← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 95 OF 101

Sashe 95

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Daga haka ta dauka ta fice zuwa dakin su Humaira. Ajiyar zuciya mai karfi Tasleem ta saki, murmushin jin dadi ta yi har da É—an buga tsalle. Lallai idan Humaira ta ci a yanda Babandi ya ce za ta ji nan duniya ba ta son auren Fadeel. Shi kuwa turaren da za ta fesa a kayan da Humairar za ta sa, zai yi sanadin da za ta haukace ta bi duniya.

Da wannan farin cikin ta fice a kicin din. Sai dai me? Bayan awa guda ta shiga dakin don ta ga irin sauyuwar fuskar da Humaira za ta yi da borin ba ta son auren Fadeel, amma ta tarar ma waya take yi da Fadeel din tana doka murmushi yanmatan dakin na tsokanarta. Wani zafi da jiri ta ji a kirjinta da kuma jikinta. Jiri har yana so ya kayar da ita. Tana da tabbacin Humaira ce ta ci ta sha shayi da kwai, don har  shigowa ta yi da zummar neman wani mayafinta a sif din Raihana ta tarar Humairar ta a yagar kwai tana loma a baki amma ya akai bai yi tasiri a jikinta ba?

"Ke Tasleem lafiyarki kuwa?"

Ta dubi mai tambayar, Sauda ce diyar Baba Amina dake aure a Zaria.

"Babu komai, kaina ke ciwo tun safe da shi na kwana."

"Ayya, ai sai ki nemi magani. Sannu."

Ta amsa da yauwa tana murmushin yake da kallon Humaira. Ta sa kai ta fice za ta nufi dakin Anna. Sai ta hangi kaya a hannun Raihana za ta shiga falon Abba da su wanda ba ya nan ya fice zuwa wajen daurin aure.

"Kayan waye wannan?"

Tasleem ta tambaya da dan sauri. Raihana ba ta ko kalleta ba don haushinsu take ji su duka ta amsa.

"Na Mrs Fadeel in sha Allah."

Wannan Mrs Fadeel din ya baƙanta ranta sosai, ta ja tsaki, Raihana ta fice tana waƙar.  "Ko anƙi ko an so, aure zai ɗauru.." Ta sani da ita take, ba ma haka waƙar take ba amma don ta ƙo a ranta ya sanya ta juya shi, wallahi ban da da wayonta aka haifi Raihana za ta rantse ba jininsu ba ce yanda ta fifita Humaira sama da su.

Wata ƙwafa ta yi, tana gani Raihana ta shige bangaren Abba ta ajiye kayan ta fito bayan ta jawo kofar, key kawai ta murɗa amma ba ta zare shi ba ta wuce dakinsu da zummar taso Humaira da ta yi wanka ta je ta shirya a can saboda mutane sun yawaita a dakinnasu. Cikin sa'a kuwa ta yi sauri ta afka ciki ta daga kayan ta fiddo kwalbar turaren ta fesa a jikinsu sosai ta mayar yanda ta gansu ta ajiye. Ta bude kofar ta fita ta rufe ta fada sashin Anna tana dariya.

"Ai idan kinsan wata ba ki san wata ba. Babandi ya cemin sai kin haukace kin bi duniya, wannan ranar nake jira. Maza jeki Mrs Fadeel ki sanya kayanki. Uniform dinki na asibitin dawanau."

Tana kaiwa nan ta feshe da dariya. Sai a lokacin ne ta samu nutsuwar shiga wanka, yarinyarta can ta jefa ta wajen Ladidi don a yi mata wanka. Zuciyarta fari ƙal za ta zama matar Fadeel.

***
Gama wayarsa da Humaira ya shiga wanka, bayan ya fito ya kammala shirinsa tsaf cikin shadda ruwan goro da ta sha aiki, kyau iyaka kyau ya yi. Dogo mijin doguwa, ga cikar zati ga kyau da haiba. Fadeel kenan. Ya fito falonsa inda Ibb da su Idris abokansu ke jiransa. Nan suka sanya mishi ihu da zuzuta haduwar da ya yi a yau.

