Sashe 59
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
"Hajiya bai kai ga nan ba. Ni dai yanzu kudi mun ci ubansu. Kawai dai abin da ya kamata a bar ta ta haihu, ni kuma zan zo na dauke gudan jinina na kai garinmu."
"Me kake so ka ce?"
"Eh ina so nace maki ni Sadik Wizzy ina son abina. A bar min ciki ta haihu na karɓi abina."
Mami ta yi shiru tana nazari. Idan har Ummita ta haihu ya karɓi abin da ta haifa watarana asiri zai tonu, ita kuma ta rantse ta gwammace gwara abin da za ta haifa din ya mutu da dai wannn gurguwar shawarar ta Wizzy.
"Ya ne wai kika yi shiru Hajiya? Ba ki ji nace maki ina son abina ba? Toh ina son abina, duk wanda kuma ya yi yunkurin aika shi lahira nima zan sanya shi dogon bacci. Ina fatan kin fahimta? Idan na karɓe abina ba sai ta je ko uwar ina za ta je ba mu raba gari?"
Zufa sosai ya rufe Mami, gaba daya kanta ta ƙulle ta kuma rasa mafita. Dole haka ta amsa da toh suka yi sallama.
***Â
*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*
*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*
09034973645
Ganin lamuran bana ƙare ba ne, ya sanya a dole suka rungumi ƙaddarar cikin Ummita. Babu yanda suka iya don a gaban idanunsu an yi dukkan wani kokari don a zubar amma hakan bai yiwu ba. Hankalin su Abba da ma kansu su Humaira ya ɗan kwanta ganin yadda Ummitan ta samu nutsuwa don sosai take kokarin ɓoye nata damuwar saboda samarwa ƴan uwannata nutsuwa musamman Mubarak wanda kullum kokarinsa ya kyautata mata. Shi ne siyo banza siyo wofi, kunna mata fina-finai a wayarsa da ma bidiyon sanya nishadi da dariya, tun ba ta dariyar har ta zo ta ɗan soma murmushi. Ranar da abin ya ishi Mami sai da ta tunkari Abba a siyasance tana ba shi shawarar ya dace Mubarak ya dinga fita kasuwa kafin lokacin da zai tafi bautar ƙasa. Abban ya nuna hakan daidai ne sai dai ya kara da fadin.
 "Amma na so ace ya hakura da kasuwarnan ya cigaba da daukewa yar uwarsa hankali ta hanyar hirar da yake taya ta. Naji dadi kwarai da na ga murmushin fuskarta jiya, na kuma sani hakan yana da alaƙa da shi. A duniya yanzu bani da burin da ya wuce na ganin farin cikin yarinyarnan. Ina kuma cike da fargabar yanda yan uwan Mahaifiyarta za su karɓi batun cikinta."
Wannan magana ta Abba ko a fuska ba ta yiwa Mami ba. Ta fakaici idanunsa ta watsa mishi harara sai kuma da ta ga ya kalleta ta gyara fuskar sosai kai ka ce gaba daya damuwar duniyarnan ita aka É—orawa.
"Ni kaina hakan yana yimin dari bisa dari, sai dai kuma hakan fa ba mai ɗorewa ba ne tunda wataran din dole ne ya wuce bautar ƙasa. A yi hakan dai yanzu, na maka alkawarin in sha Allahu zan tsaya tsayin daka wajen ganin ba ta faɗa cikin ƙuncin baya ba. Ga yar uwarta Humaira ma kullum tana nan tare da ita."
Sai da ta ambaci Humaira sannan Abba ya ce.
"Af, kinga zan manta, mun yi magana da iyayen Fadeel, mun kuma yanke nan da watanni shida zuwa sadda shi Fadeel din ya kammala gini za a tsaida zancen aurensu."
Wani irin jiri ya nemi kwasar Mami daga zaune, ta hadiyi miyau sannan cikin yaƙe ta ce.
"Wannan abin farin ciki ne sosai Abban yara, amma kuma ba ka ganin kamar zai zama mun zalunci yarinyarnan? Har wannan lokacin fa Humaira ba ta kula shi, ba ta kaunarsa."
Abba ya dan daure fuska.
"Bar ja'irar yarinya marar wayo. Ai ba ita ta haife mu ba. Ni na gaji da wadannan mugayen dabi'unnata na korar samari da wulakantasu. An kawomin ƙararta ya fi a ƙirga, a yan watannin nan da fitowarsu dalilin da yasa ban tayar da maganar manemanta ba saboda halin da yar uwarta ke ciki ne, amma ko sati ba a yi ba akwai wanda ya same ni bayan na fito daga masallaci cewa ɗansa ya gani kuma yana so. Hakuri dai na bayar. Ni ba zan biye mata ba. Aure ne dai sai ta yi, idan ba ta son shi Fadeel din ta zo ta kawo wani."
Tsaki Mami ta ja a ƙasan ranta, kamar ta shaƙo wuyan Abba haka ta ji. Kamar yanda ta saba kuma sai ta shanye bacin ran, fuskarta a ɗan daure ta ce.
"Aa fa Abban yara, nikam ba wanda zan yarda ya yiwa É—iyata dole. A dai bi abin a sannu. Yanzu dai ya muka kwana batun kai ta wurin mai magani."
Girgiza kai Abban ya yi, wato dai Mami ba ta taɓa ganin laifin ƴaƴanta.
"Duk sadda ku ka shirya zuwa Mamin Humaira, ni mene nawa a ciki zan mata dole ta je ne?"
Ya fadi cikin gatse da kuma zolaya hakan sai ya ba Mamin dariyar da bai kai ciki ba, ta É—an dara É—in tana mai farr da idanunta.
