← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 13 OF 101

Sashe 13

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Humaira wacce ta kasa tsaida hawayenta, kallon Tasleem din kawai take har ta kai aya, lebbanta na rawa amma ko harafi guda ta kasa fitarwa tsabar baƙin ciki. Wannan wace irin baƙar rana ce a wajenta haka da za a wayi gari da yi mata ƙazafin sata? Ta kasa motsawa, haka Futuha ma ta taso da nata kalar rashin mutuncin, su Yassar na taya ta. Ba ta iya cewa uffan ba sai kukan da ta ke rusawa kamar ranta zai fice. Tsawar da ta ji an daka musu ya sa ta kallon hanya, ruwan hawaye ya sa ganinta komawa dishi-dishi, sai a hankali bayan ta ɗan runtse idanu sun ɗan zuba ne sannan ta lura ashe Mami ce. Ƙarasowa ta yi fuskarta a ɗaure, sai ta koma mata Mamin da ta fara cin karo da ita a ranar farko na zuwanta gidan. Kirjin Humaira ya hau dukan tara-tara, ta runtse idanu saboda ta gama hasaso abin da zai afku, wato mari za ta sha a wajen Mami, sai dai ga mamakinta ta ji akalar faɗan sam ba a kanta yake ba, su Tasleem ta shiga yiwa tamkar za ta ari baki.

"Ashe rashin mutuncin naku ya kai har haka? Raini ne wannan ku ka yimin ko mene? Ban hana ɗayanku yiwa Humaira maganar abin da ya faru ba? Ina ce har ɗaki ke Futuha kin biyo ni akan sai an ɗauki mataki na ba ki saƙo ga ƴan uwanki cewar na kashe maganar kada wanda ya tayar? Oh saboda ku nunamin ni banza ce wurinku, hukuncina ma na banza ne shi ne dalilinku na yin watsi da zancena a kwandon shara ko?! Toh wallahi ku fita idona tun wuri, kuma daga rana irin ta yau ku ka ƙara tada wannan batu sai na saɓamaku kamanni."

Tana kai wa nan ta ja hannun Humaira zuwa ɗakinta. Ta bar yarannata a tsaye tamkar su haɗiyi zuciya su mutu don haushi, Yassar ne ya soma jan wani dogon tsaki kafin ya sa kai ya bar falon, Dawud ya mara mishi baya. Tasleem kuwa ƙwafa ta yi.

"Innalillahi, ke Futuha na soma tsoro, na yarda dagaske ne da ake cewa ƴan ƙasarsu na da asirai, anya wannan shu'umar yarinyar da Kawunta hakanan suka  bar mana uwa? Anya ba sai da suka shuka tsiyarsu sannan ta dawo wajenmu ba?"

Futuha da ta kasa magana kawai sai ta ja tsakin itama ta ɗauki wayarta ta wuce sashen Anna idanunta cike da kwallar baƙin ciki.

***
A gefen Mami kuwa, su na shiga É—akinta ta rungume hannuwanta a kirji ta daure fuska tamau har sai da Humaira ta sha jinin jikinta.

"Zauna." Ba musu ta zauna a saman kafet, ita kuwa ta hakimce a gefen gado.

"Na tsawatarwa yarannan saboda na riga da nasan takun saƙar da ke tsakaninku, ba na son a samu fuskar da za su ƙara ɗora maki karan tsana a matsayinki na yar uwarsu ta jini. Wannan ɗin ma da suke gwada maki fatana su daina na kashe shi gaba ɗaya. Amma meyasa haka Humaira? Har yanzun ina kokwanto akan kin aikata wannan laifin na ɗaukar kudi a ɗakina, amma idan  na tuna ganin da na yiwa kuɗin a cikin kayanki sai zuciyata ta tsinke. Ki faɗamin iyakar gaskiyarki, kamar yanda idan na ci karo da ɗaya cikin su Tasleem sun aikatamin laifi zan hukunta su, kema matuƙar da zuciya ɗaya nake zaune da ke ya zama wajibi na dauki mataki idan kin yi ba daidai ba."

Humaira ta ja majina tana kallon Mami. Girgiza kai ta soma cikin muryar kuka ta ke magana.

"Wallahi Mami, Allah ɗaya, ba zan yi wasa da Ubangijina wurin yi maki ƙarya ba, ban taɓa ɗaukar ko abin sakacen haƙori a ɗakinki ba tare da izninki ba ballantana kuma kudin da ba nawa ba. Mene ne bakya kokarin yimin a gidannan da zan yi maki sakayya da hakan? Kina yimin kyautatawar da ko na rayu da mahaifiyata abin da za ta yimin kenan. Toh a wane dalili zan zama butulu har na ɗauka daga asusunki? Mami wallahi ban ɗauka ba, ba ni kuma da masaniyar yanda aka yi kudin suka je cikin kayana, nidai na san na maki gyaran ɗaki, na kuma adana su a inda na gansu, na fita zuwa gidan Anti Laila."

Mami ta yi shiru tana nazarinta, duk kushen mai kushe ba zai taɓa zama da Humaira ya ji ta masa karya ko sau ɗaya ba. Toh wannan dabi'a ce ta mahaifiyarta, ta sani sarai mahaifiyar Humaira haka take da faɗar gaskiya. Ta san kuma ko a gaban Abban maganar ba za ta chanja zani ba. Sai ta yi nufin kasheta a yanzu ta hanyar numfasawa ta dafa kan Humairar cikin taushin murya ta ce.

"Ya isa hakanan, bari kukan kar ya ja maki ciwon kai. Na yarda dake ai dama, sai dai kin san kudi ba zai kai kansa cikin kayanki ba ko? Koda ace ba ke kika kai ba akwai yadda aka haihu a ragaya, kin ga kuwa dole na bincika matsayina na matar gida ko?"