"Ka ga angon Humaira."

Ya yi wani murmushinsa haÉ—adÉ—e.

"Ku tashi muje dama shi muke jira, yana so amma yana ɓatawa mutane lokaci."

Ibb ya fadi yana harararsa don tun dazu suke zaman jiransa sai da ya shiga kawai ya ganshi ya yi daiÉ—ai a kan gado yana waya da Humaira.
Fadeel ya yi dariyar da fararen hakoransa da dimple suka fito.

"Sorry, muje toh."

Daga nan suka fito gaba daya, ba su ko shiga bangaren Anti Amarya ba saboda cunkoson jama'a suka bari akan sai sun dawo.

A kan idanunta ya shiga mota suka fice daga gidan, ta ji saukar hawaye a kuncinta. Ta saki labulen dakin Antinn nata ta juya zuwa ciki. Zama ta yi ta shiga kuka kamar ranta zai fita. Wato Fadeel ya rantse ba zai aure ta ba, Humaira ya zaɓa sama da ita?

A wannan halin Rabi yayarsu ta iske ta.

"Haba Murja, wai sai yaushe za ki sa wa zuciyarki dangana?"

Ta dago fuskar tana dubanta, gaba daya tayi wata iriyar rama da baƙi, dama rabin farin na mayuka ne, har wani ja take yi kamar na soyayyen ƙosai.

"Anti wallahi ina son Fadeel."

Rabi ta zauna a gefenta.

"Amma shi kuma ba ya sonki. Wannan bai isa sanya ki hakuri da shi ki rungumi mai sonki ba? Anas ƙanin mijina sai binki yake kina wulaƙantashi."

"Anti shaye-shaye yake fa."

"Sai me? Kar ki manta ya fi mijina kudi sosai. Kedai ba burinki ki yi auren kudi ki hutawa ranki ba? Mu din ma ai fatan da muke yi maki kenan. Ki rungumi kaddara ki aminta kawai a daura maku aure. Kina haifar namiji shikenan mu burinmu zai cika kin zama matar gida. Wallahi a yanda halittar fatarki ta kara munana Fadeel ba zai taɓa kallonki ya ji sonki na aure ba balle sha'awa. Ki yi hakuri ki lallaba rayuwarki da auren Anas kar ki yi saki na dafe. Watakila ma sai kiga sanadin soyayyar da yake yi maki Allah ya shirya shi. Sai kiga ya sauya daga yanda kika san shi. Mu dai ki zama Matar Gida, ki haifar masa ɗa namiji dukiyarsa ta zama ikonki."

Rabi ta dinga yi mata famfo, har a karshe ta ji ta saduda ta amince da hakan. Da wannan murnar da farin ciki ta kira Anas ta yi mishi albishir cewa ai Murja ta aminta da batun aurensa. Shima ya yi farin ciki sosai ya kuma ce a ba shi Murjar ya ji ta bakinta. Nan ta sanar da shi eh hakane ta yi na'am har feeto ya yi mata a kunne ta cikin wayar tsabar farin ciki. Ita dai ta yamutsa fuska. Ai gwara ma ta yi kudin ta nunawa Fadeel ba shi kadai ke da arziki ba.

***
Ta shirya tsaf cikin leshin da Raihana ta tanadar mata. Raihana na kokarin miƙa mata sarƙa ta ga Humaira ta yi wani dumm, lokaci guda kuma idanunta suka kaɗa. Ta rike kanta ta shiga tari.

"Lafiya Humaira?" Ta tambaya hankali tashe.Ta yamutse fuska gami da neman wuri ta zauna dalilin jiri da take ji yana kwasarta.

"Raiha wannan wane irin turare ne? Warinsa babu dadi, kinga jiri nake ji ga amai na yunkurin tahomin."

Da sauri Raihana ta mike.

