kaunar zamanta a gidan ba.

***
  Mami da Humaira sun lissafa komai yadda ya kamata, hatta da ribar sai da suka fitar sannan ta tura acc number din Mamin ga Hajiya Rukayya tunda ita ɗin ba ta da account kamar yanda Mamin ta ce. Aikuwa ko mintuna biyar ba'a yi ba sai ga shi ta aiko kudin. Wannan abu ya yi musu dadi, washegari kuwa da wuri ta fice siyayya ita ɗaya, sauran sun tafi makaranta.
  Koda ta dawo da kaya niƙi-niƙi ga uban rana a garin haka ɗan sahu ya dinga tayata sauke ledoji. Ta kinkima zuwa ciki. A falo ta yi karo da Jannat za ta fita tare da yaranta, dama ta ga an wanke motarta tas yana sheƙi, tun faruwar lamarin sai a ranar suka haɗu, ta gaida ta amma ko kallon arziki ba ta samu ba sai giftawa da ta yi ta fice yaranta na biye da ita. Humaira ta yi mamaki don ta yi tsammanin da duka za ta rufe ta ma duk ranar da suka yi karo. Ba ta wani tsawaita tunanin ba ta maida hankali ga kayanta. Mami ta fito ta dinga yabon siyayyar. Bayan ta watsa ruwa ta sauya kaya zuwa tshirt da zani sannan ta fito zaman aiki. Sai wani nishaɗi take yi, ita da Ladidi ne suka soma, bayan dawowar su Ummita, ita ma ta shiga su ke yi tare.
  Aikin da aka ba Humaira kwanaki biyar sau gashinan a kwanaki uku an kammala komai an haɗa. Hajiya Rukayya ta sha mamaki da ta tsinci wayar Humaira cewa an gama don babu laifi da ɗan yawa snacks din. Ta yi godiya ta kuma nemi kwatancen gidan acewarta za ta turo direbanta a karɓa, nan Ummita ta karɓi waya ta kwatanta mata. Awanni bai fi uku ba sai ga direban ya karɓa ya tafi. Humaira ta dawo ciki bakinta ya ƙi rufuwa tsabar murna. Futuha ganin yanda take washe haƙora yasa ta jan tsaki.

  "Sana'a ba ilimi shirme kenan, mu dai mun yi gaba mun bar mutum, hakanan zamu kammala karatu mu zama manyan ma'aikata muna daga sama  kujera muna juya kowa. Ai Tasleem nan gaba wasu na da kallo."

Tasleem ta tuntsire da dariya. Humaira kuwa hijabinta take ninkewa da ta sanya ta fita waje ba tare da ta ce musu uffan ba, a yanda take jin zuciyarta cike da walwala ba ta jin cewa za ta biye musu su ɓata mata rai a banza. Raihana ce ta yi caraf ta sanya musu baki kuwa.
Chapter 34 · 0% Book details