Humaira ta gyaɗa kai har sannan tana sauke hardadden numfashi irin na wanda ya ci kuka ya ƙoshi. Mami ta dora da fadin.

"Toh don haka kar ki fahimce ni baibai don na tuhumeki, ya zama dole na aikata hakan ne ko don sauke hakki, yanzu kuma da ya kasance ba ke ba ce, zan bincika a sannu gaskiya za ta yi halinta. Tashi ki je ki ci abinci ki huta."

Humaira ta gyada kai kawai ta mike ta fita. Har sannan jikinta bai bar ɓari ba, sharri ya fi komai ɗaga mata hankali, ta tsani sharri, ta kuma ci alwashin ita kanta za ta dage da addu'a har sai gaskiya ta yi halinta don a yanzu kam ba ta da amsar ba su Tasleem sai lokacin da komai zai bayyana muraran.

A can É—aki ma Ummita ta tarar tana nata hawayen, sai ya zamana ita ce mamai rarrashin Ummitan da nuna mata ai Mami ta fahimce ta. Ummita ta labarta mata yadda komai ya faru. Ta kara da fadin.

"Ba ni da tabbaci akan ko su Tasleem ne da aikata hakan, amma shakka babu ina zarginsu."

Murmushi Humaira ta yi.

"Kar ki damu yar uwa, idan ma su ne ina mai tabbatar maki wataran gaskiya za ta bayyana."

Daga haka suka bar zancen, koda Abba ya zo, babu wanda ya tunkareshi da zancen don ba karamin gargadi da jan kunne Mami ta yi musu ba, koda Anna ta hau faɗa, sai Mami ta sanyayar mata da jiki da faɗin abin da ta fi tunanin akan sharrin da aka yiwa Humairar. Dole itama Anna ta lallaɓa su akan zanceya mutu. Daga ranar kuwa ba a kara tayarwa ba kuma basu fasa kiran Humaira da wannan sabon suna na ɓarauniya da suka laƙaba mata ba. Wanda hakan ya fi komai yi mata zafi, duk kuwa da Mami ta tsawatar amma a fakaice a bayan idon Mamin ba sa fasa faɗi.

***
WATA BIYU BAYAN HAKA...

Ranar ta kasance yammacin Asabar, gaba ɗaya ahalin gidan su na nan idan ka cire Abba wanda ya fita zuwa kasuwa tare da Dawud. Fuskar Mami a kallo daya za ka shaida tana cikin farin ciki. Su Tasleem dai murnarsu ba yabo ba fallasa. Humaira kuwa da Ummita aiki suke tare da Mami ba kama hannun yaro, Raihana na can ɓangaren yayannasu tana aikin gyara bisa dole don ba yadda za ta kaucewa umarnin Mami, sai dai rabin aikin tana yi ne amma hankalinta na ga chatting din da take yi da sabon saurayinta wanda ya kasance abokin yayan ƙawarta.
Humaira ta zage damtse wurin yin kayan snacks yayinda Mami da Ladidi su ke aikin girka masa dambun shinkafa da kuma kunun aya, kamar dai yanda ya buƙata. Sun kammala da wuri suka jera komai a saman tebur, Humaira a gajiye ta nufi hanyar ɗakinsu da zummar watsawa jikinta ruwa adalilin zafin da ke tasomata, Mami ta dakatar da ita ta hanyar kiranta. Juyowa ta yi gami da amsawa.

"Maza je dakin Yayanki ki dubamin waccan mashiriciyar ko ta kammala gyaran nan, idan ta kammala ki dawo ga charcoal ki kunna a sanya turaren wuta."

Ta amsa da toh sannan ta juya cikin bin umarnin Mamin. Tana zuwa daidai kofar dakin Yaya Mubarak ta ji muryar namiji kamar ta waya ya na fadin.

"Um um sweetheart, ban gaji da ganin su ba, ni da ace za ki ɗan buɗemin ko saman ne kaɗai na kalla zai taimakamin ya magancemin wani abin. Please taimakamin kin ji? Gaba ɗaya ta miƙe wallahi."

Humaira ta zaro ido, sam ba ta fahimci komai ba, ta na shirin faɗawa ɗakin don ta ga meke gudana ta tsinkayi muryar Raihana na amsawa da wata murya tamkar ba nata ba tana wata iriyar shagwaɓa.

"Um um Baby, ba zan iya buÉ—emaka ba ina jin kunya."

"Toh naji, ki yimin hotonsu na miki alkawari ina kalla zan goge, nima zan aikomaki da hotona nikam ko ace ba ki goge ba ba zan damu ba saboda ina maki son da nake jin cewa komai na jikina mallakinki ne koda ba mu yi aure ba. Uhum?"

Humaira ta dafe kirji, yanzu kam ta fahimta, ta gane komai. Nan da nan ta nemi gajiyar da ke É—ibanta tana tafiyar rangaji ta rasa, da wani irin azama ta daga labulen dakin ta fada ba ta ko tuna da sallama ba. Raihana da ke fuskantar madubin dakin rike da waya tana videocall da wanda ta kira Baby, ta hango Humaira ta cikin madubi, ba ta san lokacin da ta kashe kiran gaba daya ba gami da saurin ajiye wayar saman madubi. Cikin rawar baki da danne firgicin da ta shiga na irin kallon zargin da Humaira ke watsa mata ta ja guntun tsaki tana kama gefen bedsheet wanda tuni ta kammala gyaransa amma ta hau kara cusawa.

"Ke kuma Malama kawai sai ki faÉ—omin haka babu sallama babu komai?"
Chapter 13 · 0% Book details