"Ya Salam, naji, ai nayi zaton ko Baba Amina ko Hajjo ce suka fesa, ban ma ankara da ƙamshin ba sai yanzu. Cire kayan kar ya ja maki wata matsalar."

Ba shiri Humaira ta cire da taimakon Raihanar, ta karasa ta ware mata fankar falon ta bude labule don ta samu iska sosai, kayan kuwa ta kwasa ta fice tana ce mata ta jira tana zuwa. Humaira ko hijabi ta zura saman zanin da ta ɗora a kirjinta ta kwanta a can wata kujerar don turaren wani karfi ne da shi da ya mamaye kujerar da ta bari. A hankali kuma ta shiga ambatar sunayen Ubangiji har hakan ya haifar mata da nutsuwar zuci da na jiki. Tana a kwancen tana salati har Raihana suka shigo tare da Baba Amina da Hajjo sai ko Anti Maijidda wacce tun shigowarta a safiyar yau gidan ta faɗa cikinsu ake ta hada-hadar girki da ma dukkan ayyuka da ita kasancewar dama can za'a ce ƙawa ce ga Baba Amina duk kuwa da ta bata shekara guda hakan bai hana ƙawance wanzuwa ba. Rashin yar uwarta Jamila ne ya sanya ƙawancen ja baya sai ko idan abu ya tashi suke haɗuwa, sai kuma waya.

Humaira ta tashi zaune. Kayan ne sai a hannun Raihana sai dai yanzu ƙamshin turaruka masu daɗi suke yi na wuta da aka dora kayan saman kabbasa aka turara su.

"Ke Humaira, tashi ki sa kaya. Wane irin turare haka naji na kayan dazu? Ina yake?"

Cikin daurewar kai take duban Baba Amina sai ko ta girgiza kan.

"Wallahi Baba nima kawai dai na ji yana ƙamshin, na ma yi zaton ko ku ne ku ka fesa."

"Aa ko kaÉ—an, Raihana ma ba ta fesa maki komai ba, ina ce har da kwalin turaren ta shigo da shi a jaka. Ai ba a kai ga fesawar ba."

Nan dai aka hau jimamin wannan abu, Raihana kuwa iyaka tunaninta ya tafi ga Tasleem sai dai ba ta da kwakkwarar hujjar da za ta ce ko ita ce. Nan da nan ta shiga istigfari.

"Yanzu dai duk a ture wannan tunda dai ya wuce. Ta yi sauri ta shirya ta fito mutane sun soma cika gidan." Cewar Anti Maijidda.

Daga haka suka fice aka bar Raihana kawai sai Humairar, Raihana ita har Humaira ta kammala jikinta a mugun sanyaye yake. Can kuma sai ga mai kwalliya ta iso, Ummita ta rako ta har bangaren Abban, aka shiga yi. Ganin haka ita kuma ta fice zuwa sashin Anna wajen Tasleem.

Ta iske ta zaune tana tsantsara kwalliya a fuskarta, rabon da ta ce ta ga Tasleem cikin irin wannan kwalliyar tun lokutan amarcinta. Ta tsaya tana kallonta lokaci guda kuma tana É—an waige-waige cikin É—akin wai ko za ta ci karo da turaren.
Tasleem na ganinta ta miƙe tsaye cikin sauri.

"Lafiya na ga fuskarki wani iri?"

Tambayar kawai da ta jefawa Raihanar kenan, Raihana ta yi murmushi gami da É—aga kafaÉ—arta.

"Lafiya ƙalau ma kuwa, watakila kewar rabuwa da yar uwata ne ya soma dukana."

"Humaira?! Me ya faru da ita?"

Ta tambaya idanu waje cikin zaƙuwar son jin amsar da zai fito a bakinta. Ita kuwa idanu ta ƙuramata cike da zargi ta ce.

"Babu abin da ya faru da ita sai alheri, yanzu haka ma kwalliya ake yi mata. Kin yi zaton wani abun ne?"
Chapter 95 · 0% Book details