"Naji din, ko ma me za ka ce hakan ne kawai. Yau dai muna da baƙi, yaran Abba zasu kawo mishi ziyara. Zuwa gobe sai muje."
Abba murmushin shima ya yi, ya gane Tasleem da Futuha take nufi.
"Toh Allah ya kawo su lafiya."
Ta amsa da amin.
Humaira ce ta yi girkin gidan a ranar, ta dawo da aikinta tuƙuru na shiga kicin ganin hakan yana ɗebemata dukkan damuwa sai dai kuma har gobe masu neman ta karɓi odar su ta kasa, ko Mami ba ta sanarwa ana neman odar abinci ba saboda a ganinta ba ta da nutsuwar da za ta yi abin da ya dace.
Bayan ta kammala komai ta zuba a kuloli, ta bar Ladidi da gyaran kicin din ta koma nasu dakin. Kamar dama jira yake, sai ga waya ta shigo. Koda ta duba Fadeel ne, wani irin ɓacin rai ta ji ya danne wani sashi da ke kokarin sanyayamata rai, ta kasa fahimtar yanayin da take ji akan Fadeel tamkar dai guda biyu ne. Farin ciki da bakin cikin da ya danne wannan farin cikin. Babu walwala ta amsa da sallama. Shima ya amsa sallamarta.
"Ina fatan ban takuraki ba? Fatan kuna lafiya?"
Ta tsuke baki, tsiwa take son ace ta yi amma sai ta ji tamkar wani ɓangare na zuciyarta na kwaɓarta. Ta kai duba ga Ummita da ke kwance idanunta a kan Humairar. Sai ta ji dagaske ta kasa tsiwar a gabanta don haka murya ciki-ciki ta amsa.
"Lafiya muke. Fatan kaima haka?"
Daga ma muryarsa za ka fahimci ya ji dadin yanda ta amsa ba kwanaki da take balbale shi da faÉ—a da bakaken maganganu ba, shi kuwa bai ma san zafi biyu ne suka hade mata a baya ba, ga na halin da cikin jikin Ummita ya jefata, ga kuma na wani ciwon kai da bacin rai da muryarsa ke haifar mata marar dalili.
"Lafiya kalau nake. Ina neman É—an wata alfarma wajenki Boddo."
Sarai ta san me yake nufi da wannan sabon sunan da ya raɗa mata, wato kyakkyawa. Sai ta zaɓi ta basar ta hanyar fadin.
"Ina jinka."
"Zan iya shigowa mu gaisa?"
Ta ɗan yi jim, ba komai take tunawa ba sai zuwansa na karshe a watannin baya da har Mami ta ji babu dadi. Yanzu idan ta ce ya zo kuma fa? Ta ji wani abu na tafasa zuciyarta, bakin cikk na saukar mata da ba ta san na mene ne ba. Wani bangare na jan ta da kokarin ta furta ya zo din, amma wani bangaren na kwaɓarta da nuna ta tsane shi, ta tsani ganinsa to me zai zo ya yi mata?
"Toh."
Ta ji lebbanta kawai sun ba da wannan amsar. Shi kansa sai a ya ji wani shock don bai zaci wannan amsar zai ji ba. Ya yi makamancin tambayar ya fi a ƙirga amma kullum amsar aa, karshe ma ta kashe wayar da hujjar ya dame ta. Ya yarda addu'a tabbas na tasiri akan Humaira, don duk sadda ya dage iya dagewa a kan lamarinsu sai ya ga sauyi tattare da ita, ya kuma soma yarda da hasashen Hannatu kanwarsa da kafin ta koma Yola da ta ji irin yanda Humairar ke yi da komai ta ce ba yin kanta ba ne a nema mata magani.
"Nagode Boddo, sai na shigo."
Yana fadin haka ya katse kiran, itama Humaira ba ta ce komai ba ta sauke wayar daga kunnenta. Ta dubi Ummita da ke kallonta cikin murmushin da ba ta san dalili ba.
"Mene ne?"
Ta tambaya. Ummita ta girgiza kai.
"Ba komai, ina dai ganin wani abin mamaki ne a saman fuskarki. Idan ban yi karya ba kina mutuwar son Fadeel amma na rasa meke danne wannan son."
Humaira ta dan harareta da wasa.
"Ni ba sonsa nake ba. Mu bar zancen don Allah kafin raina ya ɓaci."
Murmushin dai Ummita ta ƙara yi, ba ta ce komai ba ta lumshe idanu tana ci gaba da jan carbin dake hannunta. Ita kadai ta san tunanin da take yi, Humaira ta dube ta. Tausayinta sosai ta ji, Sahabi har ya gaji da zuwa hira don ba fita take ba, hakanan ta daina daukar wayarsa. Kullum zancenta guda daya ne, ba za ta yaudari Sahabi ba, ta fi kaunar ya san ita din ta haramta aurensu koda kuwa bayan ta sauke nauyin cikin dake jikinta ne. Ba za ta aure shi ba sam. Ba ma za ta yi auren a duniya ba kamar yanda ta ke faɗamusu a yanzu.
Shigowar Raihana ɗakin ne da sallama ya sa Ummita bude idanun, itama Humaira ta kauda dubanta daga gareta zuwa ga Raihanar. Wannan ne ya katse tunanin dukkansu.
"Mami ta ce ku fito ku gaisa su Tasleem sun zo."
"To." Shi ne amsar da Humaira ta bayar ba don tana kaunar ganinsu ba domin ta gama sanyawa a ranta su din ba masoyansu ba ne. Ba kuma zasu kaunace su ba har gaban abada. Sai da Raihana ta kara maimaitawa sannan Humaira ta mike, Ummita daman tuni ta yi gaba. Cikinta bai da girma bai fito